Mu guji bata shugabannin da suka yi abin kirki – Rimin Zayam

Yaya ka ga yadda uwar Jam’iyyar PDP ta kasa ta yi zaben shugabanninta? Eh, ba wani abu ne na daban ba, siyasa ce kuma kowa na da ikon zaben wanda yake so, kuma Allah Ya tabbatar da wadanda Ya ba su shugabancin jam’iyyar kuma suna da gagarumin aiki a gabansu.  Babban abin da muke so […]

Mu guji bata shugabannin da suka yi abin kirki – Rimin Zayam

Yaya ka ga yadda uwar Jam’iyyar PDP ta kasa ta yi zaben shugabanninta?

Eh, ba wani abu ne na daban ba, siyasa ce kuma kowa na da ikon zaben wanda yake so, kuma Allah Ya tabbatar da wadanda Ya ba su shugabancin jam’iyyar kuma suna da gagarumin aiki a gabansu.  Babban abin da muke so shi ne su karfafa dimokuradiyya, su rarrashi masu korafi da wadanda aka bata musu a baya, cewa su yi hakuri.

Shugabannin su samar da ingantaccen jagoranci da zai kai jam’iyyar ga nasara domin na tabbata tun farko wadanda suka shirya babban taron sun yi shiri mai kyau ba su yi wani abin da zai kawo rugujewar jam’iyyar ba. Dama abin da ya shafi siyasa dole ne wani ya so, wani kuma ya ki, in ma da wani abu na daban na bacin rai ina tunanin mun dauki darasi daga abubuwan da suka faru a baya kuma za su yi abin da ya dace, kuma babbar nasararmu mun yi taron lafiya an kammala lafiya na tabbata shugabannin za su yi abin da ya dace. 

Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya dawo Jam’iyyar PDP a matsayinka na wanda kuka fara jam’iyyar tare yaya ka ga dawowarsa?

Na farko dai Atiku mutum ne mai mutunci, dan siyasa ne gogagge duk da cewa akwai wadanda suka fi shi siyasar. Dawowarsa Jam’iyyar PDP zai taimake ta da irin mutanen da yake da su, Jam’iyyar APC ta yi babban rashi ba don komai ba da hannunsa cikin kawo gwamnatin APC, kuma zuwansa PDP zai taimaki PDP da abubuwa da yawa. Bayan mutanen da yake da su zai taimake ta da abin da ya shafi kudi da shawarwari. PDP ta yi nasarar samun gwarzo irin Atiku duk da cewa dama PDP tasa ce yana cikinta ne ya fita ya koma wata jamiyyar, saboda wasu dalilai. Kuma yanzu ya dawo mun gode wa Allah, amma duk da haka sai ya yi hakuri, ya yi hakuri da mutanen  da ya same su da kuma wadanda ya bar su, idan ba haka ba a karshe watakila abin da yake tsammani zai auku sai ya ga bai auku ba. Ita siyasa domin a yi nasara jama’a su amfana ake yin ta , kodayake akwai wadanda suke yin siyasa domin kashin kansu in ba su ba ta watse, kuma akwai masu yin siyasa don kishi a ganinsu da soja su dawo gara a yi ta yin siyasa. Saboda haka a matsayinsa na uba ya rika hangawa duk inda ya ga mutane suke so ya taimaka wa wannan gefe idan har ya taimaka wa jama’a suka yi nasara a kan abin da jama’a suke so to dimokuradiyya za ta dore amma kada a ce sai abin da mutum yake so kawai. Don in aka toge a haka in aka samu bacin rai sai ka ji zai yi wa iyayen gaba. Amma alhamdulilahi mun yi murna da dawowarsa domin Atiku gidansa ya dawo. 

Ko akwai wani jan hankali da za ka yi wa jama’a musamman ’yan siyasa da yake ga zabe na kara matsowa?

Jan hankalina bai wuce maganar da ake danganta ta da Mai girma Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ba, wanda ake yayatawa a kafafen sadarwa na Intanet cewa ya yi kalaman da ba su dace ba a kan marigayi Firimiyan Jihar Arewa Sardaunan Sakkwato Sa Ahmadu Bello (Allah Ya gafarta masa), da na ji wadannan kalamai sai na tausaya masa, kasancewarsa dan Arewa kuma Gwamna a jiha irin ta Kaduna. Yau, koda Sardauna na raye, idan ka dubi abubuwan ci gaba da ya yi wa Arewa da Najeriya balle bai ma duniyar. Ban san dalilin da ya sa ya yi wadancan kalamai ba. Yanzu Sardauna ko mutumin da ke kasar Ibo ko na Yarbawa ba zai fadi mummunar magana a kan Sardauna ba balle dan Arewa. Idan aka duba za a ga Sardaunan nan ya hada kan kasar nan ya yi makarantu da ayyukan ci gaba masu dama, ya gina jama’a da masana’antu ya tabbatar da gaskiya da adalci da ci gaban Arewa da Najeriya baki daya.  Idan har shi ya fadi wadancan kalamai, ina ba shi shawarar ya tuba ga al’ummar Arewa da iyalan Sardauna, ya ba su hakuri domin shi ma ya samu nasara ya yi koyi da gaskiya da sadaukar da kai da hazikanci irin na Sardauna. Idan yana ganin ya yi kuskure to ya nemi yafiya a wajen ’yan Arewa da kuma Najeriya, domin bai kamata ko maigadin gidansa ya mutu ya zo yana fadar munanan maganganu a kansa ba, balle mutum kamar Sardauna wanda ya yi shugabancin gaskiya da adalci, da kuma Shugaba Umaru Musa ’Yar’aduwa. 

Idan muka dawo jiha da kuma tarayya kana da abin cewa?

Abin da nake cewa jama’a su yi hakuri domin kasa tana cikin matsalar rashin kudi, su jama’a suna bukatar a yi musu aiki, don haka su kara hakuri, su kuma shugabanni su yi adalci ga wadanda suke shugabanta domin a samu inganta aiki da zama lafiya da ci gaba. Matsalar kuncin rayuwa da take damun talaka a yau a nemi hanyar da za a sawwaka musu a samu waraka.