Mu rike Allah da manzonSa -Shehu Matawallen Masoya
Ko za ka bayyana mana tarihinka a takaice?Sunana Shehu A. Adamu, amma an fi kirana da lakanin Matawallen Masoya. An haife ni a ranar 5 ga Disamba, 1985, a kauyen Bakin Yuyu, a cikin Fulani. kauyen yana karkashin Dagacin ’Yangwan, a karamar Hukumar Gabasawa, Jihar Kano. Na yi karatuna na firamare da sakandare da kuma […]
Ko za ka bayyana mana tarihinka a takaice?
Sunana Shehu A. Adamu, amma an fi kirana da lakanin Matawallen Masoya. An haife ni a ranar 5 ga Disamba, 1985, a kauyen Bakin Yuyu, a cikin Fulani. kauyen yana karkashin Dagacin ’Yangwan, a karamar Hukumar Gabasawa, Jihar Kano. Na yi karatuna na firamare da sakandare da kuma makarantar allo, duk a wannan gari namu. Haka kuma na samu ilimi daidai gwargwadon iko.
Bayan n agama karatu kuma na yi harkar yawon neman kudi, inda na yi aikin gona. Na taka har kasar Kamaru domin aikin yankan shinkafa. A nan gida kuwa na zauna Jihar Taraba, inda duk na yi wannan aiki na noma.
An taba yi mini aure a shekarar 2007, amma muka rabu da matar, bayan shekara biyu. Wato mun rabu a shekarar 2009. Mun samu karuwar haihuwar diya mace, wato Ummi.
Ta yaya aka yi ka fara waka kuma me ya ja hankalinka har ka shiga sana’ar waka?
Batun da yaya aka yi na shigo sana’ar waka shi ne, wata rana na hau shafin Facebook dina sai na ga Maryam A. Baba a kan layi. Sai na gwada yi mata magana, na tura mata da wani tes kamar haka: “Allah Ya taimaki mawakiya ta Kanawa. Ina jin dadin yadda kike yin wakoki tare da Aminu ALA. Ni ma ina yin waka kuma ina da wakoki 5 amma ina so ki taya ni gabatar da su.”
Washegari na koma shafin nawa na Facebook, sai na gat a bar mani sakon lambar waya. Ni kuwa sai na kira layinta, daga nan muka yi magana mai muhimmanci. A’ahh, daga nan sai na fara tunanin kada kuma mu hadu ta tambaye ni ina waka, ni kuma ban iya waka ba; a zo a ji kunya. Sai na ce in Allah Ya yarda sai na yi waka. Domin na yi mata karyar cewa ina yin waka ne domin kawai in samu dammar yin magana da ita. Wannan karya da na yi mata kuwa, ita ce dalilin da ya sanya na matsa wa kaina cewa sai na rera waka, domin kada in ji kunya idan mun hadu da ita. To ka ji yadda aka yi na shiga sana’ar waka.
Wadanne irin wakoki kake rerawa, na soyayya, ko na siyasa, ko na addini ko na sarauta?
Maganar wadanne irin wakoki nake rerawa, to ni dai ban ga abin da ba zai waku ba a wurina. A kan komai zan iya yi masa waka. In Allah Ya so duk abin da na kawo a raina, zan iya wake shi. Koma mene ne, sai dai idan ba zan iya kama sunansa a bakina ba.
Akwai wakokin sarauta da na yi, musamman ma dai akwai wakokin mai martaba Sarkin Kano da na rera, wadanda suka hada da wakar ‘Aikin Hajji Sai dangata’ da kuma wakar ‘Mai Martaba Sadauki.’ In Allah Ya yarda zan sake su a wannan sabuwar shekara ta 2016.
Ya zuwa yanzu ka yi wakoki nawa, shin ko ka fitar da alabam kuwa?
Maganar wakokina nawa, akwai wakar ‘Babban Sarki Na Afirika’ wacce na yi wa marigayi San Kano, kuma kafin rasuwarsa na gana da shi, na sami takardar izinin yin waka daga daga gare shi. Wato marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, Allah Ya jikansa. Wakata ta biyu, na yi ta ne kan aure. Wakata ta uku ta siyasa ce, wacce na yi wa Alhaji Usman Alhaji, wato a kan takararsa ta neman kujerar Gwamnan Jihar Kano. Wakata ta hudu kuwa, na sanya mata suna ‘Gandun Aiki’ wacce na yi wa Gwamnan Kano mai ci yanzu, Alhaji Abdullahi Umar Ganduje. Ita kuma na yi ta a kan, nasarar zaben da aka samu a Kano, har ma da sama. Amma ita ma ba ta fita ba. Su kadai na buga kuma ban fitar da alabam ba sai dai niyya kawai nan gaba in sha Allahu.
Cikin wakokinka, wacce ta fi burge ka, wacce za a kira bakandamiyarka?
Bakandamiyata kuwa ita ce wakar ‘Babban Sarki Na Afirika’ domin kuwa da ita aka fara sani na a waka. Wakar tana dauke da minti 15 da sakan 9.
Ko za ka bayyana mana mawakan da kake tare da su a matsayin abokan sana’a kuma yaya dangantakarku take?
To, batun mawakan da nake tare da su, su ne Maryam A. Baba da Maryam Fantimoti da Usaini Danko da Kahutu Rarara da Ahmad M. Sadik da kuma Ali Isah Jita. Kuma akwai alaka mai karfi a tsakani na da su.
Me ka taba samu a sana’ar waka, wanda kake jin dadi da alfahari da shi?
Batun abin da na samu a waka, gaskiya in dai a matsayin kudi ko wani abu, na san dai marigayi mai martaba ya ba ni takardar izinin yin waka.
Mene ne burinka a rayuwar waka nan gaba?
Batu burina kuwa, to ka san dai shi buri a rayuwa ba ya karewa. Ina da bukatar in samu rufin asiri a rayuwata.
Ko akwai wani sako da kake son sanar da al’umma game da rayuwar sana’arka, wanda ban tambaye ka ba?
Batun sakona ga al’ummar Annabi shi ne, mu kara rike Allah da manzonSa a zukatanmu, mu rike ibada koda mun zamanto ba mu da shi, ma’ana koda Allah bai azurta mu da dukiya ba.
A gaya wa mawakan Dabo, ina mubaya’a ga kowane mawaki ko da bai zo duniya ba. Kuma ina son mu kara hada kanmu da kanmu. Mu zauna lafiya, babu shagube ko habaici a tsakainmu.
Sakona ga mawaka masu tasowa, kar ka ce daga ka buga waka, ka ce kudi za su zo a nan take. Kuma kada ka ga kana waka ka rika yin yaudara da sana’arka. Idan ka yi haka, ka ci mutuncin sana’a. Allah Ya kara ba mu zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasarmu da a jiharmu baki daya.