Motsin kasa: Minista ya hana fasa dutse da haka bohol-bohol a Abuja

A ranan Litinin da ta gabata ce Ministan Birnin Tarayya Abuja, Malam Muhammad Musa Bello, ya ba da umarnin  a gaggauta dakatar da hakar ma’adinai da fasa duwatsu da kuma gina bohol-bohol a unguwannin da motsin kasa ta faru a Abuja. Unguwannin da Ministan ya lissafa sun hada da Garki da Maitama da kuma Mpape. […]

Motsin kasa: Minista ya hana fasa dutse da haka bohol-bohol a Abuja
Motsin kasa: Minista ya hana fasa dutse da haka bohol-bohol a Abuja

A ranan Litinin da ta gabata ce Ministan Birnin Tarayya Abuja, Malam Muhammad Musa Bello, ya ba da umarnin  a gaggauta dakatar da hakar ma’adinai da fasa duwatsu da kuma gina bohol-bohol a unguwannin da motsin kasa ta faru a Abuja.

Unguwannin da Ministan ya lissafa sun hada da Garki da Maitama da kuma Mpape. Mazauna yankunan Mpape da Maitama ne suka fara jin rugugin motsin kasa a ranar Larabar makon jiya zuwa mako guda. Sannan motsin kasar ya ci gaba zuwa yankunan Durumi da Jabi da Gwarimpa a yankin Babban Birnin Tarayyar.

Mutane da dama da aka yi hira da su, sun tabbatar da aukuwar motsin kasar a Abuja. Sannan labarin motsin kasar ya mamaye unguwanni da kasuwanni da gidajen cin abinci da wuraren shakatawa, al’amarin da ya firgita mazauna birnin.

Cikin wata takarda da Sakataren Watsa Labarai na Ministan Abuja, Cosmos Uzodinma ya sanya wa hannu, ta ce Ministan ya ba da umarnin ne lokacin da ya kai ziyarar gani da ido a Unguwar Mpape, inda motsin kasar ya fi aukuwa.

Binciken farko ya nuna cewa zai iya yiwuwa yawan fasa duwatsu da hakar ma’adinai da kuma gina rijiyoyin burtsatsen da ake yi da injuna masu hakar kasa ne ke haifar da motsin kasar.

Daga nan sai Ministan ya dakatar da wadannan hake-hake har sai bayan an kammala bincike don gono musabbabin wannan motsi wadda ta tayar da hankalin mazauna Abuja.

Haka zalika a wata sanarwa da Babban Daraktan Cibiyar Binciken Gine-gine da Tituna, danladi Matawal ya fitar, ta yi gargadin cewa kada Najeriya ta dauki batun motsin kasar da ya faru a Abuja da wasa.

Ya ce tabbas akwai bukatar gwamnati ta gaggauta binciko musabbabin faruwar wannan motsin kasa na Abuja, sannan ta fito da tsarin da zai magance sake faruwar wannan motsi, wanda ake kyautata zaton kila dalilin hakar kasa ya haddasa shi.

“In dai akwai inda aka rarake a karkashin kasa ana gina titin karkashin kasa ko yin wani gini a karkashin kasa, to wannan gini kan iya kumbura jijiyoyin kasa su fara motsi.” 

“Su kansu mazauna Abuja suna matukar bukatar a horar da su matakan gaggawa da ya kamata su dauka cikin hanzari, idan irin haka ya sake faruwa.

“Idan kuma wannan motsi kaddara ce daga Allah, to fa sai a yi shirin fara kwashe mutane daga Abuja, domin ita babbar girgizar kasa takan fara ne da karamar motson kasa. Dalili, saboda karkatsewa da daddatsewar da igiyoyi ko jijiyoyin karkashin kasa suke yi ne ko kuma saiwoyin da suke rike da farantin da ke tallafe da jijiyoyin karkashin kasar su kansu,” inji Matawal.

Ya kuma kara da cewa, “Wato aman wutar duwatsu da girgizar kasa duk wasu bala’o’i ne wadanda Najeriya ba ta ma taba tunanin yi musu shirin ko-ta-kwana ba. To saboda ba a taba shirya musu ba, sai jikin mu ke ba mu cewa kamar ba mu ma san da su ba, ko kuma ba mu yarda za su iya faruwa a nan ba.”

“Zan ja hankalinmu da cewa wani ya ba mu labari cewa a inda ya ke a Mpape, inda jijjigar kasar ta fi karfi, kare ya fara ji ya na ta haushi ba kakkautawa. Domin idan ibtila’in girgizar kasa ce, to gargadin farko da jama’a za su fara ji shi ne dabbobi su fara firgita su na haushi, su na fafarniya.

“Za a ga karnuka sun kaure da haushi ba kakkautawa, maguna su kasa zaune, su kasa tsaye wuri daya, beraye su rika gig-gilmawa cikin gida ko cikin dakuna a guje, kuma a rude. Dawaki kuma su rika harbin iska da haniniya su na fizge-fizgen tsinkewa daga turakunsu.”

“Ba wani abu ba ne zai sa su rika yin wannan sai saboda maganadisun ji da saurarensu ya sansano kuma ya fizgo musu karkarwar da karkashin kasa ke fara yi a lokacin da jijiyoyin karkashinsa ke daddatsewa daga jikin farantin da ke tallafe da kasar baki daya.”

Ya ce mataki mafi sauki da kuma saurin dauka idan irin haka ta faru, to a yi gaggawar ficewa daga inda ake, a kwashi yara da kananan dabbobin da za a iya runguma, a runtuma a guje zuwa cikin fili ko sararin da babu gine-gine kusa.

Matawal ya ci gaba da bayar da wasu misalai da alamomin matakai har guda hudu masu nuni da cewa idan hakan ta auku, ko kuma ta fara aukuwa, to babu makawa girgizar kasa na tafe.

 

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu

Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni — Sarkin Musulmi