Motar shiga mafi tsayi a duniya da ta kai kafa 100

Motar kirar Limousine, ana yi mata
lakabi da mafarkin Amurkawa

Motar shiga mafi tsayi a duniya da ta kai kafa 100

Mota mafi tsayi a duniya

Kirkirar motar shiga mafi tsayi a duniya da aka yi ta samu damar shiga Kundin Tarihi na Duniya na Guinness World Record, lokacin da aka auna tsayinta aka tabbatar ta kai kafa 100 da inci 1.5.

Jami’an Guinness World Records sun ce, motar kirar Limousine, wacce ake yi wa
lakabi da mafarkin Amurkawa, an fara kera ta ce a 1986.

Mai kera motoci, Jay Ohrberg ya auna
tsawonta da kafa 60 a farkon kirkirar.

Daga baya Ohrberg ya tsawaita motar zuwa tsayin kafa 100, hakan ya sa kirar motar ta samu lambar Kundin Tarihi na
Duniya a matsayin motar shiga mafi tsayi.

Motar ta bayyana da yawa a cikin shirin fim, kafin a karshe a kai ta cikin kantin sayar da kayayyaki na New Jersey, inda
aka ajiye ta tsawon shekaru da yawa.

Michael Manning, wanda ya mallaki gidan kayan tarihi na koyar da fasaha na Autoseum a Gundumar Nassau da ke Jihar New York a Amurka, ya yanke shawarar daukar babban aiki na maido da mafarkin Amurkawa, wanda ya dade a lokacin ajiyar fasaharsa har ya kai ga rashin ceto da yawa daga cikin abubuwan da yake son farfadowa da ke cikinsa.

Ya ce, abubuwan da suka shafi kasafin kudi ne suka katse tsare-tsarensa kuma ya kare da sanya motar a kan kasuwar eBay, inda Michael Dezer, mai gidan tarihi na Dezerland Park Car Museum da wajen shaqatawa na Tourist Attractions a birnin Orlando da ke Jihar Florida ya
saye ta a shekarar 2019.

An aika da motar zuwa birnin Orlando, kuma Manning ya zo tare da ita don shiga cikin tsarin sabunta tsohuwar
fasahar.

Mafarkin Amurkawa da aka dawo da shi ya kunshi samar da filin jirgin sama mai saukar ungulu da wurin shakatawa da wurin ninkaya da dakin zafi da lambu mai korayen furanni da babban gadon saman ruwa.

Manning ya ce, yanzu za a bajekolin motar a gidan adana kayan tarihi na
motoci na Dezerland Park.

“Da gaske ba a iya sanya motar a kan hanya ba, saboda ta yi tsayi da yawa,” inji Manning.

“An kera ta ce don a nuna fasahar irin wannan motar.”