Mu kauce wa siyasar maula don inganta turakun dimokuradiyya – Nasiru Daura
Nasiru Abubakar Daura, mataimaki ga wakilin mazabar Daura da Mai’aduwa da Sandamu, a ziyarar da ya kawo ofishin Aminiya ya yi matukar kokawa da siyasar maula sabanin kai koken ayyukan raya kasa a yankunan al’umma. Malam Nasiru a ziyarar da ya kawo bayan kammmala bitar kwana uku da aka yi wa masu gudanar da ayyuka […]

Nasiru Abubakar Daura, mataimaki ga wakilin mazabar Daura da Mai’aduwa da Sandamu, a ziyarar da ya kawo ofishin Aminiya ya yi matukar kokawa da siyasar maula sabanin kai koken ayyukan raya kasa a yankunan al’umma.
Malam Nasiru a ziyarar da ya kawo bayan kammmala bitar kwana uku da aka yi wa masu gudanar da ayyuka irin nasa a Abuja, wato kan sanin makamar aiki, ya bayyana yadda masu taimaka wa ’yan majalisar wakilai ke karbar koken al’ummar mazabunsu su mika wa wakilan don kai wa gaban majalisa, ko su yi amfani da kimarsu wajen sanya gwamnatin jiha ta yi wani kokari a kai.
Ya ce wakilinsu Alhaji Sani Sa’idu Fago da ke wakiltar mazabar Daura da Mai’aduwa da Sandamu ya aiwatar da ayyukan raya kasa a fannnin lafiya, inda ya samar da kananan asibitocin kwantar da marasa lafiya uku a Daura, uku a Mai’aduwa da biyu a Sandamu duk a shekariun 2016 zuewa 2017.
Kuma ya ce lokutan da aka yi fama da ambnaliyar ruwa, wakilinsu ya kai kokensu, inda Gwamnatin jiha ta yi hadin gwiwa da hukumar bayar da agajin gaugawa don shawo kan lamarin.
“A ambaliyar da aka yi ta daminar 2016, wakilinmu ya kai kukanmu inda ya dace, har ta kai ga Hukumar NEMA da ta kare muhalli da gwamnatin jiha sun yi hadin gwiwa don shawo kan lamarin,” inji.
Ya karkare batutuwansa da bayar da shawara ga al’umma kan lallai su fifita siyasar taimaka wa wakilansu da shawarwarin da suka dace, sabanin siyasar maula wadda ke kassara turakun dimokuradiyya.
A cewarsa: “A rika rubuto koke kan al’amuran da suka shafi kyautata rayuwar al’umma, sannan mu hada karfi da karfe wajen shawo kan matsalolin matsa, ta yadda za su daina ta’ammmalai da kayan shaye-shayen kayan maye. Tunda a kwananan wani taron da ’yan siyasa suka har Mai martaba Sarkinm Kano ya koka kan lamarin. Idan muka daina siyasar maula, muka jajirce kan yadda za a kyautata harkokin rayuwarmu babu wani dan siyasa da zai bai wa wani kudi ya sha kwaya don kare muradin son ransa. Lallai mu kiyaye, mu kyautata tarbiyya don inganta zamantakewa da tattalin arzikin kasarmu.”
Mataimakin na dan majalisar wakilan yankin Daura ya yi matukar yaba wa jaridar Aminiya kan yadda take wayar da al’umma, musamman na yankunan karkara. “Mutanen Daura na karanta Aminiya, kusan kowace Juma’a muna ganinta, muna fatan za ta ci gaba da wayar da kan al’ummma, musamman wadanda ke zaune a yankunan karkara.