Mu kasance masu yafiya ga junanmu
Tare da sallama ga daukacin makaranta wannan fili, Assalamu alaikum! Bayan haka, mun yi tambihi ga junanmu a makon da ya gabata, inda muka nuna muhimmancin kauna ga rayuwar al’umma. Mun ga yadda a zahiri kauna ke haifar da samun duk wani alheri na rayuwa, kamar zaman lafiya, karuwar arziki da sauransu. A wannan makon […]
Tare da sallama ga daukacin makaranta wannan fili, Assalamu alaikum! Bayan haka, mun yi tambihi ga junanmu a makon da ya gabata, inda muka nuna muhimmancin kauna ga rayuwar al’umma. Mun ga yadda a zahiri kauna ke haifar da samun duk wani alheri na rayuwa, kamar zaman lafiya, karuwar arziki da sauransu. A wannan makon kuma, za mu duba tasirin da ke tattare da yafiya ga junanmu.
Abin da tun farko ya kamata mu fahimta game da halitta shi ne, dan Adam, an halitta shi ne a matsayin kasasshe kuma mai matsananciyar mantuwa. Wannan mantuwa da Allah Ya halitta mu da ita, tana daya daga cikin abubuwan da suke taimaka mana har muke jin dadin rayuwa a doron kasa. Idan ba domin mantuwa ba, da za mu ci gaba da zama ne a cikin damuwa da firgici a kowane lokaci. Idan ba domin mantuwa ba, zullumin mutuwar dan uwanmu kadai za ta zama wani abu da zai gallabe mu duk tsawon rayuwa.
Kamar yadda Allah Ya fada mana, Ya halitta mutum ne a matsayin halifanSa a bayan kasa, wannan ce kuma kuma ta sanya mutum ke aron wasu yanaye-yanaye daga buwayar Sarki Allah. Misali, Allah Ya kasance mai yafiya ga bayinSa, musamman idan suka saba maSa kuma suka nemi gafara. Kan haka, shi ma dan Adam yake kasancewa, muddin dai yana bukatar zama lafiya cikin wannan duniya mai wuyar sha’ani. Watau, abu ne mai kima da muhimmanci ga mutum ya zama mai yafiya ga dan uwansa, idan ya saba masa, koda ya nemi gafara ko ma bai nema ba. Tasirin haka na da tsananin amfani, ba ga wanda ka yafe mawa kadai ba, a’a, har ma dai kankin kanka.
Tasirin yafiya ga juna ita ce, mutum zai kasance cikin farin ciki a duk lokacin da zuciyarsa ta zama sasakai, ba tare da radadin tunanin wani mummunan abu da dan uwansa ya aikata masa ba. Misali, idan wane ya saba mani, kuma na ji zafi sosai a raina, na dauki wannan al’amari na yi ta jinjina shi a raina. Tunanin abin zai ci gaba da gallaba ta, zai ci gaba da kuntata mani. Wannan kunci da zai dami zuciya ta, shi ne abu na farko da zai hana ni zaman lafiya da kwanciyar hankali. A wannan lokaci, me ya kamata in yi domin in samu sauki da sa’ida a raina?
Babban magani shi ne, in tursasa wa kaina, in yafe wa wannan mutum da ya saba mani, sannan in yi kokarin mancewa da abin da ma ya faru gaba daya. Zan yi haka ne saboda ni mutum ne mai mantuwa, akwai sinadarin mantuwa da ke gudana a jinina, don haka ba zan samu saukin aiwatar da yafiya da mancewa da abin da wane ya aikata mani ba. Haka kuma, ni mutum ne da nake da rauni, wanda haka ya sanya zan iya yin kuskure ni kaina, zan iya saba ma wani. Don haka, ni kaina zan bukaci wani da na saba mawa ya yafe mani, ya mance da kuskuren da na aikata a kansa. Ke nan, abin da nake so ga wani, dole ne ni ma in yi ma wani. Idan har ina son wani ya yafe mani, to kuwa ni ma sai na kasance mai yafe ma wani.
Abu na gaba da ya kamata mu fahimta shi ne, rayuwar nan ’yar kadan ce, ba ta da yawa. Idan muka ci gaba da bata lokacinmu wajen rikon junanmu, babu shakka za mu kasance cikin asara goma da goma. Wanda haka babu abin da zai tsinana mana na kirki a rayuwa. Kai ne kullum cikin kullutun bakin cikin abin da dan uwanka ya yi maka ba daidai ba? Haba dan uwa, haba ’yar uwa, mu kasance masu yafiya da mantuwa; mu mance da wannan kuskure, mu ci gaba da fuskantar wani al’amarin na rayuwa. Lallai kam za mu ci gaba da kasancewa cikin farin ciki da samun nasarar rayuwa, idan mun yi haka. Wani abu kuma da ya kamata mu kara sanyawa a zukatanmu game da yafiya shi ne, duk abin da wani ya aikata mana, ba zai tafi a banza ba, domin kuwa hukuncin abin da ke faruwa a duniya iri daya ne. Duk abin da ya je, shi ne yake dawowa. Abin da ka aikata ma wani, komai daren dadewa sai wani ya aikata shi a gare ka. Idan ka zagi wani, wata rana sai wani ya zage ka, idan ka ci amanar wani, wata rana sai wani ya ci taka. Don haka, me zai sanya ka bata lokacinka wajen kamuwa da ramuwa ga dan uwanka? Mu kasance masu yafiya ga juna!
Bisa ga wannan bayani, ni kaina Bashir mai kasawa, mai yawan laifi ga ’yan uwa da abokai da aminai; ina neman a yafe mani. Ni ma na yafe ma kowa da kowa. Duk wanda ya taba saba mani, ko da saninsa, ko bisa kuskure; na yafe masa har abada. Allah Ya shige mana gaba, Ya yafe mana dukkan kura-kuranmu da laifukanmu, amin!