MSSN ta buƙaci Musulmi su rungumi fasahar sadarwa

Ƙungiyar ta ce akwai buƙatar Musulmi su rungumi fasahar sadarwa don ci gaban al’umma.

MSSN ta buƙaci Musulmi su rungumi fasahar sadarwa

Ƙungiyar Ɗalibai Musulmi ta Ƙasa (MSSN), reshen Jihar Kano, ta yi kira ga Musulmi da su rungumi fasahar sadarwa ta zamani da ƙirƙire-ƙirƙire don ci gaban al’umma.

MSSN, ta yi wannan kira ne cikin wata takarda da Shugaba da Jami’in Hulɗa da Jama’a na ƙungiyar a jihar, Dokta Abubakar Hassan Inuwa da Ibrahim Abbas Adam suka sanya wa hannu.

Ƙungiyar ta nuna cewa ya zama dole Musulmi ya samu ilimin fasahar zamani domin kada a bar shi a baya.

Ta kuma jaddada muhimmancin neman ilimi tare da koyon sana’a domin dogaro da kai.

Har ila yau, ta ce akwai buƙatar a haɗa karfi da ƙarfe tsakanin gwamnati da iyaye da sauran jama’a wajen cusa wa matasa kyawawan halaye nagari don daƙile shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da harkar daba.

“Harkar daba da shan miyagun ƙwayoyi abubuwa ne da suka addabi matasanmu. MSSN ba ta goyon bayan duk wasu al’amura na ɓatanci da ɓarnatar da dukiyar al’umma ko gwamnati da matasan wannan zamani suka yi da sunan zanga-zanga.”

Aminiya ta ruwaito cewa taron da MSSN ta saba shiryawa ga dalibai a lokacin hutu (State Islamic Vacation Course SIVC) mai taken ‘Mahangar Musulunci a fagen Fasahar zamani da ƙirƙire-ƙirƙire” ya samu halartar tsofaffin shugabannin ƙungiyar.

Daga cikin waɗanda suka halarta sun haɗa da Farfesa Muhammad Babangida da Dokta Abdulhadi Uba Gabari da wakilin Shugaban Ƙungiyar na Ƙasa Sadiq T. Sadiq da Sheikh Yahaya Shehu Maimota da Sheikh Yusuf Jaafar Dalha da sauran jama’a da dama.

Dalilin da ba zan bai wa Gwamnatin Tinubu shawara ba — Sarki Sanusi

Hamas da Isra’ila sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

HOTUNA: Yadda aka yi bikin tunawa da mazan jiya a faɗin Nijeriya

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana