Mu dora shugabanni bisa ma’auni
Tun bayan samun ’yancin kai a Najeriya, kullum an fi ganin kimar darajar ayyukan raya kasa da kyautata rayuwar al’umma da shugabannin farkio suka gudanar. Domn haka a kullum sai karya ’yan siyasa ke yi da sunayn magabata irin su Malam Aminu Kano da Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato da Abubakar Tafawa balewa da Zik […]
Tun bayan samun ’yancin kai a Najeriya, kullum an fi ganin kimar darajar ayyukan raya kasa da kyautata rayuwar al’umma da shugabannin farkio suka gudanar. Domn haka a kullum sai karya ’yan siyasa ke yi da sunayn magabata irin su Malam Aminu Kano da Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato da Abubakar Tafawa balewa da Zik da Awolowo. Sai kuma ga shi an smau masu fakewa da Janar Muhammadu Buhari; wasu sun yi sun ci zabe, wasu kuwa duunsu ta tonu.
Janar Muhammadu Buhari kusan a ce shi kadai ya rage a jerin shugabanni da suka nuna matukar damuw akan halin da kasar nan ke ciki. Don haka ma yake ta yin tsokaci kan matsaslar tsaro da halin tattalin arziki da kasar nan ke fama da shi. Ya yi maganganu masu ma’ana kan harin bama-bamai da ka kai Nyanya a kusa da Abuja, kuma kwana nan ya yi tsokaci kan halin tattalin arzikinmu da kalubalen tsaro.
A kodayaushe manufar wannan bawan Allah ia ce yadda talaka zai samu maslahar rayuwa; a samar da ayyukan yi ga matasa, ta yadda batagari ba za su rika yin amfani da su wajen cimma son zuciyarsu ba. Kowa ya san rashin da’a da tarbiyya al’umma ta rasa shi yasa al’amura suka tabarbare a kasar nan.
Wata illa da ’yan siyasar wannan zamani suka samu nasara a kan al’ummar kasa, ita ce ta raba kai, ta hanyar nuna bangaranci da bambanci addini da na kabilanci. To tunda mun yarda Allah ne ya hada mu a kasa daya, wajibi ne mu himmatu wajen aiwatar da ayyukan da za su hada kawunan al’ummar kasar nan. Domin karfinmu yana nan a cikin hadin kanmu.
Idan dan kasuwa ya hango abin da zai cutar da kasuwanci, hakki ne a kansa ya ankarar da ’yan uwansu don su hadu, a gudu tare a tsira tare; ko wani ya hango wata cuta da ka iya yaduwa a cikin al’umma, wajibi ne ya ankarar da masu hankali, don su yunkura wajen samar wa al’umma mafita. Shi ma likit ako jami’in kula da lafiya idan yaga wata cuta za ta yadu a sanadiyyar rashin tsafta, ko daukar matakan kariya, ya zama dole a kansa, ya nuna wa mutane mafita, tun kafin dimbin jam’a su kamu.
Matukar hukumomin kasar nan da gaske suke yi, wajen ceto al’umma daga shiga mawuyacin hali, to hakki ya rataya a kan ma’aikatun yada labarai da Hukumar Wayar da Kai ta kasa NOA, su rika bayyana wa al’umma halin tattalin arziki da zamantakewa da tsare-tsaren siyasar kasa, kai har ma da tsarin difulomasiyyarmu; don ta haka ne idan mun ziyarci wasu kasashen duniya za mu zamo jakadu nagari ga kasarmu ta haihuwa – Najeriya. Ai sanin kowa ne Janar Muhammadu buhari ya taba furta cewa “Najeriya ita ce kasarmu, kuma ba mu da wata kasar da ta fit a, don haka dole ne mu tsaya cikinta, mu kyautata.” Babu lokacin da ya dace a yi amfani da wadannan kalamai kamar irin wannan lokaci da muke ciki.
Ya zama dole ga daukacin ’yan Najeriya, mu hada karfi wajen tunkarar duk wani kalubale da ya zame mana karfen kafa. Mu dora shugabanninmu a kan ma’aunin yin daidai da akasin haka. Mu yi kokarin sanin wadanda suka dace su mulke mu. Mu kuma rage kwadayin mulki da abin duniya. Don haka nike yin kira ga ’yan kishin jam’iyyar APC da su samar da manhajar kyautata rayuwar al’umma da tabbatar da adalci, ta yadda idan allah Ya ba su mulki ko aka samu sauyi a kasar nan, kada su tafka kura-kuran da jam’iyyar PDP ta yi a kasar nan. Kuma idan PDP ta ayarda ta yi kuskure da ganganci, to su hada kai da masu nufin gyara ba tare da son rai, don samar da mafita daukacin al’ummar Najeriya.
Lokaci ya yi da za mu yi shuka da iri mai kyau, ta yadda za mu girbi hatsi mai kyau. Idan kuwa muka ki, to za mu dawo muna ta kururuwar ayyukan Buhari nagari, amma mun ki yin koyi da su. Idan kunne ya ji, to jiki ya tsira!
Alhaji Isyaku Umar dan Hadeja, Malam-Madori, Jihar Jigawa 08061572260.