MSF ta magance yunwa a Pulka
kauyen Pulka da ke karamar Hukumar Gwoza a Jihar Borno, na dauke da adadin ’yan gudun hijira da yawansu ya kai kusan dubu 60, yana fuskantar matsaloli masu yawa da suka hada da karancin abinci da ruwan sha. Kamar yadda kungiyar Likitoci masu Aikin Sa-kai ta MSF ta sanar cewa a yanzu haka ta kutsa […]
kauyen Pulka da ke karamar Hukumar Gwoza a Jihar Borno, na dauke da adadin ’yan gudun hijira da yawansu ya kai kusan dubu 60, yana fuskantar matsaloli masu yawa da suka hada da karancin abinci da ruwan sha. Kamar yadda kungiyar Likitoci masu Aikin Sa-kai ta MSF ta sanar cewa a yanzu haka ta kutsa yankin, inda take aikin rarraba kayan agaji ga al’ummar Pulka, a daidai lokacin da al’ummar yanki suka ninka sakamakon tashe-tashen hankula. Shugaban MSF a Najeriya, Luis Eguiluz ya ce akwai jami’an kungiyar tasa 200 da suke ayyukan jin kai a yankin a kullum, musamman abin da ya shafi kiwon lafiyar dubban ’yan gudun hijirar da ke wurin wadanda galibinsu mata ne da kananan yara. Makonni biyu da suka gabata ne Mista Eguiluz ya ziyarci kauyen Pulka a karon farko don gane wa idonsa halin da dubban al’ummar garin ke ciki na matsanancin hali. Duk da kai daukin na MSF, mata da dama sun koka kan wahalar da suke sha kafin su samu magunguna.
Shugaban na MSF ya kara da cewa, duk da cewa garin Pulka ya kai kimanin kilomita 100 daga Maiduguri, yana zaune lafiya sakamakon kariyar da sojoji suke bai wa yankin, masu ayyukan agaji suna iya zwau yankin ne kawai ta jirgin sama. MSF na kula da lafiya a matakin farko da na biyu, yayin da adadin mata da yara da dama ke bukatar kular gaggawa a fannin haihuwa da lafiyar kwakwalwa. Ganin da dama sun samu firgici kan kashe makusantansu a gabansu da kuma matsalolin fyade, don haka kula da lafiyar kwakwalwa abu ne da ake matukar bukata a wurin cikin gaggawa, yayin da MSF take tabukawa wajen ba da taimako a wannan fannin. Shugaban MSF din ya ce matsalar ruwan sha abin lura ce lura da yadda garuruwan da suke da duwatsu da yadda mata ke dadewa a kan layi domin samun ruwa a ’yan famfunan da aka samar. Yanzu haka akwai yara kusan dubu 15, a sansanin, wadanda da yawa daga cikinsu kodai an kashe iyayensu ko kuma sun bata. Baya ga ayyukan da MSF ta shirya, yaran nan suna zaune ne kawai tunda da makarantu sun hutu. Eguiluz ya sake cewa wasu kungiyoyi masu zaman kansu da suke gudanar da ayyuka a Pulka suna fama da matsalar rashin kayan aiki kamar isassu kuma kwararrun ma’aikata sannan aikin na yi musu yawa saboda yawan mutane. Haka kuma yadda ’yan gudun hijira suke tururuwar shiga Pulka na kawo matsalar rashin wajen kwana. Yawan ’yan gudun hijira da ke Pulka sun mamaye garin da muka tantunan kwana, wanda hakan ya janyo matsala ga mutane masu dawowa garin. “Yanzu haka akwai akalla mutum 7,000 da suke bukatar wurin kwana. Daga cikinsu, akwai 6,000 da suke zaune a waje a cikin sanyi,” inji Eguiluz. MSF tana lura da yanayin da ake ciki saboda tsoron barkewar annoba kamar bakon dauro da sankarau da ke aukuwa saboda karancin wurin kwana.