Mu leka Alkur’ani: Darussa daga kissar Karuna

Duk wani jin dadin duniya Karuna ya kai maleji.

Mu leka Alkur’ani: Darussa daga kissar Karuna

Alkur’ani

Godiya ta tabbata ga Allah Wanda Yake cewa: “Lallai ne hakika, abin kula ya kasance a cikin kissoshinsu ga masu hankali.

Bai kasance wani kirkiran labari ba, kuma amma shi (Alkur’ani) gaskatawa ne ga abin da yake a gaba gare shi da rarrabewar dukkan abubuwa da shiriya da rahama ga mutane wadanda suka yi imani.” (Yusuf: 111).

Tsira da Amincin Allah su tabbata ga mafi tsarkin halitta Annabi Muhammad wanda yake cewa “Mafi alherinku wanda ya koyi Alkur’ani kuma ya koyar da shi,” da iyalansa da sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa.

Bayan haka a makon jiya muka fara leka cikin Alkur’ani Mai girma, inda muka nazarci wasu ayoyi game da yadda za mu fuskanci rayuwar duniya, wadda Allah Ya yi alkawarin za ta kasance jarrabawa da fitina ga bayinSa.

A yau ma za mu sake leka Alkur’ani Mai girma ne domin duba kissar attajirin duniyar nan da ya yi zamani da Annabi Musa (AS) wato Karuna.

Manufar Alkur’ani ta kawo kissoshin mutanen kirki da tababbu da batattu, ita ce a tarbiyyantar da Musulmi su yi koyi da mutanen kirki, a nuna masu wadancan mutanen kirkin nan fa su ma sun sha wahala a duniya, kafin a karshe su samu nasara a kan wadanda suka karyata su.

Sannan hakan ne zai gadar wa mutanen kirki samun kyakkyawar makoma a Lahira.

Su kuma mujirimai an kawo kissarsu ce don a gargadi Musulmi su guje wa irin ayyukansu saboda kada su hadu da miyagun abubuwan da wadancan suka hadu da su na halaka, tun a nan duniya kafin su koma ga Mahalicci a gobe Kiyama.

Duka kissoshin ana ba mu su ne domin mu gyara tamu tafiyar zuwa ga makoma ta karshe tare da gargadi gare mu cewa, kada mu aikata abin da zai jawo mana bala’i da hallaka a nan duniya.

Allah Madaukaki Ya ce: “Wancan yana daga labaran alkaryoyi. Muna ba ka labarinsu, daga gare su akwai wanda ke tsaye da kuma girbabbe.

“Kuma ba Mu zalunce su ba, amma su sun zalunci kansu, sa’an nan abubuwan bautawarsu wadanda suke kiran su baicin Allah, ba su wadatar musu komai ba a lokacin da umarnin Ubangijinka ya je, kuma (gumakan) ba su kara musu wani abu ba face hasara.

“Kuma kamar haka ne kamun Ubangijinka, idan Ya kama alkaryoyi alhali kuwa suna masu zalunci. Lallai kamunSa mai radadi ne mai tsanani.

“Lallai ne a cikin wancan akwai aya ga wanda ya ji tsoron azabar Lahira. Wancan yini ne wanda ake tara mutane a cikinsa, kuma wancan yini ne abin halarta.” (Hud: 100-103).

Kudi da ilimi da tasirinsu a rayuwar dan Adam

Hakika idan muka nazarci kissar Karuna za mu ga yadda ilimi da kudi suke iya sauya tunanin dan Adam ya mance Ubangijinsa, ya rika ganin wayo da dabara da iliminsa ne suka sa ya kai matsayin da ya kai.

Amma kafin mu yi nisa bari mu jero ayoyin da suka zo game da wannan babban attajiri na duniya wato Karuna.

Allah Madaukaki Ya ce: “Lallai Karuna ya kasance daga mutanen Musa, sai ya fita daga tsarinsu alhali Mun ba shi taskokin abin da yake mabudansa suna nauyi ga jama’a ma’abota karfi, a lokacin da mutanensa suka ce masa, “Kada ka yi alfahari, lallai ne Allah ba Ya son masu alfahari.

“Kuma ka nemi gidan Lahira a cikin abin da Allah Ya ba ka kuma kada ka manta da rabonka daga duniya.

“Kuma ka kyautata kamar yadda Allah Ya kyautata zuwa gare ka, kuma kada ka nemi barna a cikin kasa, lallai ne Allah ba Ya son masu barna.

Ya ce, “An ba ni shi ne a kan wani ilimi wanda yake gare ni kawai.”

Shin kuma bai sani ba cewa lallai Allah hakika Ya halakar a gabaninsa daga karnoni wanda yake shi ne mafi tsananin karfi daga gare shi, kuma mafi yawan tarawar dukiya, kuma ba za a tambayi masu laifi daga zunubansu ba?

“Sai (Karuna) ya fita a kan mutanensa a cikin adonsa. Wadanda suke nufin rayuwar duniya suka ce, “Ina dai muna da kwantancin abin da aka bai wa Karuna! Lallai shi, hakika, ma’abocin rabo babba ne.

“Kuma wadanda aka bai wa ilimi suka ce, “Kaiconku! Sakamakon Allah ne mafi alheri ga wanda ya yi tunani, kuma ya aikata aikin kwarai, kuma babu wanda ake hadawa da ita face mai hakuri.

“Sai muka shafe kasa da shi da kuma gidansa. To wadansu jama’a ba su kasance gare shi ba wadanda suke taimakonsa baicin Allah, kuma shi bai kasance daga masu taimakon kansu ba.

“Kuma wadanda suka yi burin matsayinsa a jiya sai suka wayi gari suna cewa, “Wai! Allah Yana shimfida arziki ga wanda Yake so daga bayinSa, kuma Yana kuntatawa.

“Ba domin Allah Ya yi mana falala ba, da Ya shafe kasa da mu. Wai! Lallai ne su kafirai ba su cin nasara.”

“ Wancan gidan Lahira Muna sanya shi ga wadanda suke ba su nufin daukaka a cikin rayuwar duniya, kuma ba su son barna. Kuma akiba ga masu takawa take.

“Wanda ya zo da abu mai kyau, to yana da mafi alheri daga gare shi, kuma wanda ya zo da mugun abu, to ba za a saka wa wadanda suka aikata miyagun ayyuka ba face da abin da suka kasance suna aikatawa.” (Kasas:76-84).

Karuna ya kasance daga cikin Bani Isra’ila an ce shi dan Baffan Annabi Musa (AS) ne. Allah Ya azurta shi da wadatar dukiya da yawan kudin da taskarsa ta cika akwatunan adana kudin suka yawaita ta yadda mabudan taskokin dukiyarsa ma sukan yi wahalar dauka ga mutane masu yawa da karfi.

Saboda wannan wadata sai ya zamo yana rayuwa a tsakanin mutanensa rayuwa ta nishadi da alfahari.

Yana sanya tufafin na alfahari cike da kawa ba ya fita daga gida face ya cancada ado.

Sannan ya gina gidaje na alfahari tamkar fadojin sarakuna. Yana da masu hidima da barori da bayi da ya zaba wa kansa. Duk wani jin dadin duniya Karuna ya kai maleji.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos