Mu nazarci labarun nan biyu
Mun samu gudunmowar labarun nan daga zakakurin marubuci kuma masani, Malam Nasir G. Ahmad (08065496902):Wata mata ce, tana kwance cikin dare sai ta yi wani mafarki, danta mai shekara 17 ta gani yana kyasta ashana yana kara wutar a idanunsa, har idanun suka yi jajur!Ta farka a firgice, ta tashi ta nufi dakin danta, ta […]
Mun samu gudunmowar labarun nan daga zakakurin marubuci kuma masani, Malam Nasir G. Ahmad (08065496902):
Wata mata ce, tana kwance cikin dare sai ta yi wani mafarki, danta mai shekara 17 ta gani yana kyasta ashana yana kara wutar a idanunsa, har idanun suka yi jajur!
Ta farka a firgice, ta tashi ta nufi dakin danta, ta tsaya daga bakin taga. Nan ta ga abin da ya yi matukar firgita ta. Wato ganin sa ta yi zaune yana kallon fim na batsa a cikin kwamfutarsa! Ta ji kamar ta daka masa tsawa, ta shiga ta karbe kwamfutar, amma sai ta kanne.
Ta juya ta koma dakinta. Ta rasa abin da ke mata dadi. Ta yi tunanin ta je ta taso babansa don ya gani da idonsa, ya san irin matakin da zai dauka. Shi ma ta fasa. Sai ta roki Allah Ya yi mata ilhamar wata hanya mafi kyau don ceto rayuwar wannan yaro nata. Haka ta kwana cikin sake-saken zuci har gari ya waye.
Da safe yaron ya fito zai tafi makaranta, ya biya dakinta don yi mata sallama. Sai ta yi amfani da wannan dama ta ce da shi:
Uwa: Me ya kamaci wanda ke jin matsananciyar yunwa ya yi?
da: Sai ya je ya sawo abinci, ya koma gida ya ci.
Uwa: Idan ba shi da kudin sayen fa?
da: Sai ya yi hakuri har Allah Ya kawo masa mafita.
Uwa: Idan kuma ya tsokano sha’awar abincin da loma guda fa?
da: Tabbas ya yi wauta.
Uwa: To ai kai ka yi wautar da ta fi tasa!
da: Ni kuma?! Yaushe? Ta yaya?
Uwa: Da kake tsokano sha’awarka ga mata ta hanyar kallon fina-finan batsa. Kai har gara wancan ma, domin shi da halal ya tsokano tasa sha’awar. Kai kuwa da haram kake tsokano taka! Ka yi watsi da fadin Ubangiji da ya ce, “Ka ce da muminai maza su runtse idanunsu (daga ganin matan da ba su halatta ba), su kuma tsare al’aurarsu (kada su yi zina).”
da: (Ya sunkuyar da kansa kasa, duk kunya ta rufe shi) Lallai na yi wauta amma da yardar Allah ba zan sake ba.
Abin Lura: Da cewa iyaye na bi da ’ya’yansu ta irin wannan salon a hikima, lallai da an sami raguwar kangararrun ’ya’ya.
***
Ga labara na biyu:
An yi wani attajiri a wani birni, wanda ke da wani matsakaicin gidan gona a bayan gidansa, inda ake yi masa kiwon kaji. Yana da matarsa da ’ya’yansa hudu: Biyu maza, biyu mata. Shi ne ya ba da labarin cewa:
“Wani bakauye ya taba zuwa na sauke shi a gidana. Sai na sa aka kamo wata dakwalwar kaza aka yanka. Na umarci matata da ta soye ta don samun abin karin kumallo.
“Da gari ya waye sai muka zauna cin abinci baki dayanmu; ni da matata da ’ya’yana da bakauyen da ya bakunce mu. Sai muka tura kazar gabansa muka ce ya raba mana ita. Nufinmu shi ne mu sami abin dariya daga wautarsa.
Bakauye ya ce: “Ni ban iya rabo ba, domin daidai sai Allah. In kuwa za ku amince da irin rabona, to sai na raba.” Bakauyen ya ce da mu haka.”
Muka ce masa za mu amince. Ya dauki soyayyar kazar, ya cizgo kanta ya miko min ya ce, ‘Maigida kan gida, ga rabonka.’ Ya ciro fuka-fukan kazar biyu ya mika wa ’ya’yana mazan su biyu ya ce, ‘Fuka-fukai na ’yan samari ne.’ Sannan ya ciro kafafun kazar biyu ya mika wa ’ya’yana biyu matan, ya ce, ‘kafafu ko na ’yan mata ne.’ Sai kuma ya cizgo zumbutun kazar ya mika wa matata ya ce, ‘Zumbutu sai uwargida. Amshi naki.’ Sannan ya ce, ‘ragowa kuwa na bako ne.’ Ya dauke kazar ya cinye muna kallo, sai muzurai yake yi.
“Kashegari sai na sa aka kamo kaji biyar aka yanka. Na ce da uwargidana ta gyara su ta soye. Da muka zauna don karyawa sai na ce da bakon nan ya raba mana kajin.
Ya ce: “Hala kun rike ni da abin da ya faru jiya ne?”
Muka ce masa a’a, ba mu rike shi da komai ba. Tun da dai shi ya raba jiya, to yau ma shi ya kamata ya raba.
“To wane irin rabon kuke so? Na cika ko na mara?” Gogan ya tambaye mu. Muka ce na mara.
Sai ya ce: “To kai da matarka da kaza guda uku ke nan.” Ya turo mana kaza guda. Ya ce: “‘Yan samari biyu da kaza guda uku ke nan.” Ya jefa musu kaza guda. Ya kuma ce: “‘Yan mata biyu da kaza guda uku ke nan.” Ya tura musu kaza guda. Sannan ya ce: “Ni kuma in an gama da kaza biyu uku ke nan.” Ya janye kaji biyu gabansa, ya gyara zama zai kwashi garar baki. Muka zura masa na mujiya kawai muna kallon ikon Allah.
Da ya farga da irin kallon da muke yi masa sai ya ce: “Me kuke jira? Ko ba ku son rabon marar ne? Ai ba zai yiwu ba ne sai hakan. To ko na cika kuka fi so?”
Baki daya muka ce ‘E!’ Sai ya hade kajin wuri guda sannan ya ce: “Kai da ‘ya’yanka maza su biyu da kaza guda hudu ke nan.” Ya turo mana kaza guda. Ya ce: “Ke kuma uwargida, ke da ’ya’yanki biyu da kaza guda hudu ke nan.” Ya tura musu kaza guda. Sannan ya ce: “Ni da kaji uku hudu ke nan.” Ya ja kaji uku gabansa. Sa’annan ya daga hannayensa sama ya ce: “Godiya ta tabbata gare ka Ya Allah, bisa fahimtar da ni wannan rabo da Ka yi!”