Mu nazarci wasu sinadaran kyautata rayuwa (2)

Tare da muhimmiyar gaisuwa wacce ta fi cancanta a kullum, Assalamu alaikum. Idan mun tuna, a makon da ya gabata ne muka yi tsokaci kan wasu muhimman abubuwa guda hudu da muka ce suna gajiyar da jikin dan Adam, wadanda ke jaza masa hasara muddin ya lizimci biye musu. Wadannan abubuwa kuwa kamar yadda muka […]

Mu nazarci wasu sinadaran kyautata rayuwa (2)

Tare da muhimmiyar gaisuwa wacce ta fi cancanta a kullum, Assalamu alaikum. Idan mun tuna, a makon da ya gabata ne muka yi tsokaci kan wasu muhimman abubuwa guda hudu da muka ce suna gajiyar da jikin dan Adam, wadanda ke jaza masa hasara muddin ya lizimci biye musu. Wadannan abubuwa kuwa kamar yadda muka yi tambihinsu sun hada da yawan surutu, yawan barci, yawan cin abinci da kuma abu na hudu, watau yawan ganawa da mutane barkatai. 

To, a wannan makon ma wasu rukunnan ne guda hudu za mu nazarta, wadanda suke lalata jikin dan Adam, muddin dai mutum ya bari suka ci karfinsa. Wadannan abubuwa kuwa su ne, yawan damuwa, kamuwa da bakin ciki, yunwa da kuma karancin barci. Idan muka lura, sun kusa su zama kanne ko kishiyoyi da rukunnai hudu da muka nazarta a makon jiya, duk da cewa sun bambanta da juna. Idan mun shirya, bari mu dauke su daya bayan daya domin ganin yadda za su iya lalata mana jiki idan mun yi sakacin barinsu suka yi tarsiri a tare da mu.

Rukuni na farko da ke cikin lissafinmu shi ne damuwa. Wannan na nufin mutum ya sanya wa kansa damuwa bisa wani al’amari da ya kama masa zuciya, musamman saboda faruwar wani al’amari marar dadi ga rayuwa ko kuma saboda rashin samun wani abu mai muhimmanci ga rayuwa. Misali, mutum kan shiga damuwa saboda rashin kudi, ko rashin aikin yi ko kuma saboda wani abu mai muhimmanci da yake son samu amma ya kubuce masa.

Idan har mutum ya bari irin wannan damuwa ta auri zuciyarsa, ta wuce mizanin da ya kamata, lallai kam za ta zama cuta wacce za ta lalata ruhin jikin dan Adam. Don haka, duk irin hikima da dubarar da mutum zai yi domin ya guje wa damuwa, ya kamata ya yi domin ya rabu da ita. Idan ba haka ba kuwa, muddin damuwa ta ta’azzara ga dan Adam, to tana iya zama haddasau ga lalata jikin dan Adam. Daga damuwa, idan an bari ta ci gaba, sai ta rikide zuwa ga hauka, Allah kiyaye, amin. 

Domin magance annobar damuwa, ya kamata mu koyi yin hakuri da dukkan al’amuran rayuwa da suka same mu, musamman ma marasa dadi. Idan muka yi hakuri ne za mu koyi mantuwa da irin wadannan al’amura. Wannan zai sanya koda mun damu, abin ba zai ta’azzara ba, cikin kankanen lokaci sai mu mance da cewa ya ma faru. A kullum mu sanya wa zuciyarmu yarda da kaddara, domin duk abin da ya same mu dama tabbas zai faru, abin da muka rasa yanzu, muna iya samunsa a nan gaba.  

Rukuni na biyu kamar yadda muka lissafa su a sama shi ne bakin ciki. A nan ba muna nufin mutum ya yi wa wani bakin cikin samun wani abu ko wata ni’ima ba, muna nufin bakin ciki da ke gallabar dan Adam. Watau shi bakin ciki wata irin damuwa ce da ke kama zuciyar dan Adam, ta sanya masa wani ciwo mai radadi da zai yi ta gallabar da tunani da zuciyar mutum. Da zarar wani abu ya jaza wa dan Adam bakin ciki kuwa, to idan ba sauri ka yi ka kautar da shi ba, to da zarar ya zauna daram a zuciyarka, lallai kam yana cutarwa. Bisa haka zai zauna ya yi ta cin zuciya da kwakwalwar mutum, daga nan har ya addabi gangar jikin dan Adam. Wannan zai sanya ka ga mutum ya rame ko kuma wata cuta ta kama shi, wacce ke da dangantaka da zuciya ko kwakwalwa. Da zarar irin wannan ta faru kuwa, to shi ma yana iya haddasa hauka ko makamancin haka. Ke nan ya dace mu rika dangana da mai da al’amuranmu ga Allah. Kasancewar an halicci mutum da yanayin mantuwa, to idan muka bijiro wa kwakwalwarmu da mancewa da al’amarin da zai sanya mana bakin ciki, shi ke nan mun yi wa kanmu magani ke nan. Allah Ya kiyaye, amin.

Rukuni na uku, wanda kuma ka iya lalata mana jiki da ruhi ita ce yunwa. Idan mun tuna, a rukunnan da muka nazarta a makon jiya, har da rukunin yawan cin abinci; to yau kuma ga yunwa, wacce idan ta ta’azzara, za ta iya lalata jikin mutum cikin lokaci. 

Kamar yadda al’amarin jikin dan Adam yake, yana samun tallafi ne daga abinci da ruwan sha. Rashin wadannan a jikin mutum na nufin jikin ya rasa tallafin da zai rayar da shi ke nan. Idan haka ta faru, to jiki ya yi rashi ke nan, wanda haka zai sanya dukkan sinadaran jikin za su sukurkuce. Idan sinadaran jiki suka sukurkuce, suka rasa natsuwa da kwanciyar hankali, to babu lafiya ke nan. Don haka, mu kasance masu kula da cin abincin da ya kamata, kuma a lokacin da ya kamata daidai gwargwado, wanda haka zai yi mana maganin yunwa, wacce wasu ke wa kirari da: Ta bahuwa mai murfin karfe, ba a sha miki La haula, da rubutu gara kwadon rogo!

Rukuni na hudu kuma na karshe a wannan tsari shi ne karancin barci. A makon jiya, mun ce yawan barci na cutar da dan Adam, to kuma karancinsa ma na iya yin illa ga mutum. Abin da ya kamata mutum ya lizimci yi shi ne, ya kasa lokacinsa zuwa gida-gida, lokacin aiki daban, lokacin hutawa daban, lokacin barci daban. Amma ba hikima ba ce ga mutum ya ce zai yi ta aiki ba tare da samun lokacin barci isasshe ba. A lokacin barci ne jiki ke samun hutu, kwakwalwa ke samun hutu, yadda idan mutum ya tashi zai kasance cikin karsashi da lafiya. Rashin samun barci kuwa na nufin babu hutu ga rukunnan jikin dan Adam ke nan. Idan haka ta faru, sai al’amura su lalace masa ke nan.

Kamar yadda maudu’inmu na yau ke nunawa, ya kamata mu takaita damuwa, mu takaita bakin ciki, mu kaurace wa jikinmu daga yunwa, sannan kuma mu rika yin barci daidai gwargwado. Wannan shi ne tsarin da zai kara mana lafiya da zaman jikinmu lafiya. Rashin wadannan abubuwa kuwa na nufin cuta ga jiki. Allah Ya kara mana lafiya da zaman lafiya, amin.