MU SHA DARIYA
Shirmen makiyayi Wani Bafulatani ne ya yiwo canjin kudi tsaba, yana cikin tafiya sai daya ya fado daga aljihunsa. Koda ya ga haka sai ya ce: “Oyyo, dama kuna tafiya kuke ba ni wahala?” Sai ya watsar da sauran, ya ce: “Ku tarar da ni a ruga.” Daga Hafizu Wanka Kano, 09030400620 Gadin gawa […]
Shirmen makiyayi
Wani Bafulatani ne ya yiwo canjin kudi tsaba, yana cikin tafiya sai daya ya fado daga aljihunsa. Koda ya ga haka sai ya ce: “Oyyo, dama kuna tafiya kuke ba ni wahala?” Sai ya watsar da sauran, ya ce: “Ku tarar da ni a ruga.”
Daga Hafizu Wanka Kano, 09030400620
Gadin gawa
Wani mai gadin makabarta ne aka kawo gawarwaki uku aka aje dakin ajiye gawa. Da aka zo daukar gawa daya daga cikin ukun, sai ya shiga ya bude musu kofa suka dauka. Shi kuma sai ya koma ciki, domin ya gyara sauran, a wurin fitowa sai kofa ta rike masa riga. Maimakon ya juya ya ga abin da ya kama rigar, sai ya yi tsammanin ko gawa ce ta rike masa riga. Sai ya kama ihu da kururuwa kuma ya ki waigawa ya ga abin da ya kama masa rigar.
Daga Hussaini Sunshine Birnin Gwari, 08032824939
Hawan rakumi
Wani Bahadeje ne ya je wurin wani malami domin a yi masa fassarar mafarki, ya ce: “Malam na yi mafarkin na hau rakumi.” Sai Malam ya ce masa: “Za ka shiga Aljanna.” Bahadeje ya ji dadi, sai ya ci gaba da cewa: “Ai Malam har ga tozonsa na hau.” Jin haka sai Malam ya ce: “Ka wuce Aljanna, ka shiga wuta.” Sai ya ce: “To, da na je sai na zamo kasa.”
Daga Musa Uke Karu, 08051702591
dan baiwa
Wani mahaukaci ne ana duba tsayuwar watan Azumi, babu wanda ya gan shi, sai ya ce: “Laa, ga wata!” Sai aka ce: “Kai, lallai wannan mutumin dan baiwa ne.” Shi kuma da ya ji an yabe shi sai ya ce: “Ku duba nan, ga wani watan can ma, har yau ma ga wani can!”
Daga Sani Ibrahim, 08076231488
‘Da ni yake yi…
Wadansu Yarabawa biyu abokan juna kuma dukansu Musulmi, suka zo cirani Arewa, sai dayansu ya shiga sayar da giya. Wata rana sai suka je jin wa’azi, sun samu Malam yana wa’azi a kan giya, sai dayan ya tambaya cewa: “Mene ne hukuncin Musulmi mai sayar da giya?” Jin haka sai abokinsa ya amsa da cewa: “Malam da ni yake yi, ci gaba da wa’azinki; in an tashi wa’azi zan ba shi amsa.”
Daga Laminu Umar Abba, 08131364647