Motocin kayan agaji sun fara shiga Zirin Gaza
Jerin gwanon manyan motoci dauke da kayan abinci da magunguna da sauran kayan agaji sun fara shiga Zirin Gaza daga kasar Masar
Jerin gwanon manyan motoci dauke da kayan abinci da magunguna da sauran kayan agaji sun fara shiga Zirin Gaza daga kasar Masar.
A safiyar Asabar 20 daga cikin motoci sama da 200 suka fara shiga ta iyakar Zirin Gaza na Rafah da ke karkashin kulawar kasar Masar.
- Masar na bukatar taimako saboda rikicin Gaza — EU
- Tinubu ya ba da umarnin biyan malaman jami’a albashin watannin da suka yi yajin aiki
Rukunin farko na motocin suna dauke da kayan jinkai ne daga kungiyar agaji ta Red Crescsent, wadda ta bayyana cewa yawan kayan da aka shiga bai kai cikin cokacin abin da ake bukata a Gaza ba.
Motocin sun samu izinin tsallakawa zuwa Zirin Gana ne bayan da suka shafe kwanaki suna jiran sahalewar hukumomin kasar Masar.
Tun ranar 7 ga watan Oktoba, 2023 Masar ta datse mashigar tun bayan barkewar sabon fada tsakanin Isra’ila da kungiyar Falasdinawa ta Hamas a ranra Asabar da ta gabata.
A ranar Juma’a Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guttere, ya ziyarci Masar domin ganin shirye-shiryen shigar da kayan agajin ta hannun Red Crescent.
Masar ta amince a shigar da kayan agajin Gaza ne bayan tattaunawa da Shugaban Amurka, Joe Biden; matakin da Isra’ila ba ta amince ba, da cewa babu kayan tallafin da zai isa ga Hamas.
Hukumomin Gaza sun bayyana cewa kawo yanzu Falasdinawan da Isra’ila sun kai 4,135, tare da jikkata wasu sama da 13,000.
Hakan na zuwa ne bayan Hamas ta sako wasu Amurkawa biyu (uwa da ’yarta) daga cikin mutanen da kungiyar ta yi garkuwa da su.