Mu koyi darussan rayuwa daga wannan labarin (3)

Assalamu alaikum, ya ku ma’abuta bibiyar wannan fili na Sinadarin Rayuwa; a wannan makon za mu karkare muku wannan labari, wanda muka faro makwanni biyu da suka gabata. Babu shakka, za mu karu da darussan rayuwa masu yawa daga cikinsa. Allah Ya sanya mu dace, amin. Ga ci gaban labarin: “A’a, yaya wannan mata za […]

Mu koyi darussan rayuwa daga wannan labarin (3)

Assalamu alaikum, ya ku ma’abuta bibiyar wannan fili na Sinadarin Rayuwa; a wannan makon za mu karkare muku wannan labari, wanda muka faro makwanni biyu da suka gabata. Babu shakka, za mu karu da darussan rayuwa masu yawa daga cikinsa. Allah Ya sanya mu dace, amin. Ga ci gaban labarin:

“A’a, yaya wannan mata za ta ce in jefa mabudin nan cikin rijiya, bayan kuma na tabbata wannan dakin a karkashin kasa yake?” Tunanin da ya yi ke nan, kuma da a ce akwai wani mutum kusa da shi, da ya nemi shawararsa kafin ya bi ummurnin matar nan.

“Jefa mabudin cikin rijiyar mana! A lokacin da kake kokarin biyo ni ai ana kiran Sallah ne amma duk da haka ka banzatar da ita, ka biyo ni nan.” Cikin shagube da wata ’yar dariyar keta mai kama da murmushi take gaya masa wannan magana, shi kuwa ya yi shiru bai ce komai ba kamar wanda ruwa ya ciwo. Ta ci gaba da maganarta da cewa: “Ka biyo ni daga kasuwa a lokacin Sallar La’asar, ga shi kuwa yanzu har lokacin Magariba ya kure? Kada ka damu, kai dai jefa mabudin nan cikin rijiya kawai kamar yadda na ce, ai kana son ka faranta mani rai ko?”

Mutumin nan cikin mamaki da alhini ya duka kasa-kasa, ya jefa mabudin nan cikin rijiyar, sannan kuma ya leka ciki, yana ji dan mabudin ya tsunduma cikin ruwa tsundum! Nan da nan kuma wani matsanancin tsoro ya rufe shi, cikinsa ya duri ruwa, sai ga shi yana jin kugi a cikin nasa kamar yana jin zawo.

“Yanzu ne za ka gane ko ni wace ce.” Abin da matar nan ta fada ke nan, sannan kuma ta cire lullubin da ya rufe idanuwanta. Mutumin nan ya sha mamaki da ya ga fuskar matar nan, domin kuwa shi da ya yi zaton zai ga kyakkyawar fuskar mace mai cike da kuruciya, sai ya ga ashe wata takunannar tsohuwa ce. Ga ta mummuna kuma fuskarta babu annuri ko kadan.

“Ka gan ni ko? Ka kalle ni da kyau dai sosai, sunana DUNIYA! Ni ce abin kaunarka, wacce ka bata lokacinka kana ta bi na tun daga kasuwa. Ga shi ka rasa Sallar La’asar da ta Magariba, har ma da Isha’i wace lokacinta ya shigo yanzu. Kana ta bi na domin ka same ni, to ga shi ka same ni amma a cikin kabarinka, domin kuwa nan ciki kabarinka ne kuma kai da kanka dai ka kulle shi kuma ka jefa mabudin cikin rijiya. Don haka babu ranar da za ka fita daga kabarin nan sai ranar hisabi.”

Daga nan sai ta kece da wata irin dariya mai firgitar da mutmin nan, ta ci gaba da dariyar har zuwa wani lokaci. Daga nan sai ta ce masa: “Barkanka da zuwa wannan gida, barkanta ya kai shagalalle!” Tana gama fadin haka sai ta yi wata irin girgiza, sai ga ta ta koma kasa, ta bace. Kyandirorin nan da suka haska dakin sai duk suka mutu, duhu ya bayyana, dakin ya koma wani wuri kuntatacce kamar siffar kabari.

Wannan shi ne karshen labarin nan kuma ga kadan daga darussan da ya kamata mu koya daga gare shi. Darasi na farko da ya kamata mu koya daga labarin shi ne, ya kamata mu gane cewa duniya dai ba matabbata ba ce; duk abin da muke ciki, wata rana sai mun bar ta, mun koma makwacinmu. Kamar dai yadda mutumin nan ya bi duniya har zuwa kabarinsa ba tare da ya sani ba. Haka kuma ya dace mu gane cewa, ita duniya wata abu ce mai kyalkyali da jan hankalin mutane, don haka idan muka biye mata, za ta kai mu ga halaka ne maimakon sa’ida. Mu duba dai yadda mutumin nan ya takarkare yana bin duniya, wacce ta kasance cikin siffar mace mai kyau, ya banzatar da Sallah, ya banzatar da sana’arsa mai kyau, ya bata lokacinsa yana bin ta, ga shi bai tsinana komai nagari ba. Na farko dai bai samu duniyar da yake nema ba, har daga karshe ya fada kabari, yana ji yana gani. Ke nan ya yi hasara biyu, ba shi ga duniyar kuma bai samu makwanci mai kyau ba a kushewarsa.

Ya dace duk abin da za mu yi a duniyar nan, mu yi shi cikin taka-tsan-tsan da lura. Mu kauce wa kyalkyalin duniya, mu tsaya kan gaskiya da amfani da lokacinmu domin gudanar da abin da ya dace; domin kuwa bayan zaman duniya, akwai wani wurin zaman na daban – kabari!

Allah Ya sanya mu dace da kyakkyawar rayuwa a nan duniya, kuma idan lokacinmu ya yi, Allah Ya sanya mu cika da imani; ba kamar yadda wannan mutumin ya yi batan-baka-tantan ba, amin.