Mu koyi darasi daga Shugaban Kenya
A makonni biyu da suka gabata ne Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya ya sauke manyan Jami’an gwamnatinsa, tare da maye gurbinsu cikin sa’oi 24 ba. Watau Sifeton Janar da kuma ministan harkokin cikin gida. Manyan jami’an gwamnatin sun rasa mukamansu ne, bayan wani hari da kungiyar al-Shabab ta kaddamar akan wasu ma’aikatan fasa duwatsu da […]
A makonni biyu da suka gabata ne Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya ya sauke manyan Jami’an gwamnatinsa, tare da maye gurbinsu cikin sa’oi 24 ba. Watau Sifeton Janar da kuma ministan harkokin cikin gida. Manyan jami’an gwamnatin sun rasa mukamansu ne, bayan wani hari da kungiyar al-Shabab ta kaddamar akan wasu ma’aikatan fasa duwatsu da ya janyo asarar rayukan mutum 36. Wannan mataki da Shugaba Kenyatta ya dauka na nuna ba sani, ba sabo ya daukaka kimar kasar a idanun duniya. Shugaban ya nuna wa duniya cewa tsaron rayukan jama’arsa da dukiyarsu shi ne abu mafi muhimmanci da ya sa a gaba, fiye da bukatunsa na siyasa. Sannan kuma ya tabbatar wa Kenyawa cewa ba su yi zaben tumun dare ba.
Ina ma a ce Shugaba Jonathan na Najeriya, zai yi duba da idon basira, ya kuma dauki darasin dake ciki. Ya fahimci cewa kare rayuka da dukiya, da mutuncin al’umma shi ne abu mafi muhimmanci da ya kamata a ce shugaba yasa a gaba.
Gara al’umma ta kasance cikin jin dadi da walwala da kwanciyar hankali, babu abin da ya fi wannan ga shugaba ako ina ne a duniya. Da wacce kima za a kalleka a idanun duniya, alhalin ka bar mutanenka cikin rashin tabbas? Kai kwai burinka a ce kai ne shugaba.
Idan shugaba ya kasa tabbatar da haka, to bai cancanci shugabancin ko dabbobi ba, balle mutane.
Idan muka lura za mu ga cewa manyan jami’an gwamnatin Kenyan da suka rasa mukamansu, bai wuce a ce sun yi sakaci akan rashin daukar matakin ko ta kwana daga fuskantar hare haren kungiyar al-Shabab, duk da kasancewar ba cikin kasar Kenya take da zama ba. Mu kalli rikicin kungiyar Boko Haram da ke faruwa a Najeriya, da ya kasance abin tattaunawa a kowane sako da lungun kasar nan, a cikin birane da kauyuka saboda munun al’amarin. Musamman a halin yanzu da a kullum salon maharan kan canza wurin kai hare haren su asassan Arewacin kasar nan. Stephen Dabis Baturen kasar Austrelia, da gwamnati ta gayyato domin taimaka mata ta gano bakin zaren da za a warware wannan matsala, kasancewarsa kwararre akan sha’anin sasanta kungiyoyin tayar da kayar baya da gwamnatocinsu. Ya bayyana sunayen tsohon babban
hafsan sojan kasar nan, Janar Azuibike Ihejirika da kuma tsohon Gwamna Jihar Barno Ali Modu Sherrif , a matsayin masu daukar dawainiyar kungiyar Boko Haram. Amma maimakon gwamnati ta damkesu, a gabatar da su gaban kuliya, a’a sai wata sabuwar soyayya ta kullu tsakanin mahukunta da mabarnatan, inda har masu tsaron lafiyasu na musamman aka ba su. Kowani lokaci suna da damar shiga fadar shugaban kasa ba tare da wata barazana ba. Tunda har lamurra sun zama haka to yaudarar ‘yan kasa ne, gwamnati ke yi wajen kawo kan karshen rikicin Boko Haram.
