Mu daina la’akari da jam’iyya, mu rika duba halayen ’yan takara?
Sunan PDP ya riga ya gama lalacewa a idanuwan duniya, kuma girmanta idan tana da shi, ya gama faduwa, tun ma ba a idanuwan ’yan Najeriya da suka ci kwakwarsu danya a hannunta ba, har ma da sauran mutanen duniya da suka san wainar da mulkinta ya toya a Najeriyar.Tun lokacin da nake jin sunan […]
Sunan PDP ya riga ya gama lalacewa a idanuwan duniya, kuma girmanta idan tana da shi, ya gama faduwa, tun ma ba a idanuwan ’yan Najeriya da suka ci kwakwarsu danya a hannunta ba, har ma da sauran mutanen duniya da suka san wainar da mulkinta ya toya a Najeriyar.
Tun lokacin da nake jin sunan PDP, ba ta taba yin farin jini ko kwarjini a idanuwana ba. Wannan kuma saboda tun daga sunanta na ji na tsane ta, abin da ba zai rasa nasaba da kabilanci da bangaranci da ke raina ba. ANPP, takenta shi ne ‘NASARA.’ Ita kuma PDP, takenta shi ne ‘POWER.’ To sai na ji na tsani wadda takenta ba yarena ba ne kuma dan takarar shugabancin kasa a karkashinta ba Musulmi ba ne kuma ba dan yankina ba.
Babban abin da ya kara dagula harka tsakanina da wannan ‘Shegiyar Uwar’ shi ne mulkin tabargazar da ya faru a karkashin shugabancin Obasanjo. Sai abin ya zame mini uku, ga shi dai ba Musulmi ba ne, kuma ga shi a jam’iyyar da ba na so kuma kare da karau, ga mulkin nasa ya kasa taka rawar gani.
To sai dai kuma tun a wancan lokacin, Allah Ya taimake ni da na tsaya na yi wani nazari. Na ce me zai sa in tsani Obasanjo haka? Shin Shugaban kasa shi kadai ne mai ikon tafiyar da komai da komai, ta yaya za a yi a ce babu mai iya taka wa Shugaban kasa birki? Ba zai yiyu ba, domin ai Shugaban kasa ba Allah ba ne, kuma Allah ne kawai ba shi da mai taka masa birki ga duk abin da ya nufi yi.
A karkashin wannna tunani ne, sai na ce to idan na tsani Obasanjo, domin me ba zan tsani Mataimakinsa Atiku ba, tunda duk wata wainar a tare suke toya ta? Ya aka yi na mance da su Babangida, wadanda su ne jiga-jigan da suka daure wa Obasanji gindi har ya kai ga wannan mulki? Ina su Masari da sauran Musulminmu ’yan kabilarmu da suke majalisa? Su duk aikin me suke yi?
karshe dai sai na fahimci cewa, idan dai har domin Obasanjo yana Kirisata ne kawai nake kiyayya da shi, to wannan daidai ne. Idan kuma saboda tabargazar mulki ne da sace dukiyarmu, to ban yi adalci ba, domin akwai ’yan uwana Musulmai kuma ’yan yankina na Arewa, wadanda duk abin da ake yi tare da su ake yi. Ashe ba adalci ba ne in ki Obsanjo shi kadai, ya kamata in ki wannan gwamnatin ce ta PDP gaba dayanta. Da Musulmin cikinta da wanda ba shi ba, Bahaushenta har ma kabilarta.
To wannan matsayar da na kai a rayuwata, ita ce ta fara dusashe kaifin kabilanci da bangaranci a rayuwata (duk da cewar akwai wannan jin cewa lalle babu wanda zan so face Musulmi dan’uwana) ta kuma kara zafafa wutar kiyayya tsakanin birnin rayuwata da birnin jam’iyyar PDP. Har ma ta kai da an ce kai dan PDP ne, to lalle ni a wurina, ba ka da kima ko daraja.
Hakan ta haifar da duk inda gwamanan PDP yake, duk yadda yake yin aiki wa al’ummarsa, ni ba na gani, duk yadda yake kokarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro tare da kyautata jin dadin al’ummarsa, to in dai domin ni in gani in yaba yake yi, to ya bata wa kansa lokaci.
