Mu Sha Dariya
Sauka lafiya Wani Babarbare ne ya shiga mota daga Maiduguri zuwa Bauchi. Da mota ta tashi za a tafi sai wani mutum ya ce a sauka lafiya. Sai Babarbare ya firgita, ya fito daga motar ya ce: “Ku ba ni kudina, ni ba Lafiya zan je ba.” (Ya yi zaton motar garin Lafiya za […]
Sauka lafiya
Wani Babarbare ne ya shiga mota daga Maiduguri zuwa Bauchi. Da mota ta tashi za a tafi sai wani mutum ya ce a sauka lafiya. Sai Babarbare ya firgita, ya fito daga motar ya ce: “Ku ba ni kudina, ni ba Lafiya zan je ba.” (Ya yi zaton motar garin Lafiya za ta, ta Jihar Nasarawa saboda ya ji an ce sauka lafiya).
Daga Sani Babawuro Jama’are, 08093435003
Dolaye biyu
Bahadeje ne da Banufe sun je yin itace a daji, kowa ya yo nasa itacen sosai ya dora a kai. Da suka dawo gari, har za su shiga gida ke nan sai Bahadeje ya ce ya manto addarsa a daji. Sai ya koma da itacen nasa a kai, ya je neman addar; shi kuma Banufe ya tsaya jiransa da itacen nasa a kai. Shi ne mutane ke ta gardamar wanda ya fi dolonci a tsakaninsu.
Daga Iliyas Idris Fahad Suleja
’Yan kasuwa
Wasu matasa, Ibo da Bahaushe da kuma Bayarabe, muhawara ta kaure tsakaninsu a kan wa ya fi kwarewa a fannin kasuwanci da kuma tsabar son kudi. Sai aka tambayi Bahaushen cewa 1+1 ya ce 2. Sai Bayarabe aka ce masa 2+2 ya ce 4. Sai aka ce wa Ibo 3+3 sai ya ce Naira 6!
Daga dantanin Yalwa, 08089766487
Yaro Jafar
Wata rana Jafar da mahaifiyarsa suna hira sai ta ce masa: “Jafar, idan ka gama makaranta wane aiki kake so ka yi?” Sai ya ce: “Ina so in zama malamin makaranta.” Sai mahaifiyar ta ce: “Ai malaman makaranta ba su samun kudi da yawa, ka canza wata sana’ar.” Sai ya ce: “To ina so in zama irin masu zama a mota suna cewa: ‘Samaru Samaru, ana ba su kudi” (yana nufin karen mota saboda yana ganin kudi da yawa a hannunsu). Sai mahaifiyar ta ce: “Jafar, Allah Ya raba ka da karen mota koma malantarka.”
Daga Sulaiman Mai Bazazzagiya