Mota mafi kankanta a duniya ta shiga kundin tarihi

Wani mutumin Arizona ya kera mota mafi kankanta a duniya, har ta shiga cikin kundin tarihi a littafin tattara bayanan abubuwan da suka fi shahara na Guiness Book of Record, wanda za a tabbatar a badi. Wanda ya kera wannan mota, Austin Coulson, mutum ne wanda ke hankoron shiga wannan kundin tarihi tun yana dan […]

Mota mafi kankanta a duniya ta shiga kundin tarihi

Austin a cikin motarsa, mafi kankanta a duniyaWani mutumin Arizona ya kera mota mafi kankanta a duniya, har ta shiga cikin kundin tarihi a littafin tattara bayanan abubuwan da suka fi shahara na Guiness Book of Record, wanda za a tabbatar a badi. Wanda ya kera wannan mota, Austin Coulson, mutum ne wanda ke hankoron shiga wannan kundin tarihi tun yana dan karamin yaro.
Coulson matashi ne dan shekara 29, wanda ya bayyana cewa tun yana dan karami yake sha’awar kere-kere. A loakcin yana dan karamin yaro, yakan hau keke tare da abokansa, da ya je gida sai ya kwance keken ya yi masa kare-kare a sassan jikinsa. A lokacin da Coulson ya kai shekara 16, sai ya sayi tsohuwar motar Bronco, ya gyarata. “Na sayi littafin gyara, anan na fara koyon yadda zan kwakwance sassan jikin na’ura, sannan in mayar da komai a mazauninsa,” inji shi.
Kundin shahararrun abubuwan duniya na Guniness Worl Record, a ranar 9/11/2013 ya tabbatar wa Austin Austin Coulson shiga wannan littafi a shekarar 2014, bisa nasarar da ya samu wajen kera mota mafi kankanta a duniya.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan