MU SHA DARIYA
A sauka lafiya Wani Babarbare ne ya shiga motar haya daga Maiduguri zuwa Bauchi. Bayan mota ta shirya za ta tashi, sai wani mutum ya ce masu: “A sauka lafiya!” Jin haka sai Babarbare ya kama fada ya ce wa direba ya tsaya, ya kama kofa zai fito daga motar, yana cewa: “Ku ba ni […]
A sauka lafiya
Wani Babarbare ne ya shiga motar haya daga Maiduguri zuwa Bauchi. Bayan mota ta shirya za ta tashi, sai wani mutum ya ce masu: “A sauka lafiya!” Jin haka sai Babarbare ya kama fada ya ce wa direba ya tsaya, ya kama kofa zai fito daga motar, yana cewa: “Ku ba ni kudina, ni ba Lafiya za ni ba, Bauchi za ni.” (Shi a zatonsa motar za ta je garin Lafiya ne a Jihar Nasarawa, saboda ya ji mutunin can ya ce a sauka lafiya).
Daga Rahinatu K/Mazugal Kano, 09036444468
Wani Bafulatani
Wani Bafulatani ne da Babarbare suna cikin sahun Sallar Juma’a, liman yana cikin huduba sai tusa ta kubuce wa Bafulatani har ma ta yi kara mutane sun ji, sai suka kalli bangaren da tusa ta fito. Bafulatani ya yi tsuru-tsuru, Babarbare da yake kusa da shi sai ya kura masa ido, alamar ya gane shi ya yi tusar. Da Bafulatani ya ga zai tona masa asiri sai ya kalli Babarbare ya ce masa: “Yau ai sai ka tashi ka je ka sake alwala.”
Daga Adamu Mahmud Dogonjeji, 08057631302
Kudar fartanya
Wani Bafulatani ne ya kai kudar fartanya wurin makeri. Da aka gama kudawa sai makerin ya ce masa: “Kada ka rataya a bayanka, domin idan ka yi haka to ’ya’yan makera za su mutu.” Shi kuwa yana barin wurin makerin sai ya ce: “Don ’ya’yan makera sun mutu sai me?” Sai ya rataya fartanyar a kafada, wai don mugunta. Nan take fartanya ta kone masa baya, saboda zafin da ke tare da ita.
Daga Amiru Isa Bakori, 08075959086
Ciwo ko yunwa?
Wani Bakano ne mai makon tsiya, ya dauki hajarsa ya tafi cikin gari talla. Tun da safe har zuwa La’asar bai ci komai ba. Ya yi ciniki mai yawa kuma ya samu riba, amma ya dawo gida haka nan. Yana zuwa yunwa ta buge shi ya fadi, aka yi ta ba shi magani, amma da ya sha sai ya amayar. Can sai wani Bazamfare ya ankara da cewa yunwa ce ke damunsa, sai ya ce wa iyalin bakano: “Kun ba shi fura kuwa?” Sai Bakano da ke kwance cikin ciwo ya daga kai ya ce: “Yau sun yi wannan dabarar kuwa?”
Daga Amina Umar Gummi, 08060322272