Ina iya tunawa, a cikin wannan yanayin ne na yi tafiya zuwa garin Kano, a kan hanyata sai na bi ta cikin Jihar Katsina, inda na tarar da an kawata garin da hasken wutar lantarki sosai da sosai gwanin ban sha’awa, har sai da na fara jin a raina kamar ba a Na jeriya nake ba. Amma da yake gwamanansu dan jam’iyyar PDP ne, a haka na fice garin nan, ban bari bakina ya fadi alkhairi guda a kansa ba. Har ma ina ta fatar in ga abin da ba daidai ba domin in samu damar sukar gwamnan.
A lokacin da guguwar 2007 ta kwaso kayanta, sai guguwar sauya sheka ta kwaso nata kayan suka hada a waje daya. Inda a wannan lokacin ne mutanen jam’iyyar ANPP da nake ganin kimarta, suka fara ficewa suna komawa PDP. To saboda ni kuma waccan kiyayyar da nake wa PDP din, sai ya zama cewa duk wanda ya fice daga ANPP zuwa can, nan take aibinsa yake bayyana a idanuwana, sai in gano cewa ashe dai, ko lokacin da yana ANPP ba na kirki ba ne, soyayyar da nake yi wa jam’iyyar ce ta hana in ga ne.
Kai in dai takaice maka zance, a haka zuciya take ta kai ta kawo, ta kulla wannan ta kwance, kai har fa ta kai da ba mai sauran kima a idanuwana, face Janar Muhammadu Buhari, duk da cewa shi ma ya bar ANPP din, amma ya dauko sabuwa ne bai shiga PDP ba. Sai kuma Attahiru dalhatu Bafarawa, wanda shi kuma ya dauko DPP. Na karshe shi ne rigiji gabjin da ko motsawa ma bai yi ba, wato Ahmad Sani Yariman Bakura.
A karkashin wadannan mutum ukun ma, akwai wani abin da ya biyo baya a rayuwata. Me ya sa Bafarawa ba zai bi Buhari ba, me ya sa kuma Yarima shi ma ba zai bi Buhari ba? Domin ina yi wa Janar Muhammadu Buhari kallon jirgin Annabi Nuhu ne, wanda duk wanda bai shiga cikinsa ba, ni a idanuwana ba ya tsira. Kuma cikin ikon Allah sai na ji wai duk na fi son Janar Buhari, sai kuma mataimakinsa Pastor Tunde Bakare. Ranar sai na tambayi kaina! Me ya sa kake son Tunde Bakare alhali ba Musulmi ba ne? Nan take na gano ashe dai karya nake yi, domin duk dalili na karshe da ya sa ba na son Obasanjo a kebance shi ne domin yana Kirista, to Pastor din fa?
Yanzu dai abin da ya kawo karshen zancen shi ne, ta ci ta gyare kuma ta garwaye! Kowa ya shiga cikin kowa, ANPP, DPP, APGA da sauransu sun zama APC, ita kuma PDP ta garwaye da APC. Maganar daya ce kuma ba abin da ya canza. Duk wanda yake cikin APC ko kuma PDP, to dayan biyu, ko dai ya baro jam’iyyarsa ne ya dawo wata jam’iyyar, ko kuma tun azal yana nan bai taba zuwa ko’ina ba.
Abin da dai nake son in ce shi ne: Su ne suke mulkin tun daga 1999 har zuwa yau, kuma su ne ke neman ci gaba a 2015. Eh, su mutanen ba! Sunan jam’iyya wata karyar banza ce da ake ruduwarmu da ita. Don haka me ya rage? Mu tsaya mu kwantar da hankalinmu, ai kowa ya san nakwarai kuma ya san mugu, kada mu yi la’akari da jam’iyyar kowa, mu yi la’akari da halayensa. Domin ni na gano cewa hatta PDP da nake matsananciyar gaba da ita, Bakar tukunya ce kawai, amma za ta iya fitar da farin tuwo.
Babi (08033186727), ya rubuto daga Sakkwato