Mu Sha Dariya
Agwai da dan sanda Wani Agwai ne ya je kasuwa ya yi sata, ’yan sanda suka biyo shi da gudu sai ya samu jikin kalgo ya boye. Su kuma ’yan sandan suna kusa da shi amma ba su gan shi ba, sai daya yake gaya wa dan uwansa cewa: “Yanzu kila in muka kira […]
Agwai da dan sanda
Wani Agwai ne ya je kasuwa ya yi sata, ’yan sanda suka biyo shi da gudu sai ya samu jikin kalgo ya boye. Su kuma ’yan sandan suna kusa da shi amma ba su gan shi ba, sai daya yake gaya wa dan uwansa cewa: “Yanzu kila in muka kira shi zai amsa ko?” Agwai na jin su, sai suka ce: “Agwai!” Ya yi shiru. Suka sake cewa: “Agwai!” Ya yi shiru. Da suka sake cewa: “Agwai!” Sai ya ce: “Kaaii, ba ja mu amca ba!”
Daga Abubakar Yarima Gwagwalada Abuja, 08164828630
Kamfanin kati
Wata mata ce ita dai kullum sai ta ga a jikin kalanda ko katin shaidar daura aure an rubuta: “Congrats.” A kan haka wata rana an kawo mata biki sai ta ce: “Kai amma kamfanin Congrats yana samun kudi, ni ma zan bude irinsa.” Ita a tsammaninta, Congrats din sunan kamfani ne mai buga kati.
Daga Rabi’a Mukhtar Direba, 08134815318
Bature
Wani Bature ne ya zo wani kauyen da mutanen ba su jin Turanci, da kyar aka samu mutum guda da zai yi musu tafinta. Ga yadda suka tattauna. Bature: I came from airport. Tafinta: Na zo daga iskar tukunya. Bature: Before I go further. Tafinta: Kafin na kai ga babanku. Bature: I will like to see the head of this billage. Tafinta: Ina so in ga kan sarkin garin nan. Jin haka sai mutanen garin suka fara gudu.
Daga Musa Muhammad B. Dogo ’Yankaba Kano, 08104001040
Hoton madubi
Wata Bafulatana ce ta je birni wajen ’yan uwanta, to gidan da suke akwai irin madubin jikin bango a kofar bandaki. To duk lokacin da ta zo shiga bandaki sai ta rika ganin hotonta amma ba ta san cewa ita ce ba. Ka san Fulani da kunya, ba ta yadda su hada ido da hoton, sai ta wuce ta ce: “Ina wuni?” Kullum haka, sai rannan ta ce wa matar gidan: “Ni kam waccan matar kullum idan na gaishe ta ba ta amsawa.” Sai ta ce mata wace ce haka? Sai suka tafi don ta ga ko wace ce. Koda suka isa wurin sai ta ga madubin kofar bandaki ne.
Daga Muhammad Nasir Muhammad, 08033995650