MU SHA DARIYA
Kai Musulmina? Wani Basakkwace ne kullum yake tsokanar wani dan kabilar Ibo yana ce masa kafiri. Sai Ibon ya kai kara wajen mahaifin Basakkwacen ya ce da Ibon, “Kai Musulmina?” Sai Ibon ya ce, “A’a.” Sai Basakkwacen ya ce da Ibo, “To ai sunanka kafirina. Tafi ka ba ni wuri.” Ka sani kake tambayata? […]
Kai Musulmina?
Wani Basakkwace ne kullum yake tsokanar wani dan kabilar Ibo yana ce masa kafiri. Sai Ibon ya kai kara wajen mahaifin Basakkwacen ya ce da Ibon, “Kai Musulmina?” Sai Ibon ya ce, “A’a.” Sai Basakkwacen ya ce da Ibo, “To ai sunanka kafirina. Tafi ka ba ni wuri.”
Ka sani kake tambayata?
Wani saurayi ne ya yi wa wata budurwa wasan banza, sai ta kwada masa takalmi a idonsa ido ya yi jazur. Sai ya zo wurin abokansa suka tambaye shi, sai ya ce ya je raba fada ne aka buge shi a ido. Sai daya daga cikinsu ya ce amma kamar dukan takalmi ne. Sai ya ce a cikin fushi “Kaza-kazarka, ka san abin da ya faru kake tambayata?”
Labarai daga 09099886988
An sayar yadda ka sayo!
Wata rana wani barawo ya sato kaya sai ya ba matarsa ta kai kasuwa ta sayar. Da ta je kasuwa sai aka sace kayan, ta dawo gida ta samu mijinta a cikin jama’a suna hira. Ya ce mata: “An sayar da kayan?” Sai ta ce: “An sayar kamar yadda ka sayo.” Sai ya ce: “Babu riba ke nan.”
Daga Barde Gidan Gebi, Zango Bauchi
Ango ya baro ta
Wani ango ne ana walimar bikinsa, ’yan uwa da abokan arziki duk sun taru. Bayan an kammala sai aka ce ango ya tashi ya yi jawabin godiya. Ango ya ce: “Godiya ta musamman ga Malam Sani Tudun Kaure Dillalin Gidaje, wanda ya ba mu aron inda za mu zauna, kafin mu samu haya. Ba zan taba mantawa da Hajiya Shafale Mai ‘dashi ba, wadda ta ba ni daukar farko na kai kudin aure. Godiya ga Asabe Dillaliya, wadda ta ba mu bashin atamfofi da shaddodi da muka sa a lefe. Allah Ya saka wa kanwata Habiba, da taimakonta ne na fita kunya don kuwa ita ce ta ba ni aron akwatunan lefenta, aka sa kayan a ciki. Allah Ya bar zumunci, Ya ba mu ikon cika alkawuran da muka dauka. Haka kuma ba zan manta da Atiku Mai wanki da guga ba, shi ya ba ni aron kaya har na fita kunya. Mun gode, Allah maida kowa gidansa lafiya.”
Daga Jibrin M.D. Lafiya, 08133477778
Kawo birin in rike miki
Wata mata ce ta shiga tasi sai ta zauna gidan gaba, ana cikin tafiya sai direban ya juyo ya kalle ta da ita da danta, sai ya kwashe da dariya ya ce: “Gaskiya Hajiya ban taba ganin mummuna irin danki ba.” Ta dube shi ta yi tsaki, sannan ta ce ya tsaya ta koma baya. Ta koma baya tana zage-zage, sai wani tsoho da ke bayan motar yake tambayarta abin da ya faru, sai ta fada masa abin da direban motar ya ce mata. Tsohon ya ce: “Kin mare shi?” Sai ta ce: “A’a.” Sai ya ce: “Kawo birin da ke hannunki, in rike miki shi, ki je ki mare shi.” Jin haka, tuni zuciya ta kashe ta, ta dankara wa tsohon nan mari, saboda ya kira danta da biri.
Daga Buhari Liman Kudan, 08034500055