Motsa jiki
Wani mai kudi ne da ke wulakanta direbansa, a kullun direban na tunanin ta yaya zai rama. Wata rana yana tuka mai gidan za su je wani gari, sai maigidan ya ce a tsaya zai yi fitsari. Yana cikin fitsari sai ga direba a guje, ya bi kusa da shi ya wuce yana ta waige-waige. […]
Wani mai kudi ne da ke wulakanta direbansa, a kullun direban na tunanin ta yaya zai rama. Wata rana yana tuka mai gidan za su je wani gari, sai maigidan ya ce a tsaya zai yi fitsari. Yana cikin fitsari sai ga direba a guje, ya bi kusa da shi ya wuce yana ta waige-waige. Alhaji yana ganin haka sai ya bi direba a guje, sun dauki kamar minti biyar suna gudu sai direban ya tsaya. Alhaji ya ce: “Kai, mun yi arziki, wai me ke faruwa?” Sai direba ya ce: Babu komai Alhaji, ina motsa jiki ne kawai.”
Daga Lawali Shehu Tsafe