Mu gyara halayenmu domin samun alfanun canjin
Dukkanmu mun san hannu daya ba ya daukar jinka. Don haka dole a hada hannu wajen yin gyaran. Sai kuma mu gyara halayenmu. Wani zai ce, muna da bukatar hanya da lantarki da tsaro da sauransu, me ya hada lamarin da halayenmu.Hausawa sukance: “Waiwaye adon tafiya”. Akwai halayen da jama’armu suke yi,wadanda suka saba da […]
Dukkanmu mun san hannu daya ba ya daukar jinka. Don haka dole a hada hannu wajen yin gyaran. Sai kuma mu gyara halayenmu. Wani zai ce, muna da bukatar hanya da lantarki da tsaro da sauransu, me ya hada lamarin da halayenmu.Hausawa sukance: “Waiwaye adon tafiya”.
Akwai halayen da jama’armu suke yi,wadanda suka saba da tsarin addini,da na zamantakewa, da ya kamata su gyara.
Jan kunne da nake son yi wa matasa,wadanda zamani ya rude su, su yi nazarin wannan maganar, su nisanci duk abin da zai sa su, maye, tun da ya saba da koyarwar addini, don samun rahamar Allah, da kuma samun, canjin da suke fadin.
Matasa ya kamata su lura, a duk lokacin da za su so mutum, su tabbata akwai halayensa, da suke burge su. Masu shaye-shaye su duba, shi janar din, da su ke kauna haka yake ne?
Idan sun bugu, za su iya mu’amula da mutune ne, har ma tsarinsu ya zama irin nasa. Alhalin kuma suna nuna wa duniya, shi ne abin kaunarsu, kuma suna alfahari da shi, idan kuma sun bugu, suka yi sata, ko kisan kai, idan har hukuma ta kama su,za ta daure su shekara takwas, a kurkuku. Ko a yanke musu hukuncin kisa, shi ke nan, ba su cikin wadanda za su sha romon canji. Don haka nake kiran dukkansu, masu irin wannan hali, da su daina, saboda aikin shaidan ne. Wasu an ce, suna buguwa ne, idan ransu ya baci, ko idan sun shiga damuwa.Don Allah ina son in tambaye su, iyayensu da ba sa buguwa, ba su taba shiga damuwa ba ne?Wasu cikin iyayen ma, sun rasa na su iyayen,ko ’ya’yansu da kuma abokan zamantakewarsu, wane bakin ciki ne ya fi wannan?Duk bai sa sun shiga wannan hali ba, da a ce wannan abin yana da kyau, da iyayensu ne, za su sayo musu shi. Tun da dukkan fafutukar da iyaye su ke yi,don yaransu ne.
Wata shawarata, kuma ita ce, don Allah wadanda suka bar makaranta, su koma, wadanda suka riga su ka girma kuma, su shiga yaki da jahilci, don su samu takardar kammala karatu. Wata kila za a kafa musu, wata masana’anta, ko kuma wani ci gaba da aka kawo garinsu, idan an ce su kawo takardar kammala karatunsu, don a dauke su aiki. Duk wanda ba shi da shi, ba ya cikin masu,samun alkhairi ke nan.
Ko kuma su samu sana’anar da za su dogara da ita, domin watakila za a zo tallafa wa masu kananan sana’o’i. In har ba su da abin yi, nan ma alkhairin ya wuce su ke nan. Ga shi kuma suna kan gaba,gaba wajen cewa: “Sai canji”
A hukumar ’yan sanda, su ma akwai nagari, akwai kuma masu neman gyara. Haka nan ma kotunanmu.Hakika, akwai alkalai, masu tsoron Allah, masu son tabbatar da gaskiya. Amma, akan samu akasin haka ga wasunsu. Dukkansu, ‘yan sanda da alkalan, mutane ne, masu kima da daraja a wajen al’umma, wadanda ake musu kallo a matsayin uwa, mai tausaya wa masu gaskiya da kuma kwato wa dukkan wanda aka zalunta hakkinsa. Amma, sau da yawa, ana jin kungiyoyin kare hakkin bil- adama, suna bin diddigin kwato wa talakawa hakkinsu.
