Mu nazarci darasin da ke cikin labarin nan
Ya ku ma’abuta bibiyar Sinadarin Rayuwa, assalamu alaikum. Kamar yadda muka saba, a wannan makon ma muna dauke da sabon maudu’i, wanda idan muka nazarce shi, zai zizara mana wani sinadari na gyara rayuwarmu, sannan kuma mu kaurace wa wasu ’yan kura-kurai da muke yi a rayuwarmu ta yau da kullum. Irin wadannan kura-kurai da […]
Ya ku ma’abuta bibiyar Sinadarin Rayuwa, assalamu alaikum.
Kamar yadda muka saba, a wannan makon ma muna dauke da sabon maudu’i, wanda idan muka nazarce shi, zai zizara mana wani sinadari na gyara rayuwarmu, sannan kuma mu kaurace wa wasu ’yan kura-kurai da muke yi a rayuwarmu ta yau da kullum. Irin wadannan kura-kurai da muke aikatawa, sukan jaza mana nadama a rayuwa. Kasancewar mu ba ma’asumai ba ne, ba za mu iya hana aukuwar kura-kurai gaba daya ba a rayuwarmu; amma duk da haka, za mu iya kauce wa wadanda za mu iya, musamman ta hanyar kula.
Wani labari ne nan dan gajere zan kawo muku. Na zakulo shi ne daga cikin taskokin masu bibyar al’amuran rayuwar al’umma ta yau da kullum. Kamar yadda aka shaida mani, labarin nan ya faru a zahiri, duk da cewa ba sai mun ambaci suna ko wurin da al’amarin ya faru ba. Babban abin lura shi ne, mun fi ba labarin muhimmanci. Ke nan, ba mu damu da wurin da abin ya faru, ko sunayen wadanda abin ya shafa ba. Babban abin yi shi ne, mu kula da wata karin maganar Hausawa, wacce ke cewa; ‘idan ka ga gemun dan uwanka ya kama wuta, sai ka shafa wa naka ruwa.’ Ko kuma kamar yadda suka ce, ‘gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah.
Ga yadda labarin ya kasance:
Wani magidanci ne mai mata daya da dansa guda daya. Yaron ya kasance dan kimanin shekara hudu da haihuwa. Yaro ne mai wayau da hazaka a makarantar da aka sanya shi ta renon yara. Wata rana sai babansa ya samu kudi, ya canza mota. Ya sawo sabuwar mota wacce ake yayi, kuma ya rika kula da ita kamar wutar hunturu.
Duk safiya, magidancin nan yakan goge motarsa, sannan ya dauki dan nan nasa ya kai shi makaranta, shi kuma ya wuce wajen aiki daga can. Rannan ya fito da safe yana goge motar da tsumma, sai ga yaron ya fito, yana rataye da jikkarsa ta makaranta. Ya zo kusa da baban nasa yana jingina da motar.
A kan haka, da yake hannun yaro kamar hannun biri ne, sai kawai ya dauki wata ’yar kusa, ya koma can gefe daya na motar yana kartawa. Ashe wanii rubutu yake yi a jikin fentin motar da wannan kusa da ke hannunsa. Da farko mahaifin nasa bai ankara da abin da ke faruwa ba, sai daga baya ya gani.
Me zai faru? Mutumin nan sai kaunar motar nan ta makantar da shi, ya harzuka matuka. Ya mance da kaunar da yake wa yaron nan, ya mance da cewa dukiya mai karewa ce. Bai san lokacin da ya dauki wata wayar kebur ba, ya bazama da gudu zuwa wajen inda yaron nan yake. Ya yi ta shauda wa yaron nan kebur din a hannuwansa. Jini kuwa ya kece daga yatsunsa, dukkan yatsun suka samu mugun rauni.
Ganin haka fa aka dauki yaron nan zuwa asibiti, aka kwantar da shi. Bayan wani lokaci likita ya tabbatar da cewa ya zama dole ya guntsure yatsun yaron, idan ba haka ba kuwa ciwon daji zai lahanta dukkan su. Haka fa aka yi, yaro ya koma mai dungulmi.
Mahaifin yaro dai takaicin duniya ya ishe shi, ya rasa sukuni, saboda wannan aika-aika da ya aikata. Inda abin ya kara dugunzuma shi ma shi ne, sai da ya je asibiti rannan domin ganin halin da dan nasa yake ciki. Yaron na ganin babansa, bayan sun gaisa sai ya ce masa. “Baba, ka ga hannuna yadda ya koma, yaushe ne yatsuna za su dawo kamar yadda suke a da?”
Jin wannan bayani na dansa, sai hawayen takaici ya kwararo masa. Nan take ya tashi ya fita daga dakin jinyar, ya nufi ga motarsa da ya aje a waje. Yana isa wurin motar sai ya nufi daidai wurin da dan nasa ya karta masa, domin kuwa duk tsawon lokacin nan bai ma taba duba barnar da yaron ya yi masa ba. Da ya duba sai ya ga ashe yaron ba kartawa ya yi ba, rubutu ne ya yi mai ma’ana a jikin fentin motar. Ga abin da ya rubuta da Turanci: “Ina kaunar ka babana!”
Ganin wannan kyakkyawan lafazi da yaron nan ya rubuta, ya sanya babansa ya kara rikicewa. Allah Sarki! Ashe ma ba barna ya yi ba, gyara ne ya yi, amma ga shi saboda saurin fushi, ya haddasa wa dansa nakasa!! Mahaifin yaron ya shiga wani mawuyacin hali, hankalinsa ya gushe. Nan take ya bazama gida da gudu, ya hadiyi guba ya mutu. Takaici goma da gomiya!
Ko mun gane darasin da ke cikin wannan labari? Babban darasin da ya kunsa dai shi ne, mu rage ba dukiya daraja. Maimakon haka, mu rika daraja mutane. Da a ce maigidan nan bai shaku da son abin duniya ba, ba zai yanke wa wannan da nasa irin wannan mummunan hukunci ba.
Wani darasin kuma shi ne, mu daina zartar da hukunci a cikin gaugawa ko kuma a lokacin da muke cikin fushi. Da a ce lokacin da yaron nan yake rubutu, mahaifinsa bai harzuka ba, da a ce ya kwantar da hankalinsa ya bincika, kila da bai yanke masa wannan hukunci ba. Don haka, mu tabbatar da cewa mun gudanar da bincike kafin zartar da kowane irin hukunci.
Har kullum mu rika mutunta da daraja dan Adam, maimakon daraja dukiya. Mu kula da abin da muke tunanawa a zuciya, wannan zai sanya mu rika furta kalamai na kirki. Kalaman kirki kuwa su ke haifar da ayyukan kirki, a lokacin da ayyukan kirki kuma ke haifar da dabi’ar kirki. Ita kuwa dabi’ar kirki, ita ke haifar da nagartaccen mutum.
Allah Ya sanya mu dace, amin. Sai kuma mako na gaba idan Allah Ya kai mu, amin.