Mu farfado da martabar Arewa

A duk lokacin da aka yi maganar yankin Arewacin kasar nan, mafiya yawan mutane suna nuna matukar damuwa bisa yadda al’amura ke tafiya  a yankin idan suka yi waiwayen yadda abin yake a baya da yadda yankin ya kasance abin alfahari a wannan kasa tamu mai albarka.Haka kuma kowa yasan cewa yankin Arewacin kasar nan, […]

Mu farfado da martabar Arewa
Mu farfado da martabar Arewa

A duk lokacin da aka yi maganar yankin Arewacin kasar nan, mafiya yawan mutane suna nuna matukar damuwa bisa yadda al’amura ke tafiya  a yankin idan suka yi waiwayen yadda abin yake a baya da yadda yankin ya kasance abin alfahari a wannan kasa tamu mai albarka.
Haka kuma kowa yasan cewa yankin Arewacin kasar nan, yanki ne wanda ke da muhimmancin gaske a kasancewar Najeriya kasa daya kuma al’umma daya tun ma kafin kasar nan ta samu ‘yancin kai a shekara ta 1960.
Sannan yankin Arewa ya kasance yanki da Allah ya yi wa albarka da kasar noma da kiwo da kyawawan al’adu da mutunta juna da kuma karrama ‘yan uwan mu da ke makwaftaka da yankin, wadanda ke  zaune tun shekaru aru-aru. Bisa wadannan misalai, yankin Arewacin Najeriya ya zamo abin alfahari ga daukacin al’ummar kasar nan da kuma shugabannin da suke rike da madafun iko a wancan lokaci, duk da cewa yanzu yankin ya zamo cikin wani yanayi da ya zama wajibi a tashi a hada hannu, domin sake farfado  da martabar sa ba tare da nuna kasala ba.
Wannan  ne ta sanya mutanen da ke son ganin yankin ya samu ingantuwa  da gyare-gyare a karkashin inuwar da bature ke kira “ Northern Reformation Initiatibe” watau kungiyar farfado  da martabar Arewa  tare da kokarin hada kan al’ummar yankin daga dukkan jihohin yankin 19 domin kyautata tsaro da zamantakewa da siyasa da tattalin arziki. A rika tuntubar al’ummomin da ke jihohi 19 na yankin Arewa, tare da  yunkurin fara aikin inganta rayuwar talakawa, musamman ga daukacin manyan mutanen da ke yankin   domin farfado da yankin.
Bugu da kari, mu hadu mu yi  aiki  wajen tabbatar da ganin an ci gaba da samun cikakken hadin kai tsakanin yankin Arewacin kasar nan da sauran sassa, ta yadda za a kara samun dangantaka mai kyau a matsayin al’ummma daya, kamar yadda abin yake a lokutan baya kafin al’amura su tabarbare.
Lallai mutanen Arewa su yi shirin kyautata zamantakewar daukacin al’ummar da ke yankin da kuma wadanda suke mazauna yankin,  domin inganta kaunar juna da kare mutuncin juna, ta yadda  kowa zai amfani zaman tare.
Akwai sahihan mutane masu kishin kasa da ke bukatar goyon bayan daukacin al’ummar kasar nan domin aiwatar da ayyukan da za su amfani duk wani dan kasa . Lallai mu yi  hadin kan kasa da kuma bunkasa mutun ta kowane fanni,  ba tare da nuna wariyar addini ko kabila ko kuma wani ra’ayi da ya shafi siyasa ba.
Mu kafa kungiyoyin da za su yi fafutukar kare martabar yankin Arewacin kasar nan da inganta hadin kai tsakanin yankin da kuma sauran sassa na kasar nan,  musamman ganin cewa lokaci ya yi da za a tabbatar da kasancewar Najeriya kasa daya.
Kowa ya himmatu wajen fito da tsare-tsaren kyautata rayuwar al’umma, ta yadda za su fahimci irin kokarin da ake yi na ganin yankin Arewa ya samu martaba da daraja a kasa da kuma kyautata dangantaka tsakanin yankin da sauran sassan kasar nan.
Da yardar Allah, Arewa za ta kasance wani wurii na kawo cikakken hadin kai da kaunar juna tsakanin sassan kasar nan, tare da bunkasa zaman lafiya da mutunta juna bisa  la’akari da yadda ubangiji ya hada zaman mu tare.
Alhaji Abubakar Adamu, mai fafutikar hadin kan Arewa 09030946645.

 

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50