Shugabannin ma’aikatu,sau da yawa suna hada baki da wasu daga cikin ma’aikatan, don su yi almundahana, ko a kara ma’aikatan bogi, ko kuma a yi kwangilar karya, ko a cinye alawus na ma’aikata, ta kowane bangaren. Hakkin da ya kamata,a bai wa masu zuwa taron bita, ko kuma na karin Ilimi,ba a ba su kudin mota da na guziri, shugabanni sun danne. Akwai kuma matsalar rashin kara wa ma’aikata girma, sai su yi shekara da shekaru suna nan a matsayi daya,ba wani ci gaba, da fatan za a duba wannan matsalar.
Masu kula da ma’ajiyar ma’aikata (store keeper). Wasunsu,su ma su kan yi ha’inci a ayyukansu, sukan dauka, su sayar ba tare da an sani ba.
‘Yan kasuwa, su ma suna da muhimmiyar rawa, da za su taka, na wajen gyaran al-amura, sau tari, ana kukan cewa wasu suna ha’inci a cikin kasuwancinsu. bangaren ‘yan awo , sukan buga kasan kwano ya lotse, idan abin da ake kasawa ne kuma, sai a sanya kanana a kasa, manya a sama. Mai zai hana, a gauraya kawai, ba tare da an yaudari masu saye ba?
Idan muka gangara wajen masu sana’o’in hannu, su ma ba a bar su a baya ba. Misali kafinta da tela, masu walda, da sauransu. Ana yawan kukan cewa, ba su cika wa abokan huldarsu, alkawarin da suke yi musu. Wani lokacin ma, sukan karbi kudinsu ko kayan aikin,kan cewa, somin tabi ne, idan sun gama sai a cika musa. Daga karshe, lamarin ya zama tamkar wasan yara, da ake cewa: “kulli kucciya”, wasu ma har ta kai su ga ‘yan sanda. Su rabu ba mutun ci.
Wasu ba su biyan bashin da suka karba ba, wasu kuma, hakkin marayu ne, a kansu ba sa bayarwa. Duk da cewa Allah ya ce :
“Duk wanda ya ci dukiyan maraya,wuta ya ci” (wa iyazu billah).
A maimakon su rike ta da amana, su mayar wa masu ita babu zalunci, yadda Allah ya yi umurni, su samu su tsira daga shiga wuta. Sai su nuna son kai.
Magidanta maza, su waiwayi, yaya zamansu yake da iyalansu. Suna rike su kamar yadda suke son a rike musu ’ya’yansu mata ne?
Iyaye mata kuma, yaya mu’a malarsu take da abokan zamansu, da ‘ya’yan mazansu, da ma surukansu, suna yi musu yadda suke fatan a yi wa na su ‘ya’yan ne, ko akasin haka suke yi?
Akwai yara masu biyayya ga iyayensu, amma wasu ko, ba haka suke ba. Su ma, sai su nemi gafara ga iyayen nasu, gafara ta hakika . Tun kafin su makara. Tun da yake da su da iyayen nasu, duka rai ne da su, babu wanda ya san gawar fari.
A nan za mu tsaya, da fatan, shi Janar da kuma iyalansa, da mu ’yan Najeriya,Allah ya lullube mu da rahamarsa amin. Abubuwan da muka fada, su zame mana alkhairin duniya da lahira. Idan akwai wanda muka bata wa rai. Ya yi mana afuwa, domin gaskiya tana da daci, Allah ya yi mana afuwa, ya kuma kara mana zaman lafiya da ci gaban kasarmu har abada. amen.
Ni ce Asiya Musa mai son canji ya tabbata a kasarmu, No.10 Amazing Grace Gwagwalada Abuja
Tel: 08074278877