Motar dakon mai ta turmushe mutum 5 a Ibadan

Hatsarin ya auku yayin da motar da kwace kuma ta yi kan ’yan kasuwa.

Motar dakon mai ta turmushe mutum 5 a Ibadan

Motar dakon mai da ta afka cikin kasuwa

Kimanin mutum biyar ne suka yi gamo da ajalinsu yayin da wata babbar motar dakon iskar gas ta turmushe su a ranar Lahadi.

Aminiya ta ruwaito cewa, mutanen da karar kwana ta cimma na daga cikin wadanda motar ta afka kansu a Kasuwar Bode da ke Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Adewale Osifeso ya tabbatar da faruwar lamarin.

A cewarsa, hatsarin ya auku ne yayin da motar da kwace wa direban a yankin Idi-Arere kuma ta yi kan ’yan kasuwar.

Sai dai binciken da wakilinmu ya gudanar ya gano cewa mutanen da suka riga mu gidan gaskiya sakamakon hatsarin sun kai goma.

A cewar Mista Osifeso, mutane da dama sun jikkata kuma jami’ansu na ci gaba da fadada bincike domin fidda cikakken bayani a kan lamarin.

Hadin gwiwar jami’an hukumar kashe gobara da ’yan sanda sun taru a wurin yayin da lamarin ya auku da zummar dakile duk wani abu da ka iya zuwa ya dawo.