Mu rika mutunta al’adunmu da addininmu a fim – Baba G
Shafi’u Muhd wanda aka fi sani da Baba G. daya ne daga cikin mawakan Hip-Pop a Jihar Kano. A hirarsa da Aminiya, ya bayyana dalilan da suka sa yake sa akalar jigon wakokinsa a kan rayuwa da sauran abubuwa. Ga yadda hirar ta kasance: Lubabatu I. Garba, a Kano Za mu so sanin takaitaccen tarihin […]
Shafi’u Muhd wanda aka fi sani da Baba G. daya ne daga cikin mawakan Hip-Pop a Jihar Kano. A hirarsa da Aminiya, ya bayyana dalilan da suka sa yake sa akalar jigon wakokinsa a kan rayuwa da sauran abubuwa. Ga yadda hirar ta kasance:
Lubabatu I. Garba, a Kano
Za mu so sanin takaitaccen tarihin rayuwarka
Sunana Shafi’u Muhamamd Shafi’u, sai dai an fi kira na da lakanin Baba G. kasancewar sunan kakana na ci sai a gidanmu ake kira na Baba. Su kuma abokaina suna kira na Gayu. Daga baya sai ake kira na Baban Gayu, har dai kuma ya zama Baba G.
An haife ni a Unguwar Madabo, a yankin karamar Hukumar Dala cikin Jihar Kano. Sai dai na tashi a Unguwar kofar Ruwa B. Na yi karatun firamare a Makarantar Firamaren Gobirawa. Bayan na kammla a 1997 sai na shiga sakandaren Army Day amma na kammala a sakandaren Kwakwaci a 2003. Daga nan sai na shiga Jami’ar Byaro na yi diploma a bangren aikin jarida.
Ban yi aikin gwamnati ba sai na shiga harkar kasuwanci. Ina harkar kasuwancina ina kuma yin waka, daga baya kuma sai na shiga yin fim din Hausa. Wani lokaci baya sai na dakatar da duk harkokina na koma makarantar Islamiyya don samun ilimin addini, inda na kwashe tsawon shekaru uku a Makarantar Usman Bin Affan.
Ya aka yi ka fara waka?
Tun ina karami nake da sha’awar waka. Sai dai na fara rubuta waka lokacin ina sakandare amma ban fara bugawa ba sai a 2003. Ba na mance dalilin da ya sa na rubuta wakata ta farko mai suna ‘Rayuwa,’ wata rana mun dawo daga makaranta ina jin yunwa sai na rika tunanin yadda yanayin rayuwa yake. Bayan na rubuta sai na jawo wani abokina mai suna Peter muka je wani studiyo muka rera wakar tare; inda ni nake yi da Hausa shi kuma yake yi da Turanci. Daga nan dai harkar waka ta bude har ta kai na yi albam mai suna ‘Zuma’ wanda na sa wata wakata a ciki mai suna ‘Nasiha A Kan Auren Zamani. Wananan waka ta zama fitacciya, domin gidajen rediyo suna yawan sanya ta a tasoshinsu don fadakarwa. Na yi wannan waka ne sakamakon hana ni auren wata yarinya da aka yi, inda iyayenta suka rika yawo da hankalina saboda suna ganin ba ni da abin da zan iya rike musu ’yarsu. Duba dai yadda sha’anin rayuwa yake tafiya kari da yadda mutane ke tafiyar da rayuwarsu a kullum ya sa za ki ga mafi yawan jigon wakokina yake dauke da sakonni a kan rayuwa, don jama’a su ji su fadaka ta yadda za su gyara al’muran rayuwarsu.
Ya aka yi ka kuma shiga harkar fim?
Ina gudanar da harkar wakata sai kuma wani abokina ya ja ni cikin fim, inda ya bayyana min cewa zan iya bayar da gudunmawa a wannan harka. Kafin na fara sai da na nemi amincewar iyayena suka sanya mini albarka tare da b a ni shawarwari a kai. Fim din da na fara yi shi ne ‘Saka’ wanda muka yi da Sani Danja da Adam Zango. Daga nan aka sake sanya ni a wani a matsayin jarumin wani fim mai suna ‘Tajdid’ inda muka yi wasa tare da su marigayiya Hauwa Ali Dodo da su Kabiru Nakwango da sauransu. Ina cikin harkar fim ne na dakata na koma makarantar Islamiyya, inda na kwashe kimanin shekaru uku kafin dawowata harkar fim.
