Motoci masu lantarki a duniya: ina muka dosa? (1)

kasar Sin ta ba da sanarwar daina amfani da motoci masu amfani da makamashin man fetur a kasarta zuwa shekarar 2040.  Daga yau zuwa makonni biyu ko uku da ke tafe, za mu yi nazari kan sakon da ke dunkule cikin wannan sanarwa nata, da kasashen da suka yi wanann kuduri kanfinta, da sakamakon hakan […]

Motoci masu lantarki a duniya: ina muka dosa? (1)

kasar Sin ta ba da sanarwar daina amfani da motoci masu amfani da makamashin man fetur a kasarta zuwa shekarar 2040.  Daga yau zuwa makonni biyu ko uku da ke tafe, za mu yi nazari kan sakon da ke dunkule cikin wannan sanarwa nata, da kasashen da suka yi wanann kuduri kanfinta, da sakamakon hakan ga kudin shigarmu a Najeriya, sannan a karshe mu ji bayani kan motoci masu amfani da makamashin lantarki da yanayinsu.  A sha karatu lafiya.

 

Lahadi: 10 Ga Watan Satumba, 2017

Ranar Lahadi, 10 ga watan Satumba ne dai kasar Sin (China) ta bayyana cewa zuwa shekara ta 2040 za ta hana shigowa da kerawa da kuma amfani da motoci masu amfani da makamshin man fetur ko dizil.  Yayin da yake sanar da BBC, mukaddashin Ministan Masana’antu da Kimiyya da Fasaha, Mista din Guobin, ya tabbatar da cewa tuni kasar Sin ta fara gudanar da bincike mai zurfi a kimiyyance don cinma wannan manufa.  Ba nan kadai ba, hatta jadawali na musamman, Mista din yace tuni sun riga sun samar.  Ya ci gaba da cewa:

“Wannan bincike zai kawo sauye-sauye a bangaren mahalli da kuma habaka fannin kere-keren motoci a kasar Sin. Kamfanonin kera motoci su yi kokarin  rage sinadarai daga mahalli a motocinsu, tare da kokarin kera  motocin da suka dace da mahalli ta amfani da tsare-tsaren hukuma (da za a fitar nan gaba).”

kasar Sin dai ita ce kasar da tafi kowace kasa yawan kera motoci da yawan motocin da ake saya a kowace shekara.  A shekarar da ta gabata kadai, an kera tare da sayar da motoci sama da miliyan 28 a kasar.  Wannan adadi ya fito ne daga kungiyar masu kera motoci na duniya, wato: “International behicle Manufacturers.”

Kafin wannan sanarwa dai, kasar Sin ta fitar da dokokin dake tilasta wa kamfanonin kera motoci a kasar don samar da motoci masu karancin hanyar dumama mahalli, musamman dai motoci masu amfani da makamashin lantarki (Electric Cars) ko masu hadakar makamashin lantarki da gas (Hybrid Cars).  Wannan doka za ta ci gaba da aiki ne har zuwa shekarar 2020.  Kuma tuni kamfanonin kera motocin kasar suka fara bin dokar sau da kafa.

A nasa bangare, kamfanin bolbo ya sanar da cewa nan da shekara ta 2019 zai fitar da mota mai amfani da makamashin lantarki zalla a kasar Sin.  Haka ma kamfanin kera motoci na kasar Amurka, wato Ford Motors ya ayyana cewa zai fara tallata motocinsa masu amfani da makamashin lantarki da gas a kasar Sin, cikin shekarar 2018.  Sannan, kafin shekarar 2025, kamfanin ya tabbatar da cewa kashi 75 cikin 100 na motocin da zai kera a kasar Sin, za su zama masu amfani da makamashin lantarki ne kai tsaye.

Idan kasar Sin ta fara aiwatar da wannan kuduri nata dai, farashi danyen man fetur zai ragu a duniya, domin ita ce kasar da tafi kowace kasa yawan amfani da wannan makamashi.  Daga ita sai kasar Amurka.  Wannan mataki nata dai wani yunkuri ne na ganin ta bai wa tsaftace mahalli mahimmanci.  Domin tuni an dade da tabbatar da cewa, yawan amfani da makamashin man fetur da dizil ne ke haddasa dumamar yanayi a duniya.  Matsalar da tuni ta yi kamari kuma har ta fara shafar tekunan duniya da kasashe ko tsibiran da ke gaba da su.

