Mu sha dariya
Makaho da kuturu Wata rana wani makaho da kuturu suna bara tare sai kuturu ya ga wata bishiyar gwanda, ya ce: “Yawwa, makaho zo ga wata bishiyar gwanda kuma ta nuna, duka sunyi ja. Jira a nan, bari in hau; da ka ji kirif! To ja ta fado, sai ka lalube ta da sanda.” Makaho […]
Makaho da kuturu
Wata rana wani makaho da kuturu suna bara tare sai kuturu ya ga wata bishiyar gwanda, ya ce: “Yawwa, makaho zo ga wata bishiyar gwanda kuma ta nuna, duka sunyi ja. Jira a nan, bari in hau; da ka ji kirif! To ja ta fado, sai ka lalube ta da sanda.” Makaho ya amsa da to. Kuturu ya haye gwanda, can sai ya saki reshe ya kama ganye, sai ya fado kirif! Makaho ya fara cewa: “Yawwa, ja ta fado, ta nuna.” Sai ya fara lalube, kawai sai ya lalubo kuturu da sanda, ya kara cewa: “Madallah, ja ta fado!” Sai kuturu ya ce: “Ee, da sannu za ka gane ni ne na fado ba gwanda ba!”
Daga Mainasara Nasarawa Funtuwa, 08034208356
Zan rama
Wani dan Angas ne ya je gidan da aka yi mutuwa, ana zaman makoki. Aka zo ana raba burkutu, aka tsallake shi, kafin ya ankara sai aka ce giyar ta kare, sai ya ce: “Ai mutuwa ba a gidanku ta tsaya ba, ni ma ai akwai kawuna da yake kwance, kila ba zai kai labari ba. In ya mutu ku ka zo ni ma zan rama.”
Daga Ganakuri
Masu abin…
Wata tsohuwa ke zaune cikin ’ya’ya da jikoki, tsakar dare sai barawo ya zo mata, sai ta kama yi masa maraba kamar ta san shi, tana cewa: “Barka da zuwa, yanzu kake tafe? Ya iyali?” Ta dauko hura mai zuma daga ragaya, ta ba shi sai ya kama sha, abin ya ba shi mamaki, ya tambayi tsohuwa cewa: “Iya ina kika san ni, yaya sunana?” Sai ta ce: “Yaro ai ba kai ba har danginka da taken gidanku duk na sani. Idan na fadi takenku, ai duk dadin hurar nan da kake sha sai ka tsallake ka bar ta.” Ya nace sai ta fadi sunansa, sai tsohuwa daga murya da karfi, ta ce: “Ai sunanka barawo!”
Daga Amiru Isah Bakori, 07068147933
Marigayi
Wani saurayi ne da budurwarsa suna soyayya abar kwatance, sai ya samu aiki. Da wata ya kare aka biya shi Naira dubu 15, bai zame a ko’ina ba sai wajenta, ya tambaye ta me take so a saya mata; ta ce ta gode, ya je ya kai wa su mama. Sai ya matsa mata, ta ce man shafawarta ya kare. Sai ya ce: “A ina ake sayarwa?” Ta ce a kantin zamani (Super Market) ake sayarwa. Da suka je ta nuna kwalbar mai daya, ya dauko, ya je wajen biya; aka buga aka ce masa kudinsa Naira dubu 14 da 500. Sai ya zaro ya bayar, aka ba shi canjin Naira 500. Da aka tambaye shi sunan da za a rubuta a rasidin sai ya ce: “A rubuta Marigayi.”
Daga Zee Man Fagge, 08099476803