MU SHA DARIYA
Rokon ruwa Wani Bayerabe ne ya iske ana ta rokon ruwa, daga mai ba da sadakar Naira dubu sai mai ba da Naira 500, shi kuma Naira 100 yake da ita; ya dauko ya mika. Dare na yi sai ga ruwan sama kamar da bakin kwarya, ya fito da safe sai ya ga gininsa ya […]
Rokon ruwa
Wani Bayerabe ne ya iske ana ta rokon ruwa, daga mai ba da sadakar Naira dubu sai mai ba da Naira 500, shi kuma Naira 100 yake da ita; ya dauko ya mika. Dare na yi sai ga ruwan sama kamar da bakin kwarya, ya fito da safe sai ya ga gininsa ya fadi waje daya. Sai ya kama sharba dariya. Masu jaje suka ce: “Yaya gininka ya fadi amma kake dariya?” Sai ya ce: “Na ga ni Naira dari ce kawai na bayar amma ginina bari daya ya zube, to ina ga wanda ya ba da Naira dubu ko dari biyar?”
Daga Abdullahi Adamu Sakkwato
Garori
Wani saurayi ne ya saya wa budurwarsa waya, idan zai je wurinta sai ya kira ta. Wata rana ya je suna hira sai ya ce mata yana jin kishi. Ta ce: “Rike mini wayata, in je in kawo maka ruwa.” Da shigarta gida sai aka kira ta a wayar, sai ya ga wanda ya kira an sanya sunansa ‘Gara One’ sai ya ce to bari shi ma ya duba tasa lambar wane suna take kiransa? Sai ya ga an sanya ‘Gara Two.’ Nan take sai ga kanwarta za ta shiga gida, ya kira ta ya ce: “Ga layin wayar yayarki ki kai mata, ki ce mata ‘Gara One’ ya kira ‘Gara Two’ kuma ya tafi da wayarsa.”
Daga Rilwan DJ Boy Garki Abuja, 08086766665
Karatun Shiru
Wani dan birni ne ya kai wa ’yar uwarsa ziyara a wani kauye da isarsa kauyen, sai ya ga za a ta da Sallah; kawai shi ma sai ya yi Alwala. Sai mutanen suka ce: “Allah gafarta Malam, a yi mana Sallah.” Abinka da mutanen kauye, sun ga mutum ya sha shadda. Bayan sun idar sai daya daga cikinsu ya ce: “Kai amma fa Sallar ta ja lokaci.” Sai dan birnin ya ce: “Don ma na manta yadda ake karatun Sallar, ai da ta fi haka tsawo.” Sai suka ce: “To, yanzu da yaya ka yi mana Sallar?” Sai ya ce: “Kawai shiru nake yi, sai na yi ruku’u.
Daga
Yaro mai wayo
Wannan wata hira ce tsakanin yaro da mahaifinsa, ga yadda ta kasance: Uba: Tsakanin mamarka da babanka, wa ka fi so?. Yaro: Duka ina son ku. Uba: Yanzu idan na ta fi Amurka, mamarka ta tafi Ghana, ina za ka tafi? Yaro: Ghana. Uba: To, ka fi son mamarka ke nan? Yaro: A’a, kawai saboda ina son Ghana fiye da Amurka. Uba: To, idan kuma ta dawo ta tafi Amurka, ni kuma na tafi Ghana, ina za ka je? Yaro: Amurka. Uba: (Ya bata fuska da alamar fushi), to me ya sa za ka je Amurka, bayan ka fi son Ghana? Yaro: Saboda na je Ghana tunda farko, shi ya sa zan je Amurka!
Daga Zaidu Ibrahim Barmo, Jibiya