Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu
Huduba ta daya:Dukkan godiya da yabo sun tabbata ga Allah, Wanda muke neman taimakonSa, kuma muke neman gafararSa, kuma muke neman shiriyarSa. Kuma muna neman tsarin Allah daga sharrance-sharrancen kawunanmu da na miyagun ayukkanmu. Wanda duk Allah Ya shiryar, babu mai batar da shi; Wanda kuma Ya batar, babu mai shiryar da shi. Na shaida […]
Huduba ta daya:
Dukkan godiya da yabo sun tabbata ga Allah, Wanda muke neman taimakonSa, kuma muke neman gafararSa, kuma muke neman shiriyarSa. Kuma muna neman tsarin Allah daga sharrance-sharrancen kawunanmu da na miyagun ayukkanmu. Wanda duk Allah Ya shiryar, babu mai batar da shi; Wanda kuma Ya batar, babu mai shiryar da shi. Na shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai Yake, ba Ya da abokin tarayya a gare shi; kuma na shaida cewa lallai Annabi Muhammadu (Sallahu Alaihi Wasallam), bawanSa ne kuma ManzonSa ne, (Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi da jama’ar gidansa da sahabbansa baki daya).
Bayan haka, ya ku bayin Allah! Babu shakka, shirya al’amurra da gudanar da su a hannun Allah yake! Shi Allah Yana aikata abin da Yake son aikatawa a cikin bayinSa, kuma ba a isa a tambaye Shi dalili ba, amma mu bayinSa ana tambayarmu, kuma Allah Shi ne Mai cikakken sani!
Daga cikin sunnoninSa Madaukakin Sarki, akwai jarrabar mutane da abubuwa masu kyau ko marasa kyau domin su (gane Allah su) koma maSa. A dalilin jarrabawar ne ake gane mumini da munafuki, kamar yadda ake gane na kwarai da mugu. Allah Madaukakin Sarki Ya ce; “Ashe, mutane sun yi zaton a kyale su, su ce:”Mun yi imani” alhali kuwa ba a fitine su (jarrabe su) ba? Kuma hakika Mun fitini (jarrabi) wadanda ke a gabaninsu, domin lallai Allah Ya san wadanda suka yi gaskiya, kuma lallai Ya san makaryata (Wato Ya bambanta a tsakanin masu da’awar imanin gaskiya da makaryata).” (Ankabuti: 2-3.).
A kan wadannan ayoyi ne, Shahid Sayyid Kutub (Allah Ya yi masa rahama) ya ce: “Imani ba kalma ce da ake fadi da harshe ba kawai. A’a, hakikanin imani shi ne hakuri a kan abubuwan da rai bai so da kuma kallafe-kallafen shari’a game da kalmar imani, wadanda suka zagaye ta! (Fi Zilalil kur’an). Kuma hakika Allah Ya jarrabi ManzanninSa da AnnabawanSa (Amincin Allah Ya tabbata a gare su) da nau’o’in jarrabawa da bala’o’i iri-iri, alhali kuwa su ne mafiya soyuwar mutane a gare Shi, kuma su ne mafiya tsarkakarsu, kuma mafiya nagartarsu. To, duk wannan, kamar yadda mai littafin Asshifa ya bayyanar, an yi ne domin karin girma ga matsayinsu da daukakarsu da darajojinsu; kuma domin ya zamo sababin bayyanar da irin hakurinsu da yardarsu da al’amarin hukuncin Allah da godiyarsu gare Shi da mika wuyansu gare Shi da tawakkalinsu da dogaronsu gare Shi da yadda suke rokonSa da kuma kankan da kansu gare Shi Ta’ala da sauransu. Har ila yau domin wannan ya zama tunatarwa da wa’azi ga wadanda ba su ba – domin su yi koyi da su idan wasu bala’o’i sun same su. Kuma domin irin jarrabawar da aka yi wa Annabawan (AS) su sanyaya zukatan wadanda ba su ba, su ma su yi koyi da hakurin Annabawan (AS) idan ire-iren wadannan jarrabawa iri-iri da suka same su.”
Misali, ya ’yan uwa, ku dubi irin hakurin Annabi Ayyuba (Alaihis Salam) da Annabi Ibrahim (Alaihis Salam) da Annabi Yakub (Alaihis Salam) da Annabi Yusuf (Alaihis Salam) game da irin jarrabawa iri-iri da suka same su. Allahu Akbar!! Malam (Aliyu) Sabuni ya ambata a cikin sanannen littafin tafsirinsa wato Safwatut-Tafasir, cewa:
“An ruwaito cewa Annabi Ayyuba (Alaihis Salam) ya kai shekara 18 a cikin musibar da ta same shi, sai wata rana matarsa ta ce masa: “Da ma dai ka roki Allah Mai girma da daukaka (game da wannan matsalar).” Sai ya ce mata:” Shin shekara nawa muka yi a cikin yalwa (babu matsalar komai)? “Sai ta ce:”Shekara 80.” Sai ya ce mata: “To, ni ina jin kunyar Allah in roke Shi (fita cikin wannan lalurar) alhali shekarun da na yi a cikin ibtila’in ba su ko kai yawan shekarun da na yi a cikin yalwa (wadata ko rahama) ba.”
Ya jama’a! Hakika, akwai abin lura ga masu hankali game da labarin wadancan manyan bayin Allah! Ya Allah, Ka sanya mu masu yawan ambatonKa da gode maKa da kyautata ibadarKa. Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad (Sallahu Alaihi Wasallam) da jama’ar gidansa da sahabbansa baki daya.
Injiniya Isma’il M. Cindo Gotomo (MNSE, MNIAE) ya gabatar da wannan huduba ce a ranar Juma’ar da ta gabata, 7 ga watan Rajab 1437 Bayan Hijira daidai da 15 ga Afrilu, 2016 a Masallacin Juma’a na Haliru Abdu da ke Birnin Kebbi a Jihar Kebbi .