MU SHA DARIYA

Horon dankali Wata amarya ce ta rangada wa ango girki, ya ci ya yi ta santi, ya yi ta koda amaryarsa a wurin abokai. Bayan kwana biyu, sai ango ya yi niyyar gayyato abokansa, don su zo su dandana abincin amaryarsa. Ya gaya mata cewa abokansa za su zo don cin abincin rana. Koda suka […]

MU SHA DARIYA

Mu sha dariya

Horon dankali

Wata amarya ce ta rangada wa ango girki, ya ci ya yi ta santi, ya yi ta koda amaryarsa a wurin abokai. Bayan kwana biyu, sai ango ya yi niyyar gayyato abokansa, don su zo su dandana abincin amaryarsa. Ya gaya mata cewa abokansa za su zo don cin abincin rana. Koda suka tashi da safe sai ta soya musu dankali suka karya. Ya tunatar da ita batun zuwan abokansa. Bayan ya tafi, sai amarya ta bi lafiyar gado, ta yi ta barcinta, ba ta tashi ba sai karfe biyu na rana. Daidai lokacin kuwa ango ya shigo da abokansa, ya zo ya same ta ya ce: “An gama abinci?” Sai ta ce: “Eh, an gama.” Ya ce to a kawo, sai ta je ta tattaro ragowar dankalin da suka ci da safe, ta kawo musu. Ango na budewa sai ya ga busasshen dankali, hankalinsa ya tashi. Ya shiga ya ce mata: “Yaya haka?” Sai ta ce: “Ni dankali nake son ci yau.” Da zai fita sai ta ce ya yiwo musu cefane, sai ya ce ba damuwa. Kawai sai ya tafi kasuwa ya sayo buhun dankali ya kawo. Aka dafa da da dare, safiya ta yi, aka sake dafa dankali, da zai fita, ta ce ya kawo kudin cefane, sai ya ce: “Dankali nake son ci.” Aka yi kwana uku suna cin dankali, sai amarya ta gudu gidansu. Iyayenta suka yi mamaki, uban ya kira angon ya ce lafiya ya ga wance a gida? Sai angon ya ce: “Ban ma san ta tafi gida ba,” amma sai ya kwashe labari ya fada masa. Shi kuwa ya ce wa angon ka bar ni da ita, ba sai ka zo ba. Shi ma uban sai ya sayo dankali buhu guda ya kawo gida, dare ya yi ta ga an dafa dankali a gidansu, safiya ta yi ta ga dankali; aka yi kwana biyu ana dafa dankali, uban bai ce mata komai ba. Abin ya dame ta, ta rasa yaya za ta yi.

Daga Abdullahi Abba Askira

Danye-danye!

Wata ’yar kabilar Gwari ce ta ga wani Bahaushe zabiya, ta ga duk jikinsa ya cabe, ya yi kuraje-kuraje; sai ta ce: “Ah, wai Bahaushe yana so ya yi Bature bai iya ba, ga shi nan ya yi shi danye-danye!”

Daga 09092969381

 

Ku saurari Mudi in ana so in warke!

Wani Bakano ne mazaunin Kudu, jarinsa ya karye, ya yi kokari ya samu abu ya faskara; sai kawai ya kwanta, ya ce ba ya da lafiya. Abokan zama suka taru don shawarar yadda za a yi da jinyarsa. To, a cikinsu akwai mai suna Mudi, sai mutum na farko ya ce: “Jinyar nan, mu mai da shi gida Kano.” Na biyu ya ce: “A’a, mu nemi kudi mu saya masa magani.” Sai Mudi ya ce: “A’a, mu nemi kudi wajen ’yan uwa, mu ba shi rabi ya ja jari, rabi kuma mu saya masa magani.” Nan da nan sai Bakanon ya dago kai ya ce: “Ku saurari Mudi, kada a wuce shawararsa fa, idan har da gaske kuna son in warke.”

Daga Armaya’u Bala, 08039674777

Kurma da Basakkwace

Wani Basakkwace ne rigima ta hada su da wani kurma kuma ga shi kurman ya fi karfinsa sosai. Saboda haka kurman ya bugi Basakkwacen nan sosai, aka taso aka raba su. Sai kurma yake kwacewa kan zai dawo wurin Basakkwace; sai Basakkwacen ya ce: “Ku sake nai, in dai yadda na jiya haka ya jiya, ko kun sake nai bai zuwa.”

Daga Isah Sani Mai Arsenal Garkon-Alli, 08062332784