A wani jawabi da shugaba Jonathan ya taba yi a ranar 19 ga Yuni, 2012 a Jaridar Aminiya, shugaban ya gargadi ‘yan siyasa a kasar nan cewa ka da su bari bukatunsu na kashin kai ya jefa kasar a cikin tashin hankali, ya yi wannan gargadi ne a lokacin da yake jawabi ga ‘yan Najeriya mazauna kasar Brazil, inda ya ce bai kamata ‘yan siyasa su fifita bukatun kai akan bukatar ci gaban kasa da inganta jin dadin jama’a. To abin tambaya a nan shi ne, shugaba Jonathan ya yi wannan jawabi ne don ya burge masu sauransa, ko don ya nuna shi shugaba ne da ya sanya bukatun al’ummarsa a gaba fiye da duk wani buri nasa. Ga idanun duniya. Mutum ya kan kasance adali ne ba ta lafazi na Magana ba, a’a ta hanyar aikinsa ne ake gane haka. Idan muka lura da yadda Jonathan ke tafiyar da lamurran kasar nan, to lalle aikinsa ya sha bambam da abin da yake ikirari a kullum!
Hare-hare nawa aka kai a sassan kasar nan masu muni, wane matakin garambawul ya dauka ga hukumomin tsaron kasar nan? A wani mummunan hari da aka kai ranar 20 ga watan Janairu, 2012 a Kano, wanda ya zama mafi munin hari a yankin Arewa, inda sama da mutum 500 suka rasu lokaci guda.
Kisan ma’aikatan lafiya na Polio da aka yi a Kano cikin watan Fabrairu, 2013 ya zama irinsa na farko a tarihin Afrika. Sannan wani da ya maimaitu, wanda ya shafe wancan muni, ranar 28 ga Nuwamba, 2014 a masallacin Juma’a na Sarkin Kano. Allah kadai ya san yawan mutanen
da suka rasu. Inda a jawabin ta’aziyya aka ji mataimakin Shugaba Jonathan, Namadi Sambo ya yi subul da ba ka ya ce ‘ba hannun gwamnati a cikin wadannan hare-haren.’ Saboda rashin hujja da za su kare kansu. A ce gwamnati ta rika cewa ba ita ke kai wa ‘yan kasar ta hari ba, to kan wani dalili!
Akalla an kaiwa Sarakuna kusan guda shida hare-hare na yunkurin halakasu, inda aka rutsa da Sarkin Gwoza, wanda ya rasa ransa! Amma duk a wadannan abubuwa suka kasa jan hankalin gwamnati don kawo karshen wannan zubar da jinin bayin Allah. Kai ba mu tabo maganar hare-haren jihohin Arewa maso Gabas ba, wanda babu kalmar da za mu iya bayyanan irin mugun lahanin da aka yi wa yankin. Su kansu ‘yan majalisar tarayya sai da abin ya fara shafarsu sannan suka yi magana kan yadda tsaro ke kara tabarbarewa a kasar nan, ba wai don talakawa ba!
An samu mummunan ambaliyar ruwa kusan kashi 25 cikin 100 na sassan kasar nan a shekarar 2012, duk da gargadin da hukumar kula da yanayi ta yi kafin aukuwar lamarin, amma babu wani mataki da gwamnati ta dauka ga ma’aikatar kula da muhalli da sunan garambawul bayan afkuwar lamarin.
Mu kalli yadda ministoci suka rika cin karensu ba babbaka a ma’aikatu daban-daban da dukiyar kasa, musamman ministar man fetur da sauran masu ruwa da tsaki a harka. Me aka yi da sunan gyara? Sai ka rasa ina hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), ina alkalai da malaman addini da malaman jami’o’in kasar suka buya? ‘Yan jarida kadai ke motsi a kasar, ba don su ba da labaran ma ba za mu ji ba!
Da a ce Shugaba Kenyatta zai shugabanci Najeriya kona yini daya ne, to da lallai ya tura kusan dukkan manyan jami’an gwamnati zuwa ritayar dole, kafin ya biyo su daga karshe saboda sun gaza tafiyar da amanar kasarsu.
Kai amma fa Shugaba Jonathan ya dauki wani mataki na bazata a lokacin da ya ba da sanarwar sauke ministocinsa guda shidda. Sai dai abin takaici ya yi hakan ne domin daukar fansa ga gwamnonin jihohinsu da suka yi masa tawaye a jam’iyarsa ta PDP, inda suka kafa sabuwar PDP. Ba domin maslaha ga al’ummar kasa ba. Ya Allah ka azurtamu da shugabanni na kwarai a zaben 2015, idan Allah Ya Kai mu da rai! Halin da ake ciki ya tababtar wa da kowa a duniya kan cewa Najeriya ba ta yi sa’ar shugabanni ba.
Za a iya tuntubar Injiniya Jibril Abdul Daura ta wadannan layukan waya 08038997861, 08022997043.