Mu Sha Dariya

Babarbare da zaki Wani Babarbare ne ya je daji sai ya gamu da zaki sai ya ji tsoro sosai. Cikin fargaba sai ya duka a gaban zakin ya rufe ido yana addu’a. Koda ya bude ido sai ya ga zakin shi ma ya duka gabansa yana addu’a. Sai abin ya ba Babarbare mamaki, sai ya […]

Mu Sha Dariya

Mu sha dariya

Babarbare da zaki

Wani Babarbare ne ya je daji sai ya gamu da zaki sai ya ji tsoro sosai. Cikin fargaba sai ya duka a gaban zakin ya rufe ido yana addu’a. Koda ya bude ido sai ya ga zakin shi ma ya duka gabansa yana addu’a. Sai abin ya ba Babarbare mamaki, sai ya tambayi zakin cewa: “Kai ma Musulmi ne?” Sai zakin ya ce masa: “Ai ni idan zan ci nama sai na yi addu’a tukunna, kai fa yaya kake yi?”

Daga Alhaji Umar Foreber Gashuwa, 08108003333

 

Sai in auri Liman

Wani Bafulatani ne da matarsa daya mai suna Hamida, ran nan sai suka samu sabani, sai ya ce mata: “Kin ga, ki bi ni a hankali, idan kika yi wasa aradu sai in sake ki, ki koma gidanku.” Ita kuma sai ta tsagalgale ta ce masa: “To ka sake ni mana, sai me? Kawai da ka sake ni sai in tafi in auri Liman!” Jin haka sai Bafulatani ya shiga mamaki, ya ce: “Hoo ga ja’ira, ashe Hamida kun dade da Liman kuna munafunci! Shi ya sa kullum a wurin Sallah nake jin yana cewa ‘Sami Allahu Liman Hamida’ wato yana nufin ga Liman ga Hamida!”

Daga Bashir Yahuza Malumfashi, 08065576011

 

Kudin aikina ya karu

Wani attajiri ne da ake kira da sunan Alhaji a wani kauye, ya yi amarya sai ya dauki Buzu domin ya yi masa gadi. Wata rana Alhaji ya yi tafiya sai amarya ta shiga ban-daki za ta yi wanka, sai ta bar soson wanka a waje, sai ta kwala wa Buzu kira ta ce: “Nawaila!” Sai da ya zo sai ta ce masa ya mika mata soso. Sai da ya zo zai mika mata sai ta ce masa: “Don Allah ka shigo ka cuda ni.” Ya shiga ya yi mata wanka. Da Alhaji ya dawo suna hira da Buzu sai ya ce masa: “Alhaji kudin aikina ya karu saboda da ba ka nan amarya ta ce in cuda ta, don haka za ka kara min kudin aiki.”

Daga Umar Akilu Majeri, 09027154489

 

Lakadan!

Wani Buzu ne yake gadi a gidan wani attajiri sai kullum a fito da abinci a ci a koshi, har sai an mayar da wani gida. Ashe Buzun nan ba ya so ana mayar da abinci gida. Ran nan sai ya je gida ya yi ta ba kowa labari. Da zai dawo sai ya debo ’yan uwansa da yawa zuwa birni. Suna zuwa ko gaishe da Alhaji ba su yi ba, suna tsaye, sai Buzu ya ce wa Alhaji: “Wannan abu da yake gagararmu cinyewa kullum, yau na zo da masu gama masa aiki. Sai sauran abokan tafiyarsa Buzaye suka buga kafa kamar masu fareti, suka ce “Lakadan.”

Daga Umar Akilu Majeri, 09027154489

 

Sallar dole

Wani Bagobiri ne ya kai matarsa wajen malami, domin a yi mata rukiyya. Bayan an yi karatu sai aljani ya ce: “A shirye nake in fita amma da sharadi.” Malam ya tambaye shi sharadin, sai ya ce: “Zan fita daga jikinta amma zan koma jikin mijinta.” Sai Bagobiri ya tsorata sosai, malam ya ce masa ba a yarda ya koma jikin mijin ba. Sai aljani ya ce: “Zan koma jikin mijin nata ne saboda ba ya Sallah.” Malam ya tambayi mijin ko da gaske ne ba ya Sallah? Sai mijin ya ce: “Haka ne gafarta malam.” Sai Malam ya ce da aljanin: “To ka fita daga jikinta sai ka dawo kusa da gidansu, idan ka ga ba ya Sallah ka shiga jikin nasa.” Aljanin ya yarda. Bayan ’yan kwanaki sai matar ta bugo wa malam waya tana godiya, ta ce masa: “Ai yanzu haka kullum shi yake bude kofar masallaci.” Ashe tun farko matar ta hada kai da malamin ne, ba aljani ne ya shiga jikinta ba, sun shirya haka ne domin mijin nata ya daina wasa da Sallah!