Mu Sha Dariya

  ’Ya’yan bebe Wani bebe ne ’ya’yansa uku suka mutu sakamakon cutar kyanda, idan ya hadu abokansa suka gaisa sai ya ce: “Kana da ’ya’ya?” Idan ka ce akwai sai ya ce: “Sun yi kyanda?” Idan ka ce a’a, sai ya ce da kai: “Ba ka da ko daya, nawa duka sun yi kyanda, sun […]

Mu Sha Dariya

Mu sha dariya

 

’Ya’yan bebe

Wani bebe ne ’ya’yansa uku suka mutu sakamakon cutar kyanda, idan ya hadu abokansa suka gaisa sai ya ce: “Kana da ’ya’ya?” Idan ka ce akwai sai ya ce: “Sun yi kyanda?” Idan ka ce a’a, sai ya ce da kai: “Ba ka da ko daya, nawa duka sun yi kyanda, sun mutu!

Daga Garba Sabiyola Gashuwa, 08096284154

Sallar dole

Wani Bagobiri ne ya kai matarsa wajen malami, domin a yi mata rukiyya. Bayan an yi karatu sai aljani ya ce: “A shirye nake in fita amma da sharadi.” Malam ya tambaye shi sharadin, sai ya ce: “Zan fita daga jikinta amma zan koma a jikin mijinta.” Sai Bagobiri ya tsorata sosai, malam ya ce masa ba a yarda ya koma jikin mijin ba. Sai aljani ya ce: “Zan koma jikin mijin nata ne saboda ba ya Sallah” Malam ya tambayi mijin ko da gaske ne ba ya Sallah? Sai mijin ya ce: “Haka ne gafarta malam.” Sai Malam ya ce da aljanin: “To ka fita daga jikinta sai ka dawo kusa da gidansu, idan ka ga ba ya Sallah ka shiga jikin nasa.” Aljanin ya yarda. Bayan ’yan kwanaki sai matar ta bugo wa malam waya tana godiya, ta ce masa: “Ai yanzu haka kullum shi yake bude kofar masallaci.” Ashe tun farko matar ta hada kai da malam ne, ba aljani ne ya shiga jikinta ba, sun shirya haka ne domin mijin nata ya daina wasa da Sallah!

Limancin Sallah

Wani Bafulatani ne tafiya ta kama shi mai nisa, ana cikin tafiya sai lokacin Azahar ya yi, aka tsaya sai aka ce ya ja Sallah. Ya wuce gaba ya ja. La’asar ta yi nan ma aka ce ya ja Sallah, ya wuce gaba ba gardama. Da Magariba ta yi aka ce ya ja Salla sai ya noke. Aka ce: “Fillo me ya sa ka ki?” Sai ya ce: “Sallolin da aka yi a baya su ma don ba a cewa komai ne, wannan kuwa ana karatu, ni kuma ko Fatiha ban iya ba.”

Labarai daga Nasiru Kainuwa Hadeja, 08100229688

Amma ka hadu

Wani saurayi ne ya je dandalin shakatawa sai ya ga wata budurwa ita kadai a zaune. Ya karasa wajenta ya yi mata sallama ta amsa, sai ya fara da cewa: “Kamar na so na sanki a A.B.U Zariya.” Ta ce: “Ni ce, don ina karatu a can ne, ina mataki na 300. Kai fa?” Sai ya ce mata: “Ni ma ina karatu a can, ina mataki na 900, ina jira ne in karasa zuwa mataki na 1500, in amshi takarduna, in fara neman aiki.” Ta ce masa wane kwas yake nazarta, sai ya ce mata: “Ina karanta Islamic Engineering ne.” Ta ce masa wace firamare ya yi, sai ya ce mata: “Ai na yi Primary Election ne tukun, kafin na tafi Secondary Election, daga nan na yi B.U.K tukun, sannan na zo A.B.U Zariya. Kin ji abin yadda ya yi ta gudanuwa har zuwa yanzu.” Ita kuwa sai ta ce masa: “Kai, lallai amma ka hadu.”

Daga Yakubu Adamu Ningi, 09021109997