MU SHA DARIYA

Kidayar jinsi Rai=Namiji. Mutuwa=Mace. Arziki=Namiji. Tsiya=Mace. Hankali=Namiji. Wauta=Mace. Taimako=Namiji. Mugunta=Mace. Karfi=Mamiji. Ragwanta=Mace. Kokari=Namiji. Kasala=Mace. Nema=Namiji. Sata=Mace. Tausayi=Namiji. Keta=Mace. Ruwa=Namiji. Wuta=Mace. Kuđi=Namiji. Fatara=Mace. Koshi=Namiji. Yunwa=Mace. Dadi=Namiji. Wahala=Mace. Matsayi=Namiji. Kaskanta=Mace. Karatu=Namiji. Waka=Mace. Aure=Namiji. Zina=Mace. Zumunci=Namiji. Gaba=Mace. Kirki=Namiji. Masifa=Mace. Aiki=Namiji. Caca=Mace. Lemo=Namiji. Giya=Mace. Aiki=Namiji. Rigima=Mace. Alkawari=Namiji. Yaudara=Mace. Daga wani da bai bayyana sunansa ba Abokai biyu makaryata? Wani […]

MU SHA DARIYA

Mu sha dariya

Kidayar jinsi

Rai=Namiji.

Mutuwa=Mace.

Arziki=Namiji.

Tsiya=Mace.

Hankali=Namiji.

Wauta=Mace.

Taimako=Namiji.

Mugunta=Mace.

Karfi=Mamiji.

Ragwanta=Mace.

Kokari=Namiji.

Kasala=Mace.

Nema=Namiji.

Sata=Mace.

Tausayi=Namiji.

Keta=Mace.

Ruwa=Namiji.

Wuta=Mace.

Kuđi=Namiji.

Fatara=Mace.

Koshi=Namiji.

Yunwa=Mace.

Dadi=Namiji.

Wahala=Mace.

Matsayi=Namiji.

Kaskanta=Mace.

Karatu=Namiji.

Waka=Mace.

Aure=Namiji.

Zina=Mace.

Zumunci=Namiji.

Gaba=Mace.

Kirki=Namiji.

Masifa=Mace.

Aiki=Namiji.

Caca=Mace.

Lemo=Namiji.

Giya=Mace.

Aiki=Namiji.

Rigima=Mace.

Alkawari=Namiji.

Yaudara=Mace.

Daga wani da bai bayyana sunansa ba

Abokai biyu makaryata?

Wani ne ya samu abokinsa ya ce masa: “An aiko mini kyautar Naira miliyan dari amma na ki amsa na ce ba na so.” Jin haka sai abokin ya ce masa: “To ai wannan ba abin mamaki ba ne, domin ni bankina ya turo mini da Naira dubu dari uku, amma na mayar musu abinsu. Wani ya turo mini katin waya na Naira dubu dari daya bisa kuskure, na mayar masa da abinsa. Ina tafiya na tsinci Naira miliyan daya, na kai cigiya gidan rediyo. Idan kana musu, ka turo mini katin Naira dari biyar ka ga abin da zai faru!”

Daga Haiman Ra’is Kaduna, 08185819176

Tambaya da amsa

Wani dalibi ne ya tambayi malaminsa cewa: “Malam, idan kaza ta ci amanar mijinta zakara, ta yi tarayya da wani zakaran, to kwan da ta samu a haduwar halal ne ko haram?” Sai malamin ya amsa da cewa: “Ta aikata alfasha, kwan kuma ba zai zama halal ba har sai kun kawo ta na yanke mata hukuci.”

Daga Haiman Ra’is Kaduna, 08185819176

Ban ji kanshin turare a hoton ba

Wani Babarbare ne ya tafi daukar hoto sai a hanya ya sayi turare ya tafi da shi. Lokacin da za a dauki hoton sai ya fesa turaren a jikinsa da niyyar idan an wanke hoton zai ji kanshin turaren. Da aka wanke hoton aka ba shi sai ya sunsuna bai ji kanshin turaren ba, sai ya ki karbar hoton ya ce: “Ni ba zan yarda ba, ai ban ji kanshin turarena ba.”

Daga Sani Babawuro Jama’are, 08093435003