MU SHA DARIYA
Madara ko omo? Wani Bahadeje ne ya je ci-rani birni, ya bukaci ya sha shayi sai ya je wajen wani mai tireda, ya nuna karamar jakar garin sabulu na ‘Good Mama’ ya ce a ba shi jaka daya. Shi ya zaci garin madara ce ta leda. Ya amsa ya nufi teburin mai shayi, ya samu […]
Madara ko omo?
Wani Bahadeje ne ya je ci-rani birni, ya bukaci ya sha shayi sai ya je wajen wani mai tireda, ya nuna karamar jakar garin sabulu na ‘Good Mama’ ya ce a ba shi jaka daya. Shi ya zaci garin madara ce ta leda. Ya amsa ya nufi teburin mai shayi, ya samu wuri ya zauna. Ya ce wa mai shayi a zuba masa amma kada a sa madara. Bayan an ba shi ruwan shayi, sai ya dauki kofi daya daban ya zazzage farin omon nan, ya zuba ruwan shayi ciki ya fara shekawa. Kafin ka ce kwabo sai kumfa ta cika kofin har tana zuba. Shi kuwa sai ya ce: “Aradu wannan ai fitsarin jaki ne!”
Daga T. A. Buhari, 08092055700
Masu kwadayi
Wani Babarbare ne da Bafulatani suka fita yawo wajen gari, sai arnan daji suka kama su, suka kai su wajen sarkinsu. Shi kuwa sarkin sai ya nuna musu wani lambu ya ce su shiga su tsinki duk dan itacen da suke so. Bayan wani lokaci sai ga Bafulatani ya fito da manya-manyan mangwarori guda biyu a hannunsa. Nan take sarkin ya ce wa fadawansa su danne shi su saka masa mangwarorin a duburarsa. Nan take suka cika umarni, Bafulatani ya ci bakar wuya. Ya daga kai ke nan sai ya hango Babarbare, sai ya kece da dariya. Da aka duba domin a ga abin da yake yi wa dariya, sai aka ga ashe Babarbare ne ya tsinko manya-manyan kabewa guda biyu a hannunsa yana tahowa wajen sarki.
Daga Jibril Ali Haidar Badawa Kano, 08095655514
Damun furar Bahadeje
Wani Bahadeje ne ya je wajen mai fura da nono ya ce: “A ba ni fura ta Naira 20.” Mai fura ta mika masa, shi kuwa ya karbi furar ya cinye. Ya sake cewa: “A ba ni nono na Naira 30.” Mai fura ta mika masa, ya karbi nono ya shanye. Ya sake cewa: “A ba ni sukari na Naira 10.” Mai fura ta sake mika masa, ya karbi sukari ya shanye. Bahadeje ya koma gefe ya kama kugu yana juye-juye. Mai fura ta tambaye shi cewa: “Lafiya na ga kana juye-juye?” Sai ya ce: “Damun furar nake yi.”
Daga Hamidan Badamasi Rijiyar Lemo Kano, 07061855550
Gadin dabbobi
Wani ne matarsa za ta aikin Hajji, da yake tana kiwon dabbobi sai ta ce da mijinta: “Bala, ka kula da dabbobina.” Haka ta yi ta fada masa a kullum, har dai ta shiga jirgi. Kafin su tashi ta sake lekowa ta jirgi ta ce masa: “Bala, na fa gaya maka ka kula mini da dabbobina.” Ashe wani attajiri ya ga abin da matar nan ta yi, ya kuwa ji haushi sai ya biya wa mijin nan kujera, shi ma ya tafi Makka. A can sai matar nan ta ga mijinta wurin jifar Shaidan sai take cewa: “Kai, lallai kamar ta yi yawa, ga wani kamar Bala.” Bayan wani lokaci sai ta sake ganinsa, sai ta ce masa: “Wai ko Bala ne?” Ya ce shi ne. Ta ce: “Wa ya kawo ka nan kuma ina dabbobina?” Ya ce mata: “Dabbobin banza, su mutu mana don kaniyarsu!”
Daga Anisa Daura, 07038591359