‘Motoci masu sulke shida Minista Oduah ta saya’
Ministar Sufurin Jiragen Sama Misis Stellah Oduah ta sake samun kanta a kumumuwa bayan da aka shaida wa Kwamitin Majalisar Datawa da ke sauraron bahasin al’amuran da suka shafi fannin sufurin jiragen sama cewa motoci masu sulke shida ta saya ba biyu da ake surutu a kai ba.Wannan sabon fallasa ya zo ne a shekaranjiya […]
Ministar Sufurin Jiragen Sama Misis Stellah Oduah ta sake samun kanta a kumumuwa bayan da aka shaida wa Kwamitin Majalisar Datawa da ke sauraron bahasin al’amuran da suka shafi fannin sufurin jiragen sama cewa motoci masu sulke shida ta saya ba biyu da ake surutu a kai ba.
Wannan sabon fallasa ya zo ne a shekaranjiya Laraba a daidai lokacin da Majalisar Wakilai ta zauna domin jin ta bakin Ministar wadda ta kasa bayyana a gaban kwamitin majalisar kamar yadda aka tsara.
Ana zargin Minista Stella Oduah da kashe Naira miliyan 255 wajen sayen motoci masu sulke guda biyu amma sai ga shi a shekaranjiya an shaida wa kwamitin Majalisar Dattawa cewa, Ministar ta umarci wasu hukumomi da ke karkashinta kan su saya mata irin wadannan motoci har guda hudu.
Shugaban Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN) Mista George Uresi, ya shaida wa Kwamitin Harkokin Sufurin Jiragen Sama na Majalisar Dattawa a karkashin jagorancin Sanata Hope Uzodinma cewa Hukumar FAAN ta saya wa Minista Oduah motoci masu sulke guda hudu kan Dala dubu Naira miliyan 70 kowaccensu.
Mista Uresi, ya ce Hukumar FAAN ta sayo motoci masu sulke kirar Ledus Limousine guda biyu da motoci masu sulke kirar Prado (SUb) ga Minista Oduah.
Ministar wadda aka sa ran za ta halarci zaman kwamitin majalisar wakilai a shekaranjiya rashin halartar ta ya bata ran wakilan kwamitin inda wani dan kwamitin mai suna Jerry Manwe daga Jihar Taraba ya fusata ya ce, “Rashin halartar Ministar wani cin zarafin majalisar ce.”
A makon jiya ne kwamitin ya ba Misis Oduah zuwa shekaranjiya ta bayyana a gabansa, bayan da ya fahimci cewa tana kasar waje don yin aiki a kasar Isra’ila.
Lokacin da shugaban kamfanin Coscharis Motors da ya yi kwangilar sayo motocin Mista Maduka Cosmos ya bayyana gaban kwamitin majalisar ya ce kamfaninsa ya bi ka’ida kan lamarin.
“A sanina mun bi duk ka’idar da ta kamata. Kuma jami’an tsaro na SSS sun yi mana tambayoyi. Mashawarcin Shugaban kasa kan harkokin tsaro ya yi mana tambayoyi. Duk wata ka’ida da doka ta tsara mun bi. Muna kasuwanci ne cikin mutunci.”
Shi kuwa Mataimakin Kwanturolan Hukumar Kwastam Mista Manasa Daniel Jatau, ya shaida wa kwamitin ne cewa Kamfanin Coscharis ya shigo da motocin ne ba tare da biyan kudin fito ba, saboda Ma’aikatar Kudi ta dauke masa. Ya kara da cewa, motocin masu sulke suna cikin motoci 300 da aka shigo da su domin bikin wasanni na kasa a Legas a bara. Wannan yana nufin gwamnatin Jihar Legas ce ta ci gajiyar yafe kudin fiton.