Mota ko hannu?

Wasu mutane ne su biyu suna fada, daya ya fi dayan karfi. An raba su amma marar karfin ya ki hakura, sai mutane suka ce a rabu da su. Can da mai karfin nan ya yi masa wani wawan naushi, sai ga shi a kasa sumamme. Aka kai shi asibiti, bai san inda yake ba. […]

Mota ko hannu?
Mota ko hannu?

Wasu mutane ne su biyu suna fada, daya ya fi dayan karfi. An raba su amma marar karfin ya ki hakura, sai mutane suka ce a rabu da su. Can da mai karfin nan ya yi masa wani wawan naushi, sai ga shi a kasa sumamme. Aka kai shi asibiti, bai san inda yake ba. Can sai ya farfado, ya ga likita a kansa, ya ce: “Likita, ina fatan dai an kama direban motar?” Likita ya ce: “Ai ba hatsarin mota ka yi ba, hannun abokin fadanka ne!”
Daga Hakilu Umar (Spider Web) Bauchi, 07066777864