Bayan dawowa ta a yanzu na yi fina-finai da dama, wadanda ke kan hanyar fitowa kamar su ‘Kada Ki Zarge Ni’ fim din Darakta Saifullahi Mai Imani da ‘Kina So Na?’ Akwai wani fim din Ali Rabi’u Ali mai suna ‘Zan Dawo’ da sauransu.
Wacce nasara da kalubale ka samu a wannan harka?
Babbar nasara a rayuwa ita ce ka yi wani abu don al’umma sannan kuma a samu abin nan ya samu karbuwa. Alhamdu lillahi a wannan bangare, domin wakata ta rayuwa ta samu karbuwa, kasancewar kafafen watsa labarai na amfani da ita sosai.
kalubale kuwa wannan dole ne, babban kalubalen da muke fuskanta shi ne yadda jama’a ke yi mana kallon wasu mutane marasa aikin yi.
Wane albishir kake da shi ga masu sauraron wakokinka?
Sai in ce musu su saurari fitowar sabon albam dina mai suna ‘Mata Da Mota.’ Na yi wannan waka ce ganin yadda ake rudar mata da mota a wannan zamani. Sai ka ga mutum yana neman mace, da zarar mai mota ya zo sai ya tafi da hankalinta. Su mata in dai ba ka da mota to sunanka sorry, idan kuwa kana da mota ko da kuwa ba ka da kudin sayen mai.
Wace shawara kake da ita ga abokan sana’arka?
Shawarata ga bangaren mawaka ita ce, akwai bukatar mu rika taka-tsan-tsan da harshenmu a wajen waka, domin harshe na iya jawo wa mutum matsala. Ya zama duk lafuzzan da mutum zai yi amfani da su a wakarsa, ya tabbatar masu amfani ne, wadanda za su fadakar da mutane yadda za su bar wasu munanan ayyuka da suaransu. Wannan kuwa ya shafi kowane fanni da mawaki zai yi wakarsa a kai.
Ga masu sana’ar fim, akwai bukatar su rika fitar da fina-nai masu amfani ga jama’a, wadanda za su fadakar. Sannan kuma mu kiyaye addininmu da al’adunmu a cikin fina-finanmu. Haka kuma akwai batun sanya sutura, ya kamata mu rika mutunta kawunanmu ta hanyar sanya suturar da addininmu ya yarda da ita.
Sannan ina kiran abokan sana’ata da mu hada kai don ciyar da harkar gaba.
Wane kira kake da shi ga sauran jama’a?
Ina kira ga irin mutanen da suke kallon mu a matsayin mutane marasa aikin yi. Kamata ya yi a rika kallon mu da kyakyyawan zato, a matsayin mutane masu gudanar da halastacciyar sana’a. Kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya yi umarni cewa a duk lokacin da ka ga mutum, to ka fara yi masa kyakkyawan zato, kada ka aibata shi. Haka kuma idan an ga wani kuskure a sha’anin aikinmu, kamata ya yi a kira mu a nuna mana kuskurenmu, ba a rika zaginmu ba. Kowa ya san dan Adam ajizi ne.
Wane kira kake da shi ga gwamnati?
Ina son yin amfani da wannan dama na yi kira ga gwamnatinmu da ta rika tallafa mana kamar yadda sauran kasashen duniya ke yi ga takwarorinmu, wanda hakan ya jawo suka ci gaba a harkokinsu. Idan kika dauki misalin Indiya, gwamnatinsu na tallafa musu kwarai da gaske. A lokacin da abokan sana’armu na fim suka je Indiya a kwanan nan, su kansu Indiyawa suna mamakin yadda aka yi masana’antar fim dinmu ta Hausa take bunkasa ba tare da sa hannun gwamnati ba. A nan ne suka rika yaba kokarinmu, ganin yadda cikin ’yan shekaru kalilan muka fitar da fina-finai masu dimbin yawa. Muna kira ga gwamanti da ta duba mu, duk bangarorin biyu wato na waka da na fim; ta rika ba mu tallafi don ci gaban harkar. Babu shakak ci gaban wannan harka ci gaban kasa ne, domin Allah ne kadai Ya san mutanen da suke cin abinci a wanann harka. Kin ga ko ta wannan bangaren an samar da aikin yi ga dimbin matasan kasar nan, wanda hakan babban ci gaba ne ga gwamnati. A gefe daya ma muna kira ga masu kudinmu da su rika sa jarinsu a cikin wannan harka.