MU SHA DARIYA

Ustaz Ango Wani Ustaz ne ya yi aure, a daren farko da ya kusanci amarya, sai amarya ta ki amince masa; sai ya aske gemunsa. Shi kuwa a ko’ina an san shi da kishin gemun nasa, ba ya son abin da zai taba shi. Duk da haka, saboda soyayyar da yake yi wa amaryarsa, a […]

MU SHA DARIYA

Mu sha dariya

Ustaz Ango

Wani Ustaz ne ya yi aure, a daren farko da ya kusanci amarya, sai amarya ta ki amince masa; sai ya aske gemunsa. Shi kuwa a ko’ina an san shi da kishin gemun nasa, ba ya son abin da zai taba shi. Duk da haka, saboda soyayyar da yake yi wa amaryarsa, a daren ya aske gemunsa fes, bai bar gashi ko kadan ba. Da ya fito cikin abokai da safe, suka ga babu gemu tare da shi sai suka ce: “Ustaz ina gemunka?” Shi kuwa sai ya amsa da cewa: “Wata Sunnah ce ta kori wata Sunnar!”

 

Gaisuwar mutuwa

Wani Bafulatani ne mahaifiyarsa ta rasu, sai Sarkin Fawa da mutanensa suka je yi masa gaisuwa. Sarkin Fawa ya ce masa: “To Jauro sai ku yi hakuri, domin rashin mahaifiya babban rashi ne.” Shi kuwa sai ya amsa da cewa: “Haba Sarkin Fawa, saniya da ciki ma ta mutu mun yi hakuri balle kuma Inna?”

Labarai daga Haiman Khan Ra’is Kaduna, 08185819176

 

Gidanmu suka nufa

Wata rana ne an dauko gawa, an zo wucewa da ita kusa da Shehu Jaha, wanda shi kuma yana tare da dansa. A cikin masu raka gawar har da matar mamacin, sai ta rika alhini tana cewa: “Yanzun nan za mu kai ga gidan nan da babu shimfida, babu labule, babu abinci, babu ruwa…?” Jin haka sai dan Shehu Jaha ya kalli babansa ya ce masa: “Wallahi baba gidanmu suka nufa.

Daga Rahinatu Kofar Mazugal Kano

 

Alanguburo

Wani Babarbare ne yana kallon talabijin sai ya ga an nuno Sarkin garinsu a wajen taro. Sai ya tsugunna ya gaishe shi, ya ce masa: “Alanguburo!” Yana tsammanin zai amsa masa gaisuwar.

 

Gara da ban taka ba!

Wani Babarbare ne yana tafiya sai ya yi tuntube da wani abu cikin duhu. Ya duka ya dauka, ya shinshina sai ya ji ashe kashi ne. Ya buda baki sai ya ce: “Alhamdulillahi gara da da ban taka ba.”

Labarai daga Sani Babawuro Jama’are, 08093435003