Mu koyi “Programming” a Hausance, a sawwaqe (2)

Don Me Za A Gina Manhaja Kuma?Wani na iya tambayar cewa, “Ba ance kwamfuta ta iya lissafi ba, kuma tana iya yin komai? Me yasa kuma sai an sake rubuta wasu umarni an bata?” Amsar wannan tambaya ba nesa take ba. Dalilan da suka sa dole a bai wa kwamfuta umarni kuwa su ne kamar […]

Mu koyi “Programming” a Hausance, a sawwaqe (2)
Mu koyi “Programming” a Hausance, a sawwaqe (2)

Don Me Za A Gina Manhaja Kuma?
Wani na iya tambayar cewa, “Ba ance kwamfuta ta iya lissafi ba, kuma tana iya yin komai? Me yasa kuma sai an sake rubuta wasu umarni an bata?” Amsar wannan tambaya ba nesa take ba. Dalilan da suka sa dole a bai wa kwamfuta umarni kuwa su ne kamar haka:
1. Kwamfuta ba ta jinTuranci: Eh, ba ta jin turanci. In za ka shekara kana mata turanci ba ta san me ka ke cewa ba. Duk wani yaren duniya ba ta jinshi, in dai xanadam ne ke amfani dashi. Tana da nata harshen da dashi kaxai take iya karva da sarrafa umarni. Don haka, dole a fuskance ta da nata harshen;
2. Ba ta iya maka komai: Tabbas, duk da cewa kwamfuta ta na da hazaqa, amma kuma doluwace na qarshe. Duk da cewa kwamfuta ta iya lissafi, amma daqiqiyace na qarshe. Me yasa? Ba za ta iya zana maka hoto ba, idan kace: “Zana mini hoto.” Ba za ta iya maka komai ba, dole ka bata umarni dalla-dalla, gwari-gwari;
3. Harshenta daban: Wannan haka yake. Umarnin da ake bai wa kwamfuta, wanda muke magana a kanshi, bawai umarni ne irin wanda mai amfani da ita ke ba ta ba, wajen kunna wa ko kashewa ko taskance bayanai ba. A’a, umarni ne dake ingiza ta wajen aiwatar da aiki ta hanyar zance da ita da harshenta, wanda ake kira: “Machine Language.” Wannan harshe na takuwa jerin lambobin “1” ne da “0.” Duka bin da ka rubuta na umarni ga kwamfuta, a wannan yanayin take ganinshi. In kuwa haka ne, ashe dole ne ka gaya mata haqiqanin abin da kake son ta maka; babu gwaranci, babu zaurance.
A fannin “Programming,” bayan an rubuta umarnin da ake son bai wa kwamfuta don aiwatarwa, wanda maginin umarnin ke iya fahimta, dole ne kuma ya juya bayanan daga harshen da yake fahimta (Human Readable Code), zuwa wanda kwamfutar ke iya fahimta (Machine Language). Ana yin haka ne ta amfani da wasu masarrafai na musamman (dangane da irin nau’in yaren da mai rubuta umarnin yayi amfani dashi a farko).
Akwai masarrafar “Compiler,” da “Assembler,” da kuma “Interpreter.” Waxannan masarrafai na musamman, dasu ake amfani wajen juya bayanan umarnin da ake son bai wa kwamfuta, daga wanda xan adam ke iya karantawa da fahimta, zuwa wanda kwamfutar ce kaxai ke iya fahimta da sarrafawa. Bayani kansu na nan tafe, xaya-bayan-xaya.