Motar gas ta yi bindiga a Legas

Mutane da dama sun samu raunuka bayan motar ta yi bindiga

Motar gas ta yi bindiga a Legas

Tankar mai na ci da wuta

Wata tankar gas ta yi bindiga tare da raunata mutane da dama a unguwar Ifako-Ijaiye da ke Jihar Legas.

Hukumar Agaji ta Jihar Legas (LASEMA), ta tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Alhamis.

“Hukumar ta fara aikin kashe wutar da ta tashi a ‘Cele Bus Stop’, Karamar Hukumar Ifako-Ijaiye kuma nan gaba za mu bayar da karin bayani”, inji Darakta-Janar na LASEMA, Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu
Da yake tabbata da aukuwar lamarin, Darakta-Janar din ya ce jami’an hukumar na kokarin kashe gobarar da ta tashi sannan ya bukaci mazauna kar su tayar da hankalinsu.

Karin bayani na tafe….