Mu muka harbo jirgin sojin Najeriya —Dogo Giɗe
Rundunar sojin sama ta bayyana musabbabin faɗuwar jirgin yaƙinta
’Yan ta’adda ƙarƙashin jagorancin Dogo Giɗe sun ɗauki alhakin harbo jirgin yaƙin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya da ya faɗo a Jihar Neja.
A ranar Litinin rundunar ta tabbatar cewa helikwaftanta da yake aikin kwashe mutanen da ’yan bindiga suka addaba, ya yi hatsari, kuma ta fara bincike domin gano abin da ya faru.
- Ba mu da shirin sake kara farashin man fetur a yanzu – Tinubu
- Cin kayan marmarin da aka nika da sinadari na iya haifar da cutar Kansa – NAFDAC
Jim kaɗan bayan nan ne ’yan ta’adda suka fitar da wani bidiyo wanda a ciki suke iƙirarin harbo jirgin sojin a yankin Badna, Gundumar Chukuba da ke Ƙaramar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja.
Sashenmu na tantance sahihancin labarai ya gudanar da binciken ƙwaƙwaf don tantance sahihancin bidiyon, inda muka gano cewa ba bidiyon bogi ba ne; Don haka bisa dukkan alamu sahihi ne.
Sai dai duk da haka ba za mu iya tattabar da gaskiyar iƙirarin ’yan bindigar na harbo jirin sojin ta hanyar amfani da bindiga kirar AK-47 ba.
Dogo Giɗe na daga cikin jagororin ’yan bindigar da shi da yaransa suka addabi mazaun yankunan Jihar Neja, suna kashe manoma da jami’an tsaro.
Ko a ranar Litinin mun kawo muku rahoton yadda ’yan ta’adda suka kashe kimanin sojoji 20 a kan hanyar Zungeru zuwa Tegina da ke jihar a ranar Lahadi.
Majiyoyi sun tabbatar mana a ranar Litinin cewa ’yan bindiga 53 sun sheka lahira a yayin musayar wutar da suka yi da sojojin.
– Dalilin faduwar jirgin sojin Najeriya
Babban Hafsan Sojin Najeriya Iya Mashal Hassan Abubakar, ya yi karin haske kan hatsarin jirgin sojin da yanayin ruwan sama da hazo a sararin samaniya.
A jawabinsa a hedikwatar rundunar da ke Abuja lokacin da Gwamnan Jihar Neja Umar Bago ya kai musu ziyar ta’aziyya, ya ce, “Ba za mu yi kasa a gwiwa ba, za mu ci gaba da kokarin hana aukuwar irin haka a wuraren da muke aiki.
“Duk da cewa ba zai yiwa a kawar da hatsari baki daya ba, amma za mu yi iya kokari domin dakile su, takaita aukuwarsu da asarar.”
Ya kara da cewa matukar jirage za su tashi domin yaki da ta’addanci, dole wata rana za a iya samun akasi, don haka babban abin yi shi ne takaita aukwar hakan, wanda kuma rundunar ta riga ta dauki ingantattun matakai.
Shugaban rundunar ya kum ba da tabbacin cewa za su ci gaba da aiki domin ganin ’yan ta’adda da sauran miyagu ba su samu wurin zama a cikin Najeriya ba.
– Kar ku gaji —Gwamnan Neja
A jawabinsa, Gwamna Bago ya roki rundunar da kada ta gajiya wajen yaki da ta’addanci, sannan ya roki shugaban rundunar da ya girke jiragen yaki a filin jirgi da ke Minna domin samun sauki da saurin daukar mataki a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
Gwamnan ya kuma runduanr alkawarin masauki ga dakarunsu a filin jirgin, sannan ya jajanta wa Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya bisa rasuwar dakarunta a harin da aka kai musu a jiharsa.
Daga Sagir Kano Saleh, Idowu Isamotu (Abuja) & Abubakar Akote (Minna).