Mu koyi darussan rayuwa daga wannan labarin (1)
Ya masu karatu, assalamu alaikum. Bayan haka, muna wa masu karatu maraba da sake saduwa a wannan fili. A wannan makon, muna dauke da labarin rayuwa, wanda ke dauke da wasu darussa da za su kaifafa mana tunani, sannan su yi mana jagora game da rayuwar nan tamu ta duniya. Allah Ya sa mu dace […]
Ya masu karatu, assalamu alaikum. Bayan haka, muna wa masu karatu maraba da sake saduwa a wannan fili. A wannan makon, muna dauke da labarin rayuwa, wanda ke dauke da wasu darussa da za su kaifafa mana tunani, sannan su yi mana jagora game da rayuwar nan tamu ta duniya. Allah Ya sa mu dace da alheri, amin. Mu sha karatu lafiya:
Wani bawan Allah ne ya je kasuwa, yana tsakar gudanar da al’amuran da suka kai shi kasuwar nan sai ya ji ladani ya kwala kiran Sallah. Kuma daidai wannan lokaci, ya daga kansa ke nan sai idanunsa suka fada kan bayan wata mata. Matar nan kyakkyawa ce sosai, kuma tana sanye da ingantattu kuma kyawawan sutura, kuma tana sanye da nikabi, wanda ya rufe mata fuska ruf.
Wannan mutum ya kura mata ido sosai, ya rudu da kallonta sai kawai ya ga ta juyo fuskarta zuwa shiyyarsa. Duk da cewa ba ta yi magana ba, amma ta kalli fuskarsa ta dukar da kai, alamar dai ta gaishe shi, kuma ta juya da sauri ta ci gaba da tafiya har ta shige wani lungu na kasuwar, inda ake sayar da suturun siliki.
Wannan al’amari ya saka mutumin nan cikin rudu sosai, kuma ya kamu sosai da son ganin wannan mata. Nan take zuciyarsa ta shiga kai-komo da tunanin abin da ya kamata ya yi. Wata zuciyar ta ce masa ya kyale matar nan kawai, wata kuma ta gaya masa cewa ya tafi ya yi alwalla domin yin Sallah, wata zuciyar kuma ta ce masa ya hanzarta ya bi matar nan. Ya dai rasa matakin da ya kamata ya dauka, inda daga bisani wata zuciya ta ce masa: “Ai ka bi matar nan kawai, domin yanzu ko ka je masallacin ma, an riga an gama Sallah, don haka idan ka dawo sai ka yi sallarka kawai.”
Nan take mutumin nan ya bazama da sauri zuwa bangaren da matar nan ta nufa cikin kasuwa. Ya yi ta kalle-kalle domin gano inda ta shiga, amma sai can daga nesa ya hango ta, har ma ta kusa zuwa karshen kasuwar, tana shirin fita waje. Shi kuwa ya kara sauri domin ya same ta, kuma daidai wannan lokaci sai ta waigo. Waigowar da matar nan ta yi, sai zuciyar mutumin nan ta riya masa cewa ai domin shi ta waigo, har ma ya sanya a ransa cewa har ma ta yi masa murmushi kuma ta daga hannu ta yafuto shi. A cikin tunanin nasa, sai ya ga kamar ma hannunta da kunshi mai zanen fulawa. Don haka sai ya kara sauri har da ’yar sassarfa domin dai ya isa zuwa inda take.
Yana ta bin matar nan kuma yana ta yin tunani iri daban-daban. “Shin wannan mata wace ce ita? Kila diyar wani hamshakin attajiri ce. To, me ya kawo ta cikin kasuwar nan, me take nema?” Saurin da yake yi ya fara wuce wuri, ya soma gudu-gudu, kuma bai damu da cewa cikin kasuwa yake ba, mutane kuwa suna kallonsa, shi kuwa bai ma kula da haka ba. Burinsa guda daya ne – ya samu isa wurin matar nan, wacce ta kara kudewa zuwa wata shiyyar kasuwar.
Mutumin nan dai ya hanzarta bin matar nan, ita kuwa sai kara yi masa nisa take, yana gani ta karya kwana ta shiga shiyyar masu sayar da kayan fada, kamar su takobi, bindigar gargajiya, kwari da baka, garkuwa da sauransu. Yana saurin bin bayanta dai, amma kafin ya isa wurin, sai ya ga ta karya kwana ta shiga bangaren masu sayar da man girki. Ya bar bangaren masu sayar da makamai, sai ya ga matar nan ta shiga bangaren masu sayar da fatu da kiraga. Ta dai yi masa nisa sai kara sauri take, shi ma sai kara azamar bin ta yake yi cikin sauri har da sassarfa.
“To, amma me ya sanya wannan matar ta ki tsayawa, sai ci gaba da tafiya take? Ko dai mahaukaciya ce?” Tambayoyin da mutumin ya rika yi wa kansa ke nan, kuma bai tsaya domin ba kansa amsa ba sai ya ci gaba da bin bayanta. Bai tsaya da bin ta ba har sai da ta fita daga cikin kasuwar, ta shiga cikin gari. Suka ci gaba da tafiya dai, tun suna cikin gari har dai matar nan ta fita zuwa bayan gari. Shi kuwa gogan naka yana ta wahalar bin ta zagai-zagai.
Kash! Masu karatu, za mu diga aya nan, sai kuma mako na gaba, inda za mu ci gaba da wannan mashahurin labari. A ci gaba da biyo mu, domin ci gaba da amfana da darussan da ke zizara mana sinadaran rayuwa. Allah Ya yi mana jagora, amin.
Za mu ci gaba