MU SHA DARIYA

Santin tuwo Wata mata ce wadda take da ’ya’ya uku masu suna Sada da Bala da Umar. Sada shi ne babbansu. Wata rana ya dawo gida, mahaifiyarsa ta sanya masa tuwa da miyar kuka, wacce aka sharbane da man shanu. A gefe daya kuma kannensa biyu suna zaune suna wasa, domin sun ci nasu abincin […]

MU SHA DARIYA

Santin tuwo

Wata mata ce wadda take da ’ya’ya uku masu suna Sada da Bala da Umar. Sada shi ne babbansu. Wata rana ya dawo gida, mahaifiyarsa ta sanya masa tuwa da miyar kuka, wacce aka sharbane da man shanu. A gefe daya kuma kannensa biyu suna zaune suna wasa, domin sun ci nasu abincin kafin ya dawo. Bayan ya yi loma uku a jere, sai ya ce wa mahaifiyarsa: “Goggo, da ana shuka mutane, da yanzu Bala da Umar ba su yi tsiro ba.” Mahaifiyar da ta ji haka sai ta yi sauri ta aje masa ruwa a kofi, ta ce masa: “Sai dai in ruwan sama bai sauka da wuri ba.” Ya daga kofin ya shanye ruwan, ya yi ajiyar zuciya, ya ce: “Allah mai iko!”

Daga Isyaku Bara’u Zakkah 

 

 

Bam ko tantabara   

Wani Bahadeje ne ya dauko namijin tantabara a cikin kwali, ya zo wucewa ta inda ’yan sanda ke duba mutane. A nan wani dan sanda ya daka masa tsawa, ya ce: “Kai, mene ne a cikin kwalin nan? Zo nan ka bude shi.” Babu musu sai Bahadeje ya ajiye kwalin a gabansa. dan sanda ya kara daka masa tsawa, ya ce: “Bude mana!” Nan take Bahadejen nan ya fara kokarin budewa yana kuka, yana cewa: “Wallahi idan na sake na bude, tashi zai yi, tashi zai yi yallabai.”

Ai kafin ka ankara, ’yan sanda sun fita da gudu, sun bace daga wurin. Sun yi tsammanin  bam ne a cikin kwalin zai tashi.

Daga Kabir Sakaina Layin ’Yangoro Malumfashi 08095968366

 

Mai wayau

Wani mutum ne, wani ya yi masa laifi ya kama shi ya yi ta marinsa. Ashe akwai soja kusa, shi ma sai ya biyo ta baya ya zabga wa wannan mutumin mari. Mutumin nan ya juyo a fusace ya cakumi sojan. Ashe ba shi kadai ba ne, da ya daga kai ya ga mota kusa da su cike da sojoji sai ya wayance, ya kama karkade wa sojan nan riga, yana cewa: “Sorry sir (don Allah yi hakuri).”

Daga mai lamba 08029632912

 

Wata amarya

Wata yarinya ce mai hankali da biyayya amma kuma ba ta da ilimi. Rannan sai aka yi mata aure ta tare a gidan mijinta. Ranar farko sai ango ya zo suka zauna suna hira. bayan sun ci abinci tare, dare ya raba, sai ta ga yana tube kayansa. Ya ce da ita: “Mu shig daga uwar daki.” Nan fa sai ta fara kuka tana cewa: “Ni dai ba ’yar iska ba ce.”

Daga Alhaji danladi China Kano 08034463170