Mu ne muka kai samame otal ba ’yan bindiga ba — EFCC
Kakakin ‘yan sandan jihar ya yi watsi da jita-jitar da ake yaɗawa cewar mahara ne suka sace mutane a otal ɗin.

Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), ta ce ita ce ta kai samame otal ɗin White Hill da ke kan titin Shiroro a Minna, Babban Birnin Jihar Neja.
A yayin farmakin, an kama aƙalla baƙi 10 da ake zargi da aikata damfara a Intanet, wanda aka tafi da su Kaduna.
Wani ma’aikacin otal ɗin da ya nemi a sakaya sunansa, ya musanta jita-jitar da ake yaɗawa cewar ’yan bindiga ne suka yi basaja a kayan EFCC, sula sace baƙi 10 a ranar 27 ga watan Fabrairu.
“Ba ’yan bindiga ba ne. Jami’an EFCC ne suka zo suka kama wasu ‘yan damfara suka tafi da su Kaduna,” in ji shi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya kuma yi watsi da wannan jita-jitar.
Ya shawarci ’yan jarida su tuntuɓi EFCC domin tabbatar da sahihancin lamarin.