Motar sayarwa

Wasu samari ne su biyu suka tafi ci-rani birni kuma da ma an gaya musu cewa akwai wani mai kudi daga kauyensu da yake zaune a birnin, sunansa Sale. Suna cikin tafiya a birnin, sai suka ga wata mota an rubuta cewa: “This car is for Sale” (Wannan motar ta sayarwa ce). Sai dayan ya […]

Motar sayarwa
Motar sayarwa

Wasu samari ne su biyu suka tafi ci-rani birni kuma da ma an gaya musu cewa akwai wani mai kudi daga kauyensu da yake zaune a birnin, sunansa Sale. Suna cikin tafiya a birnin, sai suka ga wata mota an rubuta cewa: “This car is for Sale” (Wannan motar ta sayarwa ce). Sai dayan ya kalli abokinsa ya ce masa: “Kai, duba can ka gani, waccan motar ta Sale ce, da ma an ce yana da motoci da yawa a garin nan.”
Daga Maryam Abdulrashid Jaji, 07032366792