Motar gidan sarautar Ingila ta kashe tsohuwa mai shekara 81
Gimbiyar Edinburgh ce ta kade ta, mako biyu da suka wuce
Tsohuwar nan mai shekara 81 wacce ayarin da ke yi wa Sophie, Gimbiyar Edinburgh rakiya ya kade makonni biyu da suka wuce, ta mutu sakamakon raunukan da ta samu.
Matar, mai suna Helen Holland, ta mutu ne sakamakon ta’azzarar raunukan da ta samu a cikin jikinta, kamar yadda danta, Martin Holland ya shaida wa BBC a ranar Laraba.
- Aikin jarida zan koma idan na sauka daga mulki – Gwamnan Binuwai
- Kotu ta yanke wa barawon kaji hukuncin bulala 8 a Kaduna
Tun da hatsarin ya faru dai ranar 10 ga watan Mayu, matar ta suma kuma ba ta farfado ba, in ji iyalan nata.
Martin dai ya ce an kade mahaifiyar tasa ne lokacin da take kokarin tsallaka titi ta wajen da aka tanadar wa masu tafiya a kasa.
Su ma ’yan sandan birnin Landan sun tabbatar da rasuwar tsohuwar a cikin wata sanarwa da suka aike ta imel.
Wata sanarwar daga fadar Buckingham ta ce, “Gimbiyar Edinburgh na cike da bakin ciki da alhini saboda jin labarin mutuwar Hellen Holland. Mai girma Gimbiya na mika sakon ta’aziyyarta ga dukkan iyalan marigayiyar.”
Sophie, wacce ita ce matar karamin kanen Sarki Charles, wato Yarima Edward, za ta tuntubi iyalan marigayiyar da kanta, kamar yadda sanarwar da tabbatar.