Motocin Dangote 18 makare da siminti sun sha da kyar a hannun IPOB

Motocin Kamfanin Dangote su 18 dauke da lodin siminti sun sha da kyar a hannun ’yan kungiyar IPOB masu fafutukar kafa kasar Biyafara a Owerri, Jihar Imo. Isa Minjirya, daya daga cikin direbobin motocin a hirarsa da Aminiya a ranar Litinin, ya ce, sun shiga tasku  ganin motocin daukar kaya da aka kona. Manyan motoci […]

Motocin Dangote 18 makare da siminti sun sha da kyar a hannun IPOB

Motocin Kamfanin Dangote su 18 dauke da lodin siminti sun sha da kyar a hannun ’yan kungiyar IPOB masu fafutukar kafa kasar Biyafara a Owerri, Jihar Imo.

Isa Minjirya, daya daga cikin direbobin motocin a hirarsa da Aminiya a ranar Litinin, ya ce, sun shiga tasku  ganin motocin daukar kaya da aka kona.

A cewarsa, sun taso ne daga garin Ibese na Jihar Ogun a kan hanyarsu ta zuwa Fatakwal ranar Asabar, amma samun labarin da suka yi na kone manyan motocin ’yan Arewa, tsakanin Owerri zuwa Onitsha, sai suka yi hayar ’yan rakiya kuma ’yan gari wadanda za su bi da su ta wata hanyar daban.

Amma da shiga Abeokuta ta Jihar Ogun sai aka kama su, tare da kai su gidan gwamnati, bisa laifin bin hanyar da ba ta dace ba.

A gidan gwamnatin kwanan su biyu a tsare, amma saboda yawansu, sai gwamnati ta shiga yarjejeniya da kamfanin, daga karshe wani dan kasuwa a garin ya saye simintin baki dayansa.

A ranar Litinin, ake sa ran gama sauke lodin motocin 18, sannan su juya zuwa Fatakwal, sai dai bai san yadda za ta kasance ba kan hanyarsu ta komawa ba.

Kungiyar IPOB ta yi kaurin suna a wajen kai hare-hare da kisa a jihohin Kudu maso Gabashin Najeriya da sunan fafutuka.

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara

Ɗan shekara 60 ya rasu bayan faɗawa a rijiya a Kano