 

Wasu kasashen…

Kafin kasar Sin ta ba da wannan sanarwa dai, tuni wasu kasashen sun riga ta. kasar Burtaniya na daga cikin kasashen da suka fara bayyana kudurin rage yawan hanyoyi da motoci masu amfani da makamashin lantarki a duniya.  Wannan kudiri nata zai fara aiki ne a shekarar 2040, sadda za ta haramta shigowa da kerawa da kuma hawa motoci masu amfani da makamashin man fetur ko dizil.  A duniya dai kasar Burtaniya ce ta 6 cikin jerin kasashen da suka fi yawan kera motoci da sayar da su.  A shekarar 2016 kadai an kiyasta cewa motoci miliyan biyu da dubu 700 ne aka sayar a kasar.

kasar Faransa ma ta ba da sanarwa makamancin wannan a farkon shekarar da ta gabata.   Ita ma ta ce zuwa shekarar 2040 babu wata mota da za a kera ko shigo da ita ko amfani da a kasar, muddin tana amfani da makamashin man fetur ne ko dizil.  Gwamnatin kasar ta sanar da cewa yin hakan ne kadai zai sa kamfanonin kera motoci su dage wajen samar da sababbin hanyoyin kirkire-kirkire da dabarun zamani.  A halin yanzu dai kashi 4 cikin adadin motocin da ake amfani da su a kasar Faransa masu amfani da makamashin lantarki ne, ko hadakar lantarki da gas.  Kuma a farkon wannan shekara alkaluman bayanai sun tabbatar da cewa kashi 25 ciklin 100 na adadin motocin da aka sayar a kasar, duk masu amfani da makamashin lantarki ne.

A nata bangare, kasar Norway ma ta bi sahun kasashe masu kudurin takaita dalilan da ke haddasa dumamar yanayi ta hanyar rage yawan motoci masu amfani da makamashin man fetur ko dizil akan titunan kasarta, zuwa shekara ta 2025.  kasar Norway dai na cikin kasashen da tuni suka yi nisa wajen amfani da motoci masu amfani da makamashin lantarki a nahiyar Turai.  kididdigar hukuma ta nuna kashi 40 cikin 100 na motocin da ke kan titunan kasar duk masu amfani da makamashin lantarki ne.  Ba mamaki ganin kusancin lokacin da ta yanke don hana amfani da wadannan nau’ukan motoci.

A kasar Indiya ma hukumar kasar ta ba da sanarwa a shekarar da ta gabata cewa zuwa shekarar 2030, duk motoci masu amfani da man fetur ko dizil, zamaninsu zai yanke daga lokacin.  Wannan ba abin mamaki ba ne ga duk wanda ya san yadda kasar ta yi kaurin suna wajen dumama yanayi, sanadiyyar gawurtaccen hayakin da ke toroko a sasannin sararin samaniyarta.  Masu nazari kan al’amuran yau da kullum dai na ganin cewa wannan yunkuri na kasar Indiya yunkuri ne na hakika, musamman ganin yadda hukumar ke jajircewa wajen dabbaka duk wani kuduri na ci gaba da tasa a gabanta.

 

Har da wasu ma…

Bayan dukkan wadannan kasashe da bayaninsu ya gabata, akwai kasashe irin su Austria da ke nahiyar Turai, da kasar Denmark, da kasar Jamus, da kasar Holand, da kasar Portugal, da Spain, da Ireland, da kuma kasar Japan da Koriya ta Arewa, duk su ma tuni suka yi irin wannan kuduri.  kasar Amurka ma, duk da cewa a gwamnatance ba ta yi wani zance makamancin haka ba, amma jihohi guda 8 sun yi kudurin hakan.

kasashen da aka fi cinikin motoci masu amfani da makamshin lantarki a duniya dai su ne: kasar Sin, da Japan, da Kanada, da Norway, da Amurka, da Faransa, da Jamus, da Holland, da kuma kasar Suwidin.  Wadannan dai kasashe ne masu abin hannu, kuma suna cikin kasashen da ke yunkurin hana amfani da motoci masu amfani da makamashin lantarki da dizil, don rage dumamar yanayi a duniya.

 

Me ya shafi kasarmu kuma?

Daga bayanan da suka gabata mai karatu zai fahimci wani abu daya.  Wannan abin kuwa shi ne, nan da shekaru 20 masu zuwa, farashin man fetur zai sauka matuka, watakila ma fiye da yadda ya sauka a shekarar da ta gabata.  Hakan zai faru ne sanadiyyar karancin kasashe masu sayen danyen man fetur.  Domin idan muka yi la’akari da adadin kasashen da suka yi wannan kuduri a gwamnatance, wadanda kuma su ne kasashen da suka fi kowa sayen wannan haja tamu, za mu ga akwai bukatar gwamnatin kasarmu ta kara dagewa wajen habbaka sauran bangarorin ci gaban kasa, musamman harkar noma da inganta ilimi da karfafa masana’antu, don samar da ci gaba a fannin kere-kere.