Mu dubi Arewa kafin zaben 2015

Na fara ne da yi mana tuni kan lallai mu dubi halin da Arewa ke ciki, tun kafin zaben 2015, inda Shugabannin da ke kulla wa al’umma makirci. Irin halin da yankin Arewacin Najeriya yake ciki abin takaici ne, ganin yadda wasu ke hankoron ganin shugabannin wannan kasa sun ci gaba da mulki. Duk wani […]

Mu dubi Arewa kafin zaben 2015
Mu dubi Arewa kafin zaben 2015

Na fara ne da yi mana tuni kan lallai mu dubi halin da Arewa ke ciki, tun kafin zaben 2015, inda Shugabannin da ke kulla wa al’umma makirci. Irin halin da yankin Arewacin Najeriya yake ciki abin takaici ne, ganin yadda wasu ke hankoron ganin shugabannin wannan kasa sun ci gaba da mulki. Duk wani wanda yake zaune a ko’ina ne, indai a kasar nan ne, to yana sane da irin halin ni ’yasu da yankin Arewa maso Gabas ke ciki, musamman abin da ya shafi rikicin Boko Haram da ’yan gudun hijira. Kai ’yan arewa sun zama ’yan bora a kasarsu ta haihuwa. Kaico!
 A fili take, komai ya durkushe a yankin Arewa, sakamakon  hare-haren ‘yan ta’adda da rikice-rikicen addini da kabilanci da na siyasa, wanda hakan ya jawo mummunan koma baya a Arewa, musamman ta bangaren hasarar rayuka da dukiyoyin al’umma ga talauci da rashin aikin yi ga mummunan bangaranci da karan-tsana da ake nuna mana. Sannan ga rashin adalci da tausayin talakawan Arewa.
 Duk da wadannan masifu da na lissafo, wadanda suke faruwa a yanzu haka. Abin haushi akwai wadansu gurbatattun jahilai, kuma mahaukata da marassa tunani, balle hankali, wadanda ‘yan Arewa ne, amma sun dana bakarsu, suna jira 2015 ta yi, domin su jefa wa shugaban kasa mai ci a yanzu, wato (Goodluck Ebele Masu kulla makirci kuri’ar su. Wani abin takaici ma, ba wai jefa kuri’a ba, kawai, nasan akwai manyan Arewa da suke shirye wajen ba da kudin su, domin kawai su ga an sake zabar Masu kulla makirci, ya koma kan kujerar sa ta shugaban kasa.
Kuma bisa ga dukkan alamu, wadannan jahilan sun fara nuna kansu a fili, domin na ji gwamnoni har sun yi mubayi’a ga mai malafa, da kuma wasu shashashu wai (TAN), to wallahi dan siyasar da ya alkanta kansa da Masu kulla makirci (maimalafa) zai sha mamaki.
 Duk da cewa, nasan siyasa ra’ayi ce, amma shi ra’ayi yana kasancewa ne bisa wani dalili. To ya kai/ mai niyyar zaben masu kulla makirci a karo na biyu, mene ne dalilin ka/ki? Nasan amsar ba za ta wuce saboda kudi ba ne, ko mukami. To wallahi ya kai/ke talakan Arewa, mu shafa wa kan ruwa tunda wuri, kafin mu debo ruwan dafa kanmu, da kanmu. Domin duk abin da za a ba mu, to zai kare, kuma ya barmu cikin tashin hankalin da musifa, irin wadda muka fara gani a yanzu.
Duk mai hankalin da ya san matsalar Arewancin Najeriya, a fili take, wanda ni a nawa gani, da ana da niyyar magance ta, to da yanzu ta zama tarihi, to, amma saboda akwai masu amfana a sakamakon hakan shi yasa kullum ake ta sake rura wutar rikicin.
 Duk wanda ya zabi Masu kulla makirci ya yarda kashe-kashe ya ci gaba: Da  cin hanci yaci gaba;  talauci da zalunci yaci gaba; da munafurci yaci gaba!
Muna rokon Allah  ya yi mana tsari daga wadannan abubuwan, kuma duk wanda ya zabi Masu kulla makirci da sunan Arewa, idan har da hakki na a ciki, Allah ban yafe ba.
A karshe dai ina sake kira da jan hankali ga talakawa da kar mu sake wani dan iska ya zo ya yaudare mu, da abin da bai kai, ya kawo ba, wanda zai kare, kuma ya bar mu cikin masifa da bala’i.
Kafin na ajiye alkalamin na, ya zama dole na yi addu’a wa kasar mu da kuma wannan yanki namu na Arewa.
Ya Allah duk wanda yake da niyyar sake goyon bayan masu kulla makirci, ka yi mana maganinsa kafin lokacin zaben, domin ba ya son zaman lafiyar bayinKa.
Ya Allah duk ’yan uwan mu da suke cikin halin na musifa da bala’i, musamman marasa lafiya da ‘yan gudun hijira, ka kawo musu saukin rayuwa.
Ya Allah ka ba mu shugabanni adalai masu tsoron ka, kuma masu son jama’a. Allahumma-Amin!
Kwamared Gamawa, Jihar Bauchi Najeriya  (Sardaunan Gamji kuma dan kishin kasa). [email protected]. 07068